page 13

4K 335 20
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                          13
Ko kadan bataso Maheer ya ga fuskarta ba, sannan  menene alakar sa da wad'an nan mutanen guda biyu? Ina zata soma kai wannan tunanin daya taso mata rayuwar kaf a kewaye take da wasu abubuwa masu firgitarwa! Meke shirin faruwa da wannan rikitaccen circle data gani yanzu? Tana jiyo surutun su amma bazata iya fad'ar me sukace ba dan bataji duka ba, me suka zoyi to tagansu bayanta zuwa cikin gidan atare!!!!

************
   Tana shiga d'akin ta tarar dasu Mamanta suna cin abinci harda naman kaji an karramasu ta bangaren girki se duk taji kunya take cewa lemon baqinta ta siyo dazasuzo yanzu....tana nan khadeeja tazo kiranta akan ga angon da abokanan sa sunzo maganar kudin bikin dazasu bayar, tazo suje taso ta tirje mamanta tace lallai taje dole ta sauya kaya tare da d'ora niqafi saman firkarta kanta fice daga dakin zuwa inda en matan ke jiran ta ai zancen kudade!!!

Tunda ta shigo idan Maheer ke kanta so barkatai suke had'a ido, girjin dukkansu se tsananta dukawa yake hafsat kuwa duk yayin data tunano yanayin data shiga sanda ya furta mata muggan kalamai setaji tamkar ma taje ta shaqesa a wuce wurin kowama ya huta wani haushin sa da takaicin sa suke mata dirar mikiya arayuwa yanda takejin Maheer aranta bata zata akwai ranar dazata zo a rayuwarta da har zataji tsanar sa irin hakan ba, yanda ya kalli tsabar idan ta ya aibata ta da kalmar karuwanci abin yana mata ciwo matuqa!! Beji kunyar kallon mafificiyar Fuskar dake asaman tata ba ya kalleta kanshi tsaye yake kira mata wannan mugun abun datake ganin data aikata gwara mata mutuwar quruciya!! Miyar da dubanta tae zuwa ga Mahal wannan karon bazata iya jure kallon Maheer ba, shi kuwa dayasan itace se nacewa kallon ta yake wannan ya sanya ta tsargu ta miyarda kanta a qasa a haka a haka dai sukaita surutun su da en matan dake wurin akan programs da zasuyi amma hafsat batace kanzil ba....... Ummul ta kula sam Ameenu bashida niyyan barin su sui wani fitaccen bikin dazeje tarasa dalilinsa nasab zuwa programe ko d'aya ne...amma dai acikin mutane seka gagara cewa komai illah kallon su kawai kamar yanda Nancy tae haka itama tae!! Maheer ne yace

"Yanzu dai Nine zan dauki nauyin dinner da komai daya shafeta  seku tsayar da matsaya d'aya akan kudad'en da ake bayarwa na al'adarku nawa kuke ganin ze isheku" kallon Mahal Ummul keyi tasani tana qaunar sa soosai kurun dai tarasa gane inda zuciyarta keta wurgi da ita! Wanj zubin idan ta tuna mahal har kuka takeyi yau kam tafi ko yaushe rikicewa ganinsa tare da Ameen, amma bata nuna ba sam ga alama  shidin qani ne cox bataji bakinsa tunda aka zauna.....khadeeja ce tace

"To Ku fad'i dai nawa zaku bayar semu ji idan zeyi mana karmu fad'i abinda ze baku wuya" murmushi su Ameen sukai har Mahal ma dake wurin, shi tausayi ummul ke bashi kuma yanzu, sabida yana jin qananun maganganu gameda Ameen d'in  akan rashin sanin sana'ar sa gashi bashida mata yanata girma, yayi mamakin ma dasuke abota da Maheer sabida ya masa zarra har a shekaru sedai kuma Business men ne dukansu ba lallai bane ace se shekaru yazo d'aya zasuyi abota...Muryar Maheer ne ya qatse masa masa tinaninsa

"Waccen me Fuskar a niqafi ta bamu acc details ku saka kudin acikin acc nata, idan tace ya wadatar shikenan na kula ita zataji tausayin mu ita kad'aine bata magana" Dariya suka sanya dukkansu banda Nancy dataji bala'in takaicin sa kamar ta shaqesa seda Ummul tace

"Nanuwa ki bayar mana"
*"NANUWA"* ya qara nanata sunan a ranshi ita kuwa bataso akaji bakinta ba sam, da qyar tace

"Ka shirya in fad'a maka?" Tana bude bakinta yasoma tunanin yasan muryan amma seya kawarda wannan tunanin,Bayaso ya yaudari kansa.........Kallon ta yae kafin ya miyarda dubansa zuwaga Ummul

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now