page 30

4K 283 16
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

           30

Yau kusan wata d'aya da sati biyu kenan da haihuwar Ummul yarinyarta tayi girma sosai bazakace bakwaini bace, tayi kamar mahaifinta yamkar an tsaga kara, ita kuwa uwar se rama takeyi tamkar kud'in guzuri a tsorace take kwana sabida labarin dataji a bakin Naja akan kwace jarirai da ake a wurin iyayensu bata kuma san ina kaisu ba, shak'uwa me tsananin yawa ta shiga tsakaninta da Naja, taji labarin iyayenta aka dauka akan zaman dole takeyi anan kusan shrkaru biyar rabonta da gidansu, da iyayenta da dangi, tayita kokarin gusuwa amma ba hanya......

Hankalin Ummul baya jikinta EDD da aka bata kan azo da ita nan sauran shi sati biyu kacal, hakan yana nufin kenan zasu rabata Da NaNan ta zasu k'wace ta daga hannunta tosu kaita ina? In hakane tun yanzu ya dace ta keci jejin kota nemi dabarar yi sabida akwai matsala, ga mikin ta na haihuwa har yanzu da saura sabida rashin magani koda na hausa ne tana cikin tsananin damuwa me yawa ba er kad'an ba.

***************
      A parlor su sophie ne ke zaune suna hirarsu har Nancy wani zubin zakaga suna raha gaba d'ayansu tamkar basa gallaza mata, yauma hakan ce en matan uku se hira suke suna shewa dukkansu acikin kayan bacci masu wando iya gwiwa da riga me gajeran hannu amma tanada tsayi har socks suka sanya sabida ana tab'a sanyi a garin babu me d'ankwali acikin su, ita nancy ma tsawon sumar kanta daya sauka har cen bayanta ta tattaro zuwa gefen kafad'arta ya sauka ta gaban qirjinta, tana sanye da madubi sabida matsala da idanta ke bata akan yawan duba takarda suna hiran tana dannan wayanta.....zuwa wannan lakacin ta zama 'yar gida sun gama sakin jiki da Maheer ta cire shi aranta babu abinda take mai kallo se yayanta uwa d'aya uba d'aya, gidansu ne anan suke zaman hira musamman idan yaa Maheer baya nan.....islam ce ta shigo tana yamutsa fuska su sophie suka kalleta atare suka hada banda Nancy

"Sannu anty kin fito" murmushi ta musu

"Nafito en uwa ya kuke?" Murmushi sukayi shauty tace

"Qalau muke anty" kallonta Nancy tayi da murmushi a fuskarta

"Isy baby how body" ta furta tana gyaran zaman madubin idanta, yamutsa fuska islam tayi

"Yadai kamata kisan banbancin da dakuma yanzu, matsayin yayarki nake inda kikazo agolanci fa yayan su nake aure, ai ya dace ki ajiye qawancen mu nada ki gayar dani yanda kikaji kowa yayi bawai ki kirani da sunan raini ba tsabar izgili, amma bari yayan yazo zance ya miki magana ki san yanda zakimun magana, kina b'atamun rai gako Dr. Yace adena b'ata raina" sophie ma yau taji haushin wannan wulaqancin da islam kewa Nancy ita kuwa Nancy batace komai ba ta tattare yanata yanata tayi hanyar d'aki,tsaki ta bita dashi ta zauna wurin data tashi, ta tabbatar maganar da Anty Nasara ta fad'a Gaskia ne, wato dai Nancy ta manta halacci auren mijinta takeso tayi ko, itako kozatayi yawo tsirara bazata tab'a bari mijinta ya auti vergine ba gwara ya auro magajiyar karuwai, ko Umma ta gano bata santa arayuwa duk sunfison Nancy da ita tunda suke shirin auramai ita dabadan anty Nasara ba dabazama tasan miyan da ake yiba, amma ba komai wuya zata sanya ta gudu da k'afanta tabar gidan!!!

      Suma duksu sophie se suka bi bayan Nancy, a d'akinta suka sameta sophie tace

"Mesa wai ke adinga miki abu bazaki yi magana ba, me anty islam ke nufi dake zata rik'a kiranki agolar, ko agolancin kike aiba gidan ubanta bane itama" Murmushi tayi tace tana kallon sophir

"Ku manta da ita sophir duniya taga ta samu shiyasa, a turan nan Allah sa yaa Mahii  ya samu wata matar ya aura" ta qarashe maganar tana dariyar mugunta , sha'awa d'aka mata duka tayi a cinya

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now