page 7

4K 327 42
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

*Assalamu Alaikum, ina me baku hakurin rashin cika alqawari hakan ya farune sabida matsalar wattpad sena kammala typing seya share gaba daya, sabida haka nakega zamu miyarda posting book din idan anyi yau gobe baza'ayi ba se kuma jibi*

   
                       07
**********
    Zaman makarantar haka ya kasance cikeda wata iriyar shaquwa tsananin maheer damuka islam, kullum suna tare kokuma idan basa tare to kuwa suna nan maqale a waya amma Maheer betab'a furtawa Islam kalmar so ba....yayinda Nancy ke matuqar shan wahalar soyayyar datake wa  Maheer wacce ta tabbatar koda babu Islam baze so er qauye irin taba, kullum setayi kukan rashin sa da soyayyar sa datake neman illatar da ita, yauma kamar kullum tana zaune yana zuba lecture yana musu sallama akan se sun dawo hutu tunda sun kammala exams dinsu yau, ji tae wani zazzafan zazzab'i ya mata dirar mikiya, koyaya zata iya jure rashin Maheer na watanni uku? Koyaya zataji bayan rabuwar da zasuyi? Ganinsa kawai yakan saukar mata da nutsuwa sosai azuciyarta mesa zuciyarta da gangar jiknta basu mata adalci ba akan soyayyar Maheer? Ina ita ina shi? Ko bayan talauci batada wani gata a duniyar nan se Allah.....haka aka watse kowa ya fashe hannunta Islam taja

"Muje office d'in sir maheer yace na sameshi office" badan bataso ba amma tasani sabon ciwon zuciya kawai  zata samu sabida yanda Islam ke wani karairaya tana zuba shagwab'a kuma Sir Maheer d'in yana biyeta abin sam ba'a magana......

    Kallon kallo suka tsayayi na en daqiqu yayinda  kan daga bisani Maheer ya sauke ajiyan zuciya yace cikin zolaya

"En mata lapiya kinga fine boi kin bini da kallo se ince se an biyani kallo na da akeyi" shagwab'e fuska tae

"Allah ni Sir kaine kake kallo na, kuma kasan nafika kyau" murmushi yae yace

"Am dena yayin lukutayen mata ne silinda nake so kinji naga alamun so kike ki nanuqemun yanzu kuma meya kawo ki" murmushi tae ta zauna kusa da Nancy datae zaune tae quri da ido tana kallon su, kamo hannunta tae   tace

"Dan Allah Nancy nida Sir wayafi kyau? Kuma ina agabanki yamun waya kafin mushiga exams cewa na sameshi office" murmushi tae aciki niqafin ta tace cikin muryan ta me sanyi

"Qawata kin fishi kyau shima yasani ai, kuma mu bamuce munayi dashiba sadakin mu tsadanr dashi baze iyaba" kallonta yae karo na farko kenan dayaji tayi magana da raha kuma  me tsayi har haka yace

"Aini banasan lukutar mace, aje cen akai kasuwa" dariya suka saka dukkansu se yau yajiyo sautin dariyarta daya kusa kashesa akan yanda yaji yakeson yanayin dariyar ta cikin jan ciki murya can qasa qasa me taushi, kawar da wannan tunanin yae,cen kuma ya tsinkayi muryan ta tana fad'in

"Dama Lukutaye seme mota kaiko taya baka dashi, bana baiwa talaka qawata" dariyar suka qara sakawa  dukansu ya zauna kana yace yana kallon islam

"Issy baby nifa daga nan se kano, shisa nace kizo mui sallama, inshaa Allah yau kano ta dabo zan kwana, tunda aka soma exams banje naga umma na ba zumud'i nake" Ga mamakin Nancy Qwallah tagani a idon Islam harya fara silalo mata ta tsinkayi muryanta tana furta

"Haba mana dan Allah, ka bari se gobe kaji" ta qarashe maganar murya na rawa har tana langwab'e kai, a rikice ya d'an kalle ta

"Bana san kukannan Islam ki dena naji sengobe shikenan?" Murmushi tai ta soma share hawayenta

"Zan bika muje gidan ka tare yau muyi hiran bankwana" murmushi yae yace

"Ina godiya Issy baby" miqewa tae tace

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now