page 35

4K 336 14
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham..

             35
Ranar kam islam fushi tayi me zafi,tama dena kula Maheer, shima d'in shareta yayi har washe gari yayi babu mewa wani magana, haka Nancy ta fito da shirin zuwa skul tana d'ingishi ita adole    waiga wacce taji rauni, Sophie se sannu take mata suka fita zuwa gate d'in gidan sabida normally sunada skul bus ita ke wucewa dasu to idan kayi late tana barinka sedai wata tazo, dayake yanayin karatun turawa ba irin namune babu ruwansu da d'an wane su kowa yana hawan bus ko taxi.....driver ya d'akko su Maheer shida Islam se cin magani sukeyi dukkansu, tsayar dashi maheer yayi akan su wuce dasu Hafsat, a gaba Sophie ta zauna yayinda Hafsat ta zaga gefen da maheer yake ta bud'e tana ta faman d'ingishi ta shige, Matsawa yayi tana zaunawa ta rik'o hannun shi

"Aauucchh yaa Maheer k'afara zafi" kallonta yayi zuwa yanzu ya soma fahimtar hadda raki acikin lamarin na Nancy hannunshi dake tsak'ale a nata ya kalla yace cikeda kasala

"Sannu ze dena ne"  k'ara matse hannunshi tayi ta kwantar da kanta saman kafad'arshi

"Inama ace yau banida test daba inda zani wlhy" murmushi yayi amma shi kanshi beji nutsuwar hakan datayi ba, d'an matsawa yayi kanta ya goce ta d'ago suka had'a ido sunfi 20 secons suna kallon juna ta had'e fuskar nan alamun yaya zakamun haka bece komai ba se k'ara matsawa kusa da ita da yayi ya kasa koda kwakwaran motsi mayar da kanta tayi saman kafad'an nashi ta kwanta tana wani basarwa, islam yi tayi tamkar bata gansu ba, yanzu ta gama hak'ik'an  cewa kanta cewar lallai Maheer neman Hafsat yakeyi, idan hakane sun cucesta kuma basu kyautaba ko kad'an.....sannan kuma bazata tab'a yafewa dukansu ba musamman ma ita Hafsat, seta tozartar da ita.......

*************

   Durk'ushe yake agaban Alhj Baba yana bashi hakuri amma k'ememe mutumin nan ya had'e rai

"Kai kana gani kamar kafini wayau ne? Yaushe ma ka taso akan harkar? Wanene kai? Nizaka guda akan matar ka? Dole ka kawomun ita in baiwa maza masu iyawa su mata ciki in biya bashin danaci danni kasan bana asara, mutane da yawa nake huld'an cinikayya na dasu sauran masu cikin na siyar danasu"

"Kayi hakuri Alhaj nabaka yarana sunfi 10 wannan iyalin tawa ita nake fatan qarasa rayuwata da ita har abada, nima inaso in samu magazai kamar yanda ka sameni kayi hakuri, zanyi wani auren semu haifa maka adadin dakake buqata kayi yanda kaso dasu" mari ya danna masa seda yaga wutar lahira

"Da Ummul nakeso, yaranta nakeso na siyar bana kowaba dan ubanka kai harkayi girman dazaka gayamun wai iyali dan kutirin uba" dafe wurin yayi ya mik'e tsaye

"Nagaji da kashe yarana, inaji ajikina bawani adopting nasu da akeyi tsafi kakeyimun da yarana,kaima namijine kaje kayita haifar yaran mana kana yanda kaso dasu,koda ba tsafin akeyiba ai turawa kake siyarwa kace, shikenan mu muna musulmai su sutashi a yahudu mucewa Allah me, wlhy nagaji da bauta maka tunda bakai bane Allah, bazan  kuma k'ara b'oye maka ba kaji na gaya maka, ka cutar dani ka gurb'ata tarbiyata Allah ya isa" mamakine ya sanya Alhj Baba yin sororo yana kallonshi har yabar gidan ya kasa koda qwaqwarab motsi...

*****************
   Kai tsaye gidansu Ummul ya nufa, yaje har huci yakeyi yana rarrashinta akan  bakin cikin dayake ciki seda yayi mata kuka, ita kuwa Allah Allah takeyi ta fad'a masa tanada shigar sabon ciki, har asibiti taje ma satin cikinta 7, koda ta fad'a masa murna awurinsa ba'a cewa komai sunsha murnarsu susu kad'ai sambarka.

***************
    Maheer yana cikin damuwa sosai, bayason yanayin islam gata da uban ciki, ta d'auki fushi dashi me zafi kusan kwanaki biyu kenan bata kula sa, gashi batacin abinci yana ganin kamar yanayin yanda Hafsat keyin abubuwa ya dace ace Abba ya bari a sanar wa islam zancen auren nan, besan dalilin Abba na yanke wannan hukuncin ba ace ko yayyunsa babu wanda ya sani, abun yayi yawa amma yazeyi shi awa yace Abba beyi daidai ba haka yayita zarya acikin d'akin shi kad'ai yana neman mafita, daga k'arshe ya kira Umma, itace ta buk'aci ya d'auke islam daga gidan zuwa wani gidan tunda ko rent ne yana halin yin hakan, tunda yake a London gidanne kurun dasu...sosai yayi Na'am da shawarar ta, batare da b'ata lokaciba yasoma shirin neman gidan gadan gadan...ba b'ata lokaci ya samu wani gidan  babu nisa da unguwar tasu ak'afa ma sekaje baka sha wahala ba, a parlor ya tadda islam ta had'e rai sosai ko kallonshi batayi ba  zama yayi kusa da ita yace

WATA FUSKADonde viven las historias. Descúbrelo ahora