page 48

3.3K 309 14
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

             48

Kife rub da ciki ta fad'i, wanda k'aran data k'walla ne ya janyo hankalin wata mace da mijinta dake k'ok'arin wucewa acikin mota akanta, ganin mutum a kwance ya bashi daman yin reverse ya parka, shida matarsa a tare suka fito daga cikin motar, karen da yai tsaye akanta ya sona korewa kan su birkitota, sunyita jijjigata amma ko motsi sema jini da matarsa ta kula yana bin jikinta, yarensu ta masa suka kwashe ta suka juya acikin gari.........

**************

      Anty Fareedah ta kira a waya inda take shaida mata aiki takeyi zata nemeta daga baya, dukda yanayin muryan hafsat kurin ya isa ya nuna mata cewan da matsala sosai.....!!! A gaggace ta kammala ta patients sannan ta koma office dayake mallakinta ta danna masa key, farar rigar dake kan kayan jikinta ta zare tukunna sannan ta bud'e fridge ta d'akko ruwa a roba da cup tazo ta zauna ta tsiyaya tasha....zafi ake a agarin tana ganin tamkar idan Allah yaso ruwane ze sauka akwai alamun hadari a garin sosai kuma. Wayanta ta zaro ta danna wa Hafsat kira tana d'agawa ta soma yi mata kuka wiwi akan abinda umman tace da ita, ta zayyane mata komai a waya..ta k'ara da cewan

"Anty Fareedah seda aka gama yagamun budurcina sannan a miyar dani k'aramar bazawara dan Allah da manzan sa ki baiwa Umma hak'uri wlhy koda banasan Maheer ni ban isa nace inason aurena ya mutu ba, dan Allah ki taimakeni" shiru ne ya ratsa wayan na wuccin gadi, kan Fareeda ta nisa tace

"Nasan da maganar amma ban tab'a zata umma zata d'auki muguwar shawarar k'awayenta ba, da alama anty Nasara ce ta taje ta gaggaya musu labarin cikin gida dayike batada hankali, amma yanzu bari muwa tufkar hanci....Zan kira Abba kaina a tsaye in fad'a masa komai" Nisawa tai tana sauke ajiyan zuciya a hankali

"To Anty Nagode sosai Allah saka da Alkhairi" kashe wayoyin sukayi yayinda Hafsat ta kwanta a rigingine  tana kallon saman d'akin,abubuwa dayawa sun cunkushe mata, tunda ta had'u da Maheer abubuwa gaba d'aya suka tarwatse a rayuwarta, da farko dai karatunta a sanadin maheer ya tarwatse, k'awancenta da islam ma a sanadin maheer ne ya tarwatse, rabuwarta da gidansu sanadin maheer ne, duk talaucin gidan ubanka yafiye maka rab'e rab'e har ciwo tai na fitar rai akan shi, an mata auren dole akan Maheer ga wannan ciwon daya taso mata haik'an duk a sanadin maheer...yanzu ya k'arb'e mata abu mafi  girman daraja a wurinta sannan seta dawo bazawara akan shi?!! Kenan ya tattare duk ya tab'arb'are mata rayuwarta ya gurb'atar da ita? Lallai tarayyarta da Maheer ba alkhairi bace...

*************

     Da gaggawa aka karb'eta zuwa d'akin masu haihuwa a asibitin,  cikin kuma lokacin dabe wuce mintuna arba'in ba ta haifo yaranta biyu duka maza, abu mafi tashin hankali shine jinin ta daketa tsiyayewa harta fice a hayyacinta!!!

   Jikin Ameen ya soma ficewa tunanin maheer, zazzab'i sosai yakeyi lokaci d'aya ya fyad'e ya rame, wuraren sha biyun dare ya soma jijjiga wanda ala dole Maheer da wasu yaransa suka kwasheshi zuwa asibiti.....Neman taimakon jinin da ake ne ya zowa Maheer a kunne akan wata baiwar Allah me cikin da aka tsinta kuma ta haihu lafiya amma tanata zubar da jini ana sanya jinin yana ficewa, kalmar an tsinta ne yaja hankalinsa zuwa wurin wanda ya nemi ganin matar yanaso ya taimaka aikuwa yana zuwa se Ummul ya tarar rai a hannun Allah, beyi k'asa a gwiwa ba wurin gayawa Ameen da har lokacin be gama kammala mutum ba, ai kam tare suka koma dukda bashida lafiya, suka nuna evidence na cewar su en uwantane wannan ma shine mijinta, har hotunansu a tare seda suka nuna dake kan wayar Ameen tukunna aka masa bayani akan matuk'ar wai ba emergency theater aka mata ba aka cire mahaifar gaba d'aya to tabbas da akwai yuyuwar itama arasa ranta, be tsaya wani b'ata lokaciba sukayi signing aikam aka wuce da ita wurin opertion d'in..
Ba k'aramun dad'ine ya lillib'e Ameenu ba dayaga yaranshi maza har biyu kyawawa sosai.

