page 4

4.2K 364 18
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                        04
A qofar office d'insa ta tsaya tana danna er qaramar wayar ta ta android qirar kamfanin techno bugu na y2 er qaramar alhakin data jima da fita yayi, wannan ya sanya sam batasan da zuwan suba har suka qaraso wurin, gayan murya Dr. Shema yae yayinda Maheer ya qurawa wayar dake hannunta ido sosai takesha maintenance wannan ya sanya sam bazakace tsohuwar bugu bace,a ninke take da leda me kauri duk jikinta gashi an had'ata da screen protector wannan wane irin maleji ne da tattali d'an tsiya? Sam wannan be dace mace ba koda yake wataqil laifin matsiyacin mijinta ne banda haka wannan tun yaushe ta fita a yayi? Gyaran muryanshi yae dan kanshi ya saisaita nutsuwar sa yabi bayan Dr. Shema ganin harya qure cikin office d'in.....da sallamar sa shima ya shiga yayinda Hafsat ta mara masa baya  tana me duqar da kanta wannan sabon malamin nasu yana santa gwiwowinta yin sanyi matuqa, wannan idan nasa suna neman razanar da ita gashi da kallo sekace maye, seya qura mata wannan gwala gwalan idan nasa baya ko qiftawa!! Ita kuwa duk sanda ta kalli cikin qwayar idansa se jikinta ya mata sanyi qalau, sallama tae Dr. Shema ya kalleta sosai yace

"Hafsag mesa kikaje class late abinda baki sababa" sauke idanta tae qasa dake cikin farin gilashin daya gagara b'oye kyawun idanuwan nata tace cikin sanyi

"Sir jiyanne na jima ina karatu har na raba dare, to kuma shine ko sallan asuba ban samu nayi ba da wuri se after 7 na farka a gurguje nazo nan sekuma nae rashin sa'a nayi late kayi hakuri" murmushi yae ya mayarda dubansa zuwa ga maheer da yae tsaye tamkar wani statue yana jin haushin Hafsat ji yanda take wani magana sekace wata sarauniya tana fitar da sautin d'aya d'aya....

"Malam Maheer dan Allah ka bata wani question's d'in tayi yanzu, nasan hafsat da san karatu bazatayi late haka kurin ba"

"Ok" itace kalmar daya furta kurun ya zauna ya zaro question's masu zafi har qwaya  goma ya danna mata, cikeda nutsuwa ta zauna ta zane takar dar da soshin ta masu gamsawar ta miqe ta bashi tana meyin godiya wa dukkansu, bayan fitarta ya qurawa takardar ido yana nazarin amsoshin daba'a gabansa ta zauna tsit  tayisu ba dabaze yadda  cewar dakai aka amsasu ba acikin mintuna goma sha biyar......ya yaba karatun yarinyar sedai shisam baya san mace me yanga koda yake ruwan mijinta tunda ko ba'a fad'aba daganinta kaga matar aure.....

***********
     A yangace Islam ta shigo lecture hall d'in tana tafiya ba abinda kake jiyowa se qarar takalminta qwas qwas qwas taku da d'ai d'ai da2 cikeda yanga daji da ajinta plus kyau na sura dama na fuska da Allah ya wadata ta dashi, cingom takeci amma ilahirin kumatunta lob'awa yakeyi, Maheer tamkar wani dutse haka ya tsaya yana kallonta koda yake d'aukacin mutanen dake hall d'in kallonta suke mata da maza kuwa, kasa korarta yae wanda ya baiwa kowa mamaki, kasancewar wannan ne karonsa na uku yi musu lecture amm sun lura 10mns yake idan time nashi yae kan yashigo kuma idan ya shigo baya bari kowa ya shigo amma yau yaya haka? Shi kuma a b'angarensa da qyar ya saisaita nutsuwarsa be tab'a ganin yarinyar a class d'in ba kuma course biyu yake musu to wacece ita?" Ci gaba yae da lecture d'insa yanda yafara tun farko a haka a haka harya kammala amma a rikice yake duk yayinda ya d'aga idanshi dan kallon d'aliban se idanuwansa su gagara kallon kowa se wannan baiwar Allah daya gani kusa dame niqafi a zaune (yanda yake kiran Nanuwa a zuci kenan) ......zuwa yanzu d'aliban sun karanci halayensa na san yin kiran register ma'ana seya kira sunan kowa bayan ya kammala lecture daya bayan daya idan aka kiraka seka fita hakan yae ko yau, ya kammala kiran kowa suka fice se mutum biyar daba sunansu a attendance na ranar.....mutum hud'u suka bishi suna roqon ya basu su rubuta amma fir yaqi saurarar su sedai tun a wurin ya kula me yanga (kamar yanda ya rad'awa Islam suna a zuci) bata bi bayan saba bayan ya tanbatar bata rubutaba sabida anfi 50 mns da fara lecture d'in kafin ta shigo ya kuma tabbatar  attendace ya jima da baro wurin da take, yarasa dalilinsa na damuwa da halin ko inkula data nuna wa attendace  d'in dashi ma baki d'aya.... Yafi 40mns zaune yana yaqi da zuciyar sa wurin ganin ya yakice tunanin salihatul islam a ranshi amma abun yaci tura ya fuskanci yana cikin damuwa akan baiwar Allah to kodai aljana ce? Banda  haka yaya zata zo masa class late ya gagara d'aukar mataki a kanta?  Yana tsakiyar tunanin hakan ya jyo knocking a qofar office d'in gyaran zaman agogon hannunsa yae ya kalli time sannan yace

