page 18

3.5K 341 17
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

18
Maheer besan meke faruwa yana zaune a parlor gidansa babu abinda zuciyar sa ke masa se azalzalarsa akan yaje yaga Islam beson fushin ta ko b'acin ranta ko kadan, yayita kiran layinta a kashe gashi gaba d'aya ya damu, Maheer yana qaunar Islam sosai baso na wasa ba......breakfast kurun yake jira ya tafi ya qakara, whatsapp nashi ya shiga yaje gun status kai tsaye.....acen yaga wani friend dinsu ya saka rawan dasu Hafsat sukayi jiya beso hakan ba ze mata fad'a sosai akan rawa, tanada kamun kai koyaya takeson rawa tasan inda ya dace tayi rawar shine yafi,acikin maza bayaso yanzu gashi video din yana yawo hakan aibe kyautuba tsaki yaja a ranshi yace

"Nikuma awa?" Wuce status d'in yayi sekuma ya miqe tsaye da sauri kamar wanda aka tsikara ya qara qurawa picture din ido, hoton sane shida ita anja arror akusa da ita wai ana cigiyarta tun jiya da dare daga kai amarya kowa ya mata shedar batada yawo an jajje gidajen en uwa ba'a same taba.......da jallabiyar jikinsa ya fita daga gidan jikinsa har rawa yakeyi b'ata fa, jiya ya ganta wurin kai Amarya to ina tashiga? Shida kanshi ya kula da rashin ganin dabe mata ba sanda ake qoqarin barin gidan amaryar akai en mata gida har layinta ya nema be shiga ba...... Kai tsaye gidansu islam yaje anan yakejin wai tana kwance babu lapia tun shekaranjia.....har ciki ya shiga suka gaisa yake gaya mata aikuwa ta nemi cutar dake damunta ta rasa, se kuka tare sukaje gidan su Nancy islam se kuka take masa amma hankalinsa baya gunta, koda suka je khadeeja ce me musu bayanin

"A tare muka fito daga cikin gidan Amaryar fitsarine ya mayar dani da gudu inyi kafin mu dawo, na barta aharabar gidan...mune farkon fita gaba daya amma sena samu matsala danaje fitsarin nashiga toilet setai locking ga d'akin dana shiga babu kowa acikinsa haka nayita kici kicin na bude ga wayana na bata riqo yana jakarta qaramun wayana dake hannuna ba kati haka naita jiran tsammani da qyar na bude qofar koda nazo ba kowa shisa ban nemetaba na hau adaidaita kawai na dawo, neman wayana dana bata riqo ne ya ankarar da mutanen cewar ba'a gantaba a wurin sam!!!! Ta qarashe maganar tana kuka hadr da toshe bakinta da hijabin ta

" tundaga lokacin wayanta da nawa aketa kira basa tafiya ko nan da cen, Mamanta sumanta biyu muna zargin kidnerpers dinnan dasukai yawa ne a gari" Shiru Maheer yae yana nazarin kalamanta kanshi yayi zafi yarasa ma mezeje ga islam se qara d'aga masa hankali take tana faman kuka...

**************

Nancy se zare iso takeyi tarasa gane inda take bayan ta farka, hankalinta ya matuqar tashi ganin kanta datae acikin qungurmin daji ita kad'i kuma a d'aure jikin icce, takasa gane shin mafarki takeyi ko Gaske ne......innalillahi wa innah ilaihirraji'un itace kalmar dataketa nanatawa a bakin ta, bilhaq dai ta gano tana cikin musiba bazata iya tuna komai ba se ganin wasu maza suna tambayarta ko nane gidan Amaryar Aminu tace e shikenan seta wayi gari ta ganta a wani d'akin tare da wata mace kantae wani yunqurin kuma tarasa ina take se yanzu, waiga wa tae gabas da yamma kudu da arewa bataga alamar ko kadangare a jejin ba, babu alamar gari a gaba bare a baya, wurin yayi tsit se ita kadai runtse idanta tae ta soma rero duk wata addu'a datazo bakinta haka ta wuni har yamma ga jakarta a kusa da ita an ajiye mata amma bataza iya kunce kantaba bare ta dauki jakar ko zataga wayarta!!! Wannan shine tashin hankali wanda ba'a saka masa rana.....wata irin razananniyar qara ta saka sabida ta gaji ga yunwa ga qishiruwa, ta qosa ta ganta a kunce, babban abinda yafi daga mata hankali shine rashin yin salloli idan zata irga da kyau tunjiya da aka d'akkota rabon datae salla yo batamasan inda kanta yakeba bare tace zatayi salla.... Adu'ar taci gaba dayi ganin ihun ba abinda ze fitar da ita bane......duhu ya sauka se wannan lokacin tasoma jin kukan tsuntsaye alamun sun dawo daga inda suka tafi qishiruwa takeji sosai tamkar zata mutu, yawun bakinta ya gama qafewa wani duhu ta gani tsaye agabanta abinda , a hankali ta d'aga kanta sama domin kallon meye anan ta sume bayan ganin abin....

