page 49

3.4K 320 35
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

      49
Anwa Ummul aiki susscesfully an cire mahaifan gaba d'aya ta huta, sedai bata farfad'oba dayike an mata alluran bacci....'yan biyu se cancara qarar yunwa sukeyi dole aka soma musu da madara karsu jigata......

********------********
      Dukkansu sun kasa yin komai se kallonsu dasukeyi, hankalin Umman ya tashi ganin su a haka, tana zargi ko fad'a ne sukayi harya kai suka fad'a daga saman,sophie dake bacci acikin baccin tajiyo kururwan su wanda yasanya tai hanzarin  tashi ta sakko itama, itane tai jarumtar zuwa ta d'aga hafsat amma t kasa, tadai kula tana numfashi amma sam bata cikin hayyacinta, ita kuwa islam jini ta hanci da baki...hankalin kowa ya mugun tashi da taimakon securities na gidan aka wuce dasu asibitin su Fareedah inda umman da kanta ta mata waya, cikin gaggawa aka karb'esu  aka shiga duddubasu.....

    Hafsat kam ciwon tame yai mugun tashi se kuma islam data samu targad'e a kafad'anta da kuma k'afanta se buguwa datai ba laifi tad'anji ciwo sedai ba masu hawalan warkewa bane...kowa yarigada ya gama cewan islam ce taja tajata fad'a suka fad'o a tare se tsine mata ake, har aka kwana biyu suna asibitin ga kuma babu wanda aka sallama, amma ita islam da magana da komai tanayi har tashima dukda raunin k'afarta yayinda Hafsat ke cikin tsananin rad'ad'i da azabar ciwo sabida har yanzu batamasan inda take se dogon bincike akeyi akanta kasancewar tanada matsalan da ake neman ciwo kanta tun farko.

*Bayan kwanaki biyu*
      Kwanansu hud'u aka sallami islam, inda hafsat har lokacin shiru ko motsi, abincinma ta NG tube ake bata, sosai take shan wuya abubuwa sun mata nauyi a zuci........ Yau su maheer suka dira Niger ta jirgi suka zo a kano suka sauka, kai tsaye gidan islam suka nufa har ummul da Ameen, a d'ayan part d'in suka sauka gidan akwai tight security ya sanya suka sauka acen, beko lek'a wurin islam d'inba dama ya sanya kuku ya dafa abinci  da komai ya fice, yana matuk'ar so yaga Hafsat, yana sani ya shareta be sanar mata zancen tafiya ba sabida yasan condition nata tabbas zata shiga damuwa.

A sukwane ya shiga cikin gidan, yaje d'akin umma batanan, ya duduuba parlor na sama dana k'asa bata ban. Kai tsaye ya juya d'akin Hafsat, ya d'anyi knocking shiru kanya tura k'ofar d'akin ya shige  da sallama d'auke a labb'ansa, ganin ba kowa ya sanya shi juyawa yana tunanin ko tasamu sauk'ine sun soma fita, a k'ofar d'akin yaci karo da Gimbiya me aikin gidan, zubewa tai tana kwasar gaisuwa cikin k'aguwa ya d'aga mata hannu ya kuma ce

"Ummana da Hafsat fa?" Kallon shi tai.... Tana rik'e baki "Yallab'ai dama baka san abinda ya faru ba?" Gyaran tsayuwar sa yae cikeda mamaki, ko kan su taso yai waya da ummansa amma bata sanar masa komai ba, anty fareedah ma bayan ya iso sunyi waya amma komai batace masa ba

"Meyene ya faru kuma?" D'an jim tai batai magana ba seda ya daka mata tsawa

"Danla malama dake ake magan nace gayamun dalla dalla meya faru ne?" Cikin rawan jiki ga tulin munafurci na cinta, dan sarai taji uwar na gayawa k'awayen ta besan miyan da ake shaba tace