"Yes come in" a hankali ta tura qofar ta shigo qamshin turarenta ya daki hancinsa ya lumshe idan sa sannan a ankali ya bud'esu ya dire a kanta bayan tayi masa tsayuwar d'aya ga wata a gaban teburinsa cikin wat murya dayake da tabbacin idan ya ci gaba da saurarenta zata tarwatsa masa tunaninsa tace

"Sir dama akan attendace ne nazi signing ban samu nayi ba" gyaran zaman sa yae yace yana me qoqarin had'e rai ya tsare gida

"Mesa baki yiba"

"Hanging nae a hanya nazo late yamun nisa" kallonta yae language datake usung kad'ai ya isa ya sanar maka cewar qwanqwasashiya ce yace

"Sekije kiyita hanging mana meye nawa aciki" hannunta ta sak'ala akan jakarta dake maqale a kafad'arta tace

"Na sakko ne ya sanya ka ganni anan sir Maheer, kai hakuri ka bani na zana abin dabefi mintuna biyu ba dan Allah ka bani" ya gano kanshi na shirin tarwatse masa idan ya daddage da sauraren muryarta wannan ya sanya ya janyo takardar ya bata....kallonsa tae

"Sir banida pen a taimakamun plss" ya gagara kallon cikon qwayar idanta shu'umin kallo take wurga masa baze iya jura ba kansa a qasa ya bata kawai, zanawa tae ta juya takardar ta fuskance sa ta d'aura biron akai tace cikin yanga

"Sir aikina ya kammala saura naka" be gane me take nufi ba sam seda tace cikin shagwab'a har tana maqe kafad'a

"Allah ni sir sekamun marking,naqi wayon" murmushi ya sub'uce masa dabe shirya wa ba ya daga biro yae alamar mark ajikin sunan ta, murmushi ta sake masa tace

"Nagode sir, Allah ya bar mana kai, dama kuma ina taso in gaya maka sunanka danaji abakin students yamun dad'i, inshaa Allah idan ban auri me suna maheer ba zan haifi d'a me suna Maheer" yaji dad'in kalamanta mutum ne me yawan san a yabawa wani abu nasa yace

"Nagode A jikin sunanki Naga kinsanya Salahatul Eslam, ni kaina sunanki yamun dad'i sosai, idan ban auri me sunan kiba zan haifi 'ya in rad'a mata wannan sunan kinji"  tana dariya ta juya masa manya manyan mazaunanta tae gaba,kasa hakuri yae yafito office d'in yana kallonta tare da ya gansu dame niqafi ko yanzu to menene alaqarsu? Wannan er gayun da wannan kidahumar er qauyen? Tab'e baki yae ya juya office d'in yana me ayyana kyawun jiki dana surar da Allah yae wa Islam.....

   Bayan la'asar ha fito qasan da yae parking domin ya wuce gida, acen daga nesa su Nancy da Islam suka hango tahowarshi suna kallo ya hude wannan farar qatuwar range din ya shige, Nanuwa tace

"Koda yike gulma ba kyau amma ina matuqar mamakin Sir Maheer, manyan motocin nan dayike hawa Anya malamin jami'a ze iya kuwa?" Dariya Islam tae tace

"Kinsan meya taka?, d'an iskan da iskanci zemun seda namai shu'umanci ya kame tsufansa ya adane" dariya tae

"Allahu ya shiryeki qawata, ni yau dinnan ma bacci nakeji wlhy, hostel zan koma kefa? ".......

Haka ya kwana tunanin Islam yayinda Nancy ta kwana tana tunanin Sir Maheer ta kasa gane alaqar dake tsakanin zuciyar ta da Maheer.....mesa zata damu dashi har haka, gobe sukeda psycholinguistic kuma tasan shiyake musu ta qagara goben tae bata da burin daya wuce ta ganta agaban Maheer tana kallon sa yanda yake rero lecture aka! Yake karanto abubuwa sekace shine yae kansa ohhhhh...........

Mom Nu'aiym

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now