page 16

4.1K 357 11
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                          16
Sosai yasha mamakin yarinyar to ita kuwa  menene da riqa ninke wannan fuskar ta d'aura *Wata Fuskar* akan kyakyawar fuska irin wannan? Dukda ya kula akwai makeup a kan fuskar amma ya tabbatar da cewar itace tawa makeup d'in kyau bawai makeup d'inne ya mata kyau ba, tana sanye da rantsattsen lace maroon color ta yafa mayafi fari dayake ratsin fari ne ajikin lace din, mayafinta asaman kafad'unta duka biyu ta zagoshi be sauka ba bare ya rufe mata jikinta wannan ya sanya duk a takure take, yakuma kula sosai da hakan  murmushi ya sakarwa kanshi ya kula ya shagala sosai da kallon Nancy yana qoqarin kawarda dubanshi gareta ta juya masa baya nan take doguwar sumar kanta da aka linke kusan hudu aka mata daurin zara buhari ya bayyana, kafe idanshi yae akan sumar kanta ko shakka bayayi yanayin Nancy ya masa shi duk wannan qaton qugun nata be dameshi ba sam hankalinsa yatafine akan murmushin ta me qayatarwa daya tabbatar murmushin ne yake sada zuciyar sa da tata wuri d'aya suke tattakin had'ewa su tarwatse masa!!!  Gyaran zaman sa ganin dayae ta tinkarosa gaba d'aya, runtse idan sa yae haka halittar tafiyarta take ya gano hakan sanda take nufar sa ko a hijan haka tafiyar ke nunawa qafafuwanta ba tsaye suke ba miqe sundan bole aqasansu irin bow legs din nan sedai ba sosai ba kamarma heeps din dasuke shirin mata yawane suka miyar da qafafuwan haka, miyarda kallonsa yae zuwa ga fuskarta Allah ya mata arziqin goshi kam qatoto ma kuwa bazece yawa fuskar kyauba muniba amma bako shakka be wani yi mata kyau ba sedai yarasa ata ina kyawun ke fitowa to? Lumshe idon sa yae ya furta a sarari "Daga cikin ruhin mamammalakiyar fuskar ne bako shakka" Zuhair ya miqa masa kyakyawan kallo yace

"Kaima kana kallon wacce yarinyar ne ko, ban taba ganin bow legs sunyi kyau ba se nata dukda ba sosai suka bole ba amma kam ana gani tangaram, sedai kalli fuskar tsarki ya tabbatarwa ubangijin daya qera wannan halittar" kan Maheer ya lalubo wata kalma harta qaraso da yaron masu rarraba abinci a bayanta dauke da tray tana murmushi ta nuna ma yaron table tace

" yaa Maheer ga abinci kui hakuri se yanzu yake isowa ina wuni" yau kawai Maheer yaji kalmomin bakinsa sun masa nauyi ya kasa furta koda qwaqwaran kalma dayace se murmushi yake zuba mata itama haka aka gama jere abincin tace

"Yaa Maheer idan kana buqatar wani abun call me plss, islam fa banan na ganku atare ba" kallon wurin datake yae bema san yaushe ta tashi a wurin ba, murmushin sa kawai yake narka mata,kanma yace wani abun islam ta dawo, harara ta wurga mata

"Danla ni muje ki tayani nuna wa masu rabon abincin nan baqin mu na musamman Allah a tsauwale nake da mayafin nan, tamkar zan runtuma ihu" Dariya tayi

"To ai kuma wlhy kinyi kyau qawata kamar bake ba, babu ma wanda ze yadda kece Nanuwan Baba iro" dariya suka kwashe dashi dukkansu kan su juya a tare  yanayin tafiyar Nancy yake kallo ata baya yana murmushi........

Mintsilinta lslam tai tace "ke mazari a hijabi yau banga kina rawar ba" Murmushi tae

"A wannan taron zanyi rawa Islam? Kumama babu sutura ajikina fa dan wannan mayafin wlhh gwara na wurgar ma nake gani nikam"

"Amma kinsan beyiba kice bazakiwa ummul lik'i ba, koda na 2 mns kiyi, kina sani sarai mutanen nan kallon maqiya suke muku, plss ki nuna musu kin fisu murnar bikin kije kiyi rawa abinki, bafa komai bane ba yanzu an wuce wannan abubuwan dakike Nancy" murmushi ta sake yi a karo na barkatai

"Zanyi liqin mana rawar cedai bazan yiba" haka suka wuce suna wannan zancen,tayi likin amma batai rawar ba sam har aka tashi a wurin bikin......

***********
    Yayar Maheer sam ta kasa aminta da aurensa da islam yayinda mahaifiyarsu tace sam baza'a takura masa ba, idan bazasu tayashi da addu'a ba tokuwa su bari kawai sabida ita bataga dalilin fasa yin auren ba dan kawai ana taqamar yarinya bataji, a bincikenta kaf bataji inda akace yarinyar ta tab'a barin gidansu zuwa wani wurin domin yin zaman kanta ba, in ko hakane meye nasu na dirza rashin mutunci har suce bazasu bari ya aureta ba, qaddarace ta rayuwa kuma wlhy kowa ze iya afka mata" Badan sunso ba suka hakura tare da sanyawa abun albarka....Anty Nasara itace babba kuma itace fitinanniya acikinsu sam ita bawai dan ance yarinyar tayi yawon tazubar ba kawai batason talakawa, yanda friends dinta ke bata girna ace auren Maheer dataci buri zasuyi da er matsiyata qyaure kofar gidansu yarinyar ance basuda shi se fatar buhu a irin wannan gidan zasukai baqin su ko en rakiyar daukan amarya da en kai lefe? Gaskia da sake wai an baiwa me kaza qafa.....bari yaje amma taga maheer din!

WATA FUSKATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang