page 47

3.6K 301 27
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

         47

Maheer ya shiga damuwa sosai akan Ummul, kwana biyu ma Hafsat bata ganshiba, yana tare da Ameenu suna gabatar da wani muhimmin bincike, har sun cafke yaran Alhal Baba kusan hud'u, da Alk'awarin basu Naira miliyan goma su duka su rarraba indai suka fad'i inda take, sun samu amsar tambaynsu da wannan.....amma sesuka ci gaba da tsaresu akan sesun tabbatar an ganta tukunna zasu sakesu.......

***************
      Islam tasha mamakin yanda yae, d'akinsa taje babu alamar ya d'auki suturunsa amma babu wasu dagacikin kayan dayake amfani dasu na toilet ko wani abu makamancin hakan, babu laptop da sauran kayan aikin sa, me hakan yake nufi? Ta tambayi kanta, bame bata amsa wannan ya sanya ta juya akalar tunanin ta zuwa neman anty Nasara..... Ringin biyu ta d'aga wayar cikeda isa tacr

"Sanadiyanki an hanani huld'a da kowa na zuri'ar mu, kin cuci halacci dason dana nuna miki mesa zaki kirani yanzu?"  Ta k'arashe maganr da tsawa