"Yallaba'i dama fa umman kane naji tana rok'an Anty hafsat akan wai su had'e kai acewa me gida bata sanka araba auren, injin umman wai bazasu barka ka nutsu ka samu kwanciyar hankali ba, kuma sannan islam ita takeda tsatso dakai dan haka ita ta hak'ura kawai dakai karka tsufa da wuri akan tashin hankalinsu, to daga sannan dai ban kuma jin d'uriyan anty Hafsan ba, sedai naji umman tanata dukan k'ofar d'akin ta tak'i ta bud'e se da yamma sosai Anty islam tazo tanemi ganin hafsat d'in akace tana sama, to dagacen dai dambe ya kaure a tsakaninsu suka gangaro daga saman nan har k'asa bame motsi, Alhamdulillah ita anty islam an sallameta jiya daga asibiti dan ta samu sauk'i ita anty Hafsan dai ko d'azu danaje asibiti kai abinci da driver gwanin tausayi ta hanci ake bata abinci" ta k'arashe maganar cikin share k'walla alamun tausayi" yama rasa mezaice mata ko kuma wane tunanin zeyi be tsaya cewa da ita komai  ba ya sakko daga matattakalar benen da gudun fanfalak'i zuwa mota, body guard d'insa naganin sa suka bankad'e masa murfin mota kai tsaye convey suka rufa masa baya da kusan mota biyar tasace a tsakiya suka bar harabar gidan me k'atoton gate har round about ne aciki, tafiyan kusan mintuna uku kansuje gate nan take ha wangale kansa sukai waje...dama yanada guards nashi baya buk'atar yawon dasune sam yanzu ma akan Alhj Baba ne basusan ta ina ze bullo musu ba...kai tsaye office d'in farida ya wuce, beko wani tsaya knocking ba ya bankad'e k'ofar, ita da umma ne da mijinta suna tattaunawa, dukkansu mik'ewa sukayi tsaye ganinsa yace cikin sauri

"Fareeda Hafsat fa? Tana inane yanzu" labb'anta sun gagara sanar masa tana ICH (Intensive care Unit) tana kwatanto hankalin sabyanda ze tashi inhar itama d'azu da akai refering nata can tasha kuka shifa dake tsananin san matar sa? Ta gaza furta masa kalma d'aya kowa se kallonsa yake, tunkan tai Magana yaji zuciyar sa ta tsinke ya gagara tsayuwa zubewa a wurin gaba d'aya seda mijin fareeda ya rik'esa

"Ka kwantar da hankalinka matar ka tana nan, amma bazamuji k'warin gwiwar sanar maka ba harseka bamu nutsuwarka ka kwantar da hankalinka gaba d'aya....kallon sa kurun yakeyi baya ko k'iftawa tamkar ze cinyesa haka yakeji

" inajinka tana ina yanzu?" Seda Dr. Ya g'yara tsayuwarsa sannan yace "ICH" Mik'ewa yai tamkar wanda aka tsikara ya nanata kalmar ICH a bakinsa sekace me koyon magana, da riverse ya juya da gudu zuwa wurin baya ko ganin gabansa, dukkansu da gudu suka rufa masa baya, har suka isa an hanashi shiga se cizge cirge yaje yanda yaganta daure da ox da glass ita kad'ai batasan inda kanta yake ba, ya kalli umman sa

"Umma keda islam ne ko, kina kallo islam ta wurgo mun ita daga saman ita tanacen tana hutawa amma Hafsat na na nan tanashan bak'ar hawala ko, ummana nine fa mahee d'inki yaushe kika dena san farin cikina? Naji komai daya faru a wurin Gimbiya, yaya yarinya batada lafiya kuma kin sani, da aurenta kaman daga sama kice araba? Wlhy ni idan babu hafsat arayuwa ta banga amfanin taba ma, ita kuwa islam kinsan tayi attempting kisa daga farko yanzu kuma kin dawo kin bata damar ke b'ancewa itada Hafsat again, ga sauran abinda kuka ragemun nan a kwance, wlhy umma ban tab'a zata zakimun haka ba, amma shikenan" kowa yai shiru yana sake sak'e a xuci yayinda ya juya kurun zuwa gidan islam cikin rashin kuzari, har aka isa bema sani ba seda tukunna suka ankarar dashi k'arasowar tasu ya fito, kai tsaye ciki ya nufa yaci karo da 'yarsa a hannun maid ya karb'eta yanata masa wasa tamkar ba komai a ransa yayi missing d'inta sosai, islam dataji sallamar sa ta fito seta tsaya kurun ta kasa ce masa komai, bed room nashi ya shige ya kwantar da 'yar ya rubutawa islam takarsar sakinta ya fito da babyn ya baiwa maid d'in ya bita d'akinta, mik'a mata takardan yai ta gagara karb'a a gefen ta ya ajiye ya juya mata baya

"Ga takardar sakinki nan, ban sakeki dan bana sankiba, Allah ya sani akanki nasan meye so kuma har gobe ina sanki, sedai bazan zauna da macen dake iya yin kisa ba, 'yata kije da ita sekin yaye ta tukunna ,zan k'arb'o abata, dummanin abubuwan dake ciki  Gidannan danke na siya ki tattare ki tafi dashi har motoci dake mallakinki, zan turo miliyan biyar a acc naki kimun renon 'yata, ki shirya da safe za'a maidaki sokoto" Wata uwar k'ara ta k'walla tahau magiya har waje ta bishi amma be saurare taba!!!

....\ko saki nawane akawa baiwar Allah, ko zaman ze k'ara dawowa oho.....muje zuwa

Pheey gobe da safe akwai wani inshaa Allah,inayinki tawan kina k'aunar littafinnan fiye da kowa dame rubutun gaba d'aya😀😀😀

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now