page 15

3.6K 367 33
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                          15
Tare da Ameenu yauma sukaje gidan su Ummul, wayar gafsat Ameenu ya kira ta fito suka gaisa sannan yace da ita

"Nancy en mata, an dinga b'oye fuskar nan acikin niqafi, keda ummul halinku ne ko ita seda nasha  daga ta dena nace fuska aiba al'aura bane,kin dinga qudundune fuska kenan a qyalle haba qanwata" Jin ankira hafsat da suna Nancy ya ankarar da Maheer akan Hafsat, tabbas ya gaskata zarginsa akanta itace qawar Islam, tun ranar daya ganta awurin karb'ar kud'in nan ya ga kamar yasan qwayar idanta,yanayin tafiyarta ma ya hadda ce ya soma zargin Nancy ce tun ranar gashi yanzu ma ya qara tabbatar da zargin sa...

"Yaa Ameen zan riqa rage sakawa inshaa Allah" murmushi yae

"Enhen kokefa lil sis, yafiye miki ai, kuma ranar dinner da kamu plus arabi'an night dazamuyi karna ganki da wannan hijabin idan ma bakida mayafai zan bada kudi aje asiya wannan alfarmar kawai kiyi kwalli kamar wayayyiyar mace nace buqata kiyi ranar shagulgulan bikin nan" Dariya tayi sosai seda gaba bakinta ya washe acikin niqafin har suna hango hasken fararen haqwarenta kanta ce

"Na siya wasu ai, inshaa Allah zanyi gayen an decently" dariya suka saka har Maheer.....

"Dama saqon d'inkunan tane na karb'o mata danaje abj tace ana mata dilke shine tace nakira layinki ki karb'a so ki bude bayan mota ki dauka" da murmushi ta amsa da "to" sannan ta juya bayan ta dauko tazo zata musu sallam Maheer ya kasa hakuri yace

"Wainikam Nancy bake bace qawar Islam?" Murmushi ta masa

"Au dama baka ganeni ba? Nice kuwa qawarku" fad'ad'a fara'ar sa yae ya kalli Ameen yace

"Dama wannan dakake ganinta ai d'alibata ce, ka barni da ita kurun akan niqafin nan, a class tafi kowa iya  kawo points amma iya muryanta kawai muka sani, muryan ma kaga tamu dabance da en gida dan wlhy ban shaidata ba se yanzu danaji ka kirata da suna Nancy dan haka frnds nasu ke kiranta dukda yake tun ganin farko qwayar idon yazomun da alamar sani"

"Kai haba kace mun zatasha carry over idn bata dena zuwa muku da niqafi ba" dariya yae yace

"Auu qanwar taka kakewa fata, qawar islam d'inace fa sosai kullum suna tare" da mamaki ya kallesa

"Wannan mara jin?" ga mamakin Namcy lokaci d'aya maheer ya had'a rai

"Yanzu sabida Allah seka kalli tsabar idona kace zaka gayamun koriya akan islam? Nazata kowani kaji ze zagarmun ita zaka tare, fiancee na be dace ace kaida kanka zaka zageta ba" murmushi ya wadata fuskarsa dashi yace..

"Allah huci zuciyar Abokina wasa nake, yanzu mu tafi kenan?" Be qara bi ta Nancy ba ya zaga ya shige gaban mota suka wuce, itakam dama tace wannan Maheer din be shaidata da kyau ba, daya ganeta sam dabaze sake mata ba yanda suka rabu ba arziqi a gidan sa zuwansu tare da Islam......

*************

    Durqushe agaban mahaifiyrasa yake ya qasqantar da kansa sosai yana sauraren abinda zatace bayan da yagama zayyana mata bayani gameda son auren islam kuma lokaci d'aya ya sanar masa rayuwar da islam tayi mara kyau da kuma tuban datayi sabida Allah, abubuwan dabe dace ta sani bane kurun be sanar mata ba.....d'akin nata ya d'auki tsawon mintuna goma bakajin qarar komai se bugawar zuciyoyin mutanen biyu secen ta nisa sannan tace