*************
Maheer ya rasa dalilin damuwar sa akan Mancy, ko Ummul bata cikin nutsuwa kullum setayiwa Ameen kuka, ango ya kasa gane kanta, mahaifiyar Nancy tana nan an miyarda yaranta Niger amma tana nan, gashi an koma skul amma Nancy bata nan yanzu tsawon wata d'aya kenan da b'atan Nancy amma bako wanda yaga sanda wani abu ya sameta, Islam kam an gama ramewa an lalacewa akan rashin Nancy indai ka santa to kallo d'aya zaka mata ka gano cewar tana cikin rashin kwanciyar hankali da nutsuwa na rashin Aminiyarta school d'inma tana zuwane kawai sabida babu yanda zatayi, auren ta kuma saura sati uku gaba d'aya ji takeyi batason auren nan kwata kwata, indai Nancy bata nan gani take auren ma gwara babu, da farko ta dauka kidnappers ne har tana shirin kudaden data tara na yawon duniya take shirin siyan kayan daki ta bayar a hada a karbo ta amma segashi shisu basu kiraba...tafi qaunar yau ace gawar Nancy aka gani tasan mutuwace akan hakan.....

Maheer kam acikin ranshi yakejin azabar daya kasa bayyana ta sabida babu wata alaqa ta jiji a tsakaninsa da nancy dazata sanya ya kasa mancewa da lamarin ta ya bita da addu'a kawai, wani zubin har abinci yake kasa ci,abu mafi bashi mamaki shine yanda yake mata kuka duk sanda ya tunata seyayi kuka kenan kuka ya zame masa d'abi'a kullum sabida da ita yake kwana yake kuma tashi baya manta ta wanda ya sanshi ma yasani walwalarsa ta ragu sosai...

Yauma kamar kullum kwance yake acikin bahon wanka an zuba flowers masu tsananin qamshi acikin ruwan dayake wanka dasu, ya kasa koda mosti bare yae wanka hawaye yakeyi yana tunanin Hafsat metawa mutane? Dawa take fad'a?, police sunyj shiru da binciken inda ta shiga to yaya hakane?.."..

Kallon Anty reeda anty nasara tae tace "Wai matar tasa tana nan ne? Kike zancen an bugo IV?" Kallon ta tae

"To anty ina zataje tana nan mana?" Biki fa saura sati biyu ko d'inkuna bamui ba, Umma kuma tayi zancen kayan lefe" Zaro wayarta tae jikinta har rawa yakeyi, ta nunawa Reeda wani hoto

"Wannan dake tare dashi wacce suke ajikin wannan hoton atare wacece ita to? Nasha itace amaryar ai?" D'an murmushi tae
."Ba wannan nasani ba bari kiga wacce ze aura damukaje gidansu kina dubai" nan take ta nuna mata hoton islam jikin ta kuwa har rawa ya somayi ita anty nasaran ta kalli fareeda cikeda tsoro tace

"Nashiga uku sis, wlhy nayi hauka da shirme kuwa?" Qura mata ido tayi tana mamakin kalamanta kantace

"Ban fahimcekiba sis?"

"Kinsan na sanar dake banason auren nan,nakuma kira Maheer namasa magana akan ya janye yaqi, shine danaga wannan pic a social media nace to lallai itace, senawa er akuri sending lokacin zanje umra daganan na wuce dubai, tofa shine dana tura mata nace a sace yarinyar a tsoratar da ita sosai akan maheer, ni tunda tace ansace yarinyar ban qarawa hajiya maganar ba, jin anyi shiru ya sanya nayi tunanin yarinyar ta janye ne shisa banbi ta kaiba, amma bawai sace yarinyar dawowar danai shekaranjiya hajiya azumi ke gaya mun wai taga fuskarta ta farka musu bisa kuskure shisa ta sanya aka kaita jejin amanawa wannan mugun jejin aka manna mata igiya suka jibge mata kayanta anan, wai idan ta mutu ko oho basu suka kashe taba, to nima banji dadin hakan ba amma senace bani nayiba ko lahira banida laifi" Mamakinta ne ya sanya Reedah miqewa tace

"Anty Binta yaushe kika canja? Wannan wane irin mugun tane fisabilillah? Koda islam dince yanzu keba ruwanki kenan? Idan da ace Meerah ce zakiji kwanciyar hankali tana wannan jejin? Karfa ki manta ko masu shiga ciki seda tsafe tsafe haba anty Nasara wlhy baki kyauta ba, qyamar dakikewa talaka hartakai kiga kamar idan ya mutu ruwansa shisa kiyashi duk d'ayane a gunki? Lallai ma Anty" shiru ta danyi kantace

"Karkimun raini wayau Fareedah kinaji ba" zama tayi ta dauki wayarta tawa kanta sending pic din ta wtsapp sannan batama mata sallama ba ta fita..........

Mom Nu'aiym

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now