************
   Islam ta tsorata ainun ganin kwana biyu babu Maher d'inta babu labarin sa, hankalin ta yakai k'ololuwar wurin tashi akan rashin sa, zuwa yanzu ta gama amanna ta kwantar da hankalinta akan Hafsat kurun shine mafita agareta su zauna lafiya tunda yake mijinta ba wulak'anci yake mata ba, tana cikin tashin hankali yanzu idan Maheer ya saketa waye ze aureta? Ai ita a duniya ta gama kad'ewa kuma har abada bazata auru a wurin kowa ba, ta yanke shawarar zuwa gun Hafsat tukunna ta bata hakuri wannan ne ya sanya ta shirya fita itada babynta zuwa gidan Abba.

   Babu laifi ta samu kyakyawar tarba awurin umma, inda kai tsaye ta buk'aci ganin Hafsat kuma umman tace taje tana sama, zuwanta k'ofan d'akin yayi daidai da fitowan Hafsat a shirye nasan zuwa gidan anty Fareeda sabida cewam datayi tazo....murmushi islam ta sakar mata wanda ya matuk'ar bata mamaki, rabon dataga fuskar islam da irin wannan murmushin tun suna school tanaga, kasa miyar mata da murmushin baya tai se zura mata idanta da tai tana nazarin ta, ba tun yauba tasan halin islam ciki da waje, ta san kalan murmushinta na yak'e kona gaske koma na mugunta, babu shakka duk sanda kaga wannan kalan murmushin shinfid'e a fuskar islam toko tabbad da gasken takeyi to meye haka kuma? Anya zata yarda da ita kuwa? Kodai umma ta gama yi mata bayanin raba auren ne? Shine take murna taci galadaba akanta? Idan haka ne ma bari tai mata na  yan duniya itama....

"Sannu issy baby, daga ina haka?" Ta fad'a tana me hak'waran ta cikeda k'arfin hali, amma ga mamakin ta setaga islam ta k'ura mata ido tamkar me nazarin wani abu, se kuma ta matso daf da ita ta rik'o hannun ta

"My Nancy kuka kikayi? Meya sameki ne?" Ta sani duk yanda takai ga b'oye damuwarta tabbas seya bayyana a idon islam, dukda haka gani tai tamkar islam d'in tasan komai dukan cikinta ne takeyi taji ta bakinta, wani irin k'ululun bak'in cikine ya tado ya tarnak'eta da arayuwa tanaga bata tab'a jin irin shiba tanaga, had'iyar paracetamol ne tayiwa k'ululun kanta d'ago ta kalli  islam sosai

"Menene ya ragu acikin gurb'ata rayuwata da kika sanya hannu akayi dabaki sani ba islam? Menene kuma ya saura acikin rayuwata da kike hari shima? Dukkanin shirin dakikayi akaina ai ya tabbata ko? Kinsan komai islam, abu d'aya nake gaya miki shine dukkanin abinda kai wa waninka nan ko cen sekaga sakamako, kuma wlhy wannan karon kam, na shirya d'amarar yak'i da koma waye akan mujina,  wlhy summa tallahi, mahaliccin sammai da qassai ne kad'ai ya isa ya rabani da mijina" kallon mamaki islam ke binta dashi harta kai aya, da k'yar ta lalubo kalmar

"Meyayi zafi haka Hafsat? Ni na isa na rabaki da maheer? Abinda ma na kula dashi  shine  sam kwanciyar hankalina dana aurena seda sanya hannunki zeci gaba da wanzuwa, farin cikin mijina kece ina ni gangancin cewa zan rba aurenku? Kumama ni awa dana isa na raba auren ku keda mijina? Nayi k'adan wlhy idan ma akwai wani abin dake faruwa ki yarda dani bansan komai ba, dq zuciya d'aya nazo miki, na dena d'aukan zigan kowa inasone muyi zaman lafiya" Harara Hafsat ta danna mata tukunna taja gajeran tsoki tayi hanyar gangarowa daga sama, kanta ne yai wani irin mugun sara mata ta dafe wurin islam tayi tsaye kurun tana binta da kallo, luuuu taga zata fad'i ta gangara ya sanya islam sake jakar hannunta ta bita da nufin tarota lokaci d'aya tana k'walla k'ara da kiran sunan ta, k'addara ta riga fata domin kuwa atare suka shiga gangarawan  seda duka gama gangarewa gaba d'aya, babu d'aya daga cikinsu dake motsi Umma data wanko da gudu itada da masu yin hidima agidan sukai cirko cirko....

Mom Nu'ayim

My pheey wannan shafin nakine, kiyi hakuri sekinga na safe.....

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now