"Tabbas Maheer Zaka samu d'inbin lada idan kayi hakan musamman idan kayine da zuciya d'aya badan ka wulaqantar da ita ko tozarta da ita ba, kakumayine domin ceton al'ummar annabi ka rage yawan b'ara gurbi acikin al'umma, sedai fa ka sani  akwai qalubale babba agaban ka, kaga da farko dai akance yara sukan tsotsi ire iren abubuwan nan awurin iyayen su mata kaga matsala ta farko shine yaranka, na biyu kuma irin wa d'an nan matan sun saba da kashe kud'ad'e kamar ba gobe kakuma sani dukiyarka ta kasuwan cice bata siya sa ba, karkayi tunanin ana cewa aduk africa mahaifinka ne na daya a dukiya kakuma yi tunanin shine na uku a duniya ka sani komai yawan dukiyarka zata iya qarewa yau ko gobe kuma kud'i ayi amfani dasu ta tsafta tacciyar hanya, sabida haka nasan dole tazama me yawan buqatar kudi wa dan nan matsalolin sune abin damuwar dazaka duba amma ni bandaja ga hukuncin Allah, 'ya'yayen mu da muka gansu a shirye shirin Allah ne ba namu bane, idan Allah ya qaddari aure ka kasance me yawaita yin adu'a shiriyar wa 'ya'yayen dazaka haifa tunda kaga ita mahaifanta bawai sunyi yawon tazubar bane qaddarace ta haye kan ersu badon sunso ba, amma sakaci da addu'a yakan janyo hakan sabida haka ka dage ka kuma kula da er mutane, dan Allah idan kasan cewar zaka kawo er mutane ne ka wulaqantar da ita karka aureta , mahafinka  kuma ka rigada kasan bawai zama yakeyiba seyafi 3 month bezoba be kuma dad'e da juyawa ba sabida haka zan masa waya tare da adane abubuwan dabe dace yajiba na kuma san ze amince inshaa Allah" Dama beyi tsammanin suyi masa gaddamaba sabida kasancewar sa masu sauqin kai da fahimta da wannan yabar komai awurin mahaifiyarsa  ya zabga godiya ya miqe...

***************

     Bayan kwana biyu dayin maganar su ranar data fado ranar talata ana i gobe wankan amaryar matar Ameen mahaifiyarsa ta sanar masa amincewar mahaifinsa akan auren, tare da wakilta en uwansa akan zuwa neman auren tare da sanya qalilan lokaci acewarta washe garin yace aje.........

*******
  Kamar daga sama kuwa Ummul taji wannan labarin bakin mahaifinta wanda Maheer ne da kansa yazo ya sameshi ya masa bayanin komai kuma a washe garin sukazo akai komai aka sanya ranar auren nanda watanni biyu kacal!!!!! Wannan kenan.

***************
    Yauce ranar wankin matar Ameen kuma an cashe daidai gwargwado,kamar yanda sakkwatawa keyi da safe sukai salalli da magrib akai wankan na amarya se kuma washe gari akai bikin kamu

Ba kadan ba Ummul tae kyau kuma ta tilastawa Nancy yin makeup ma ko islam tazo musu bikin, haka suka tasa islam agaba da zolaya suka  kuma manna mata sirinrin mayafi shisa duk a wurin bikin a takure take ga maza sunzo ciki kuwa harda Maheer!! Ga wacce ta wadata wurin da abinci madam season 7 batasan kowa ba se Nancy so ita takewa nacin waza a kaiwa duk yayinda data miqe setakejin tamkar duk ita kae kallo.....tunda Maheer yaga wannan halittar hankalinsa ya tashi tunda yake be tab'a ganim mace me kyawun daya gani a fuskar Nancy ba, kai bama nan ba be yarda da love @ first sight ba se yau din nan, shibama kyawun ba yanayin murmushin datake zubawa ne ke dulmiyar dashi gefe d'aya kurin na kuncinta ke lob'awa haka kuwa ba qaramin kyau yayiwa fuskar tata ba, ga wushirya madaidaiciya dake tsakanin kyawawan haqwaranta!!! Wnnan murmushin yake bi da kallo ba fuskata ba, jin Ana kiranta da Nancy ya sanya ya ankare dacewar bega waccen ba kenan wannan itace Nancy?!!!!!  Ya tambayi kanshi

Mom Nu'aium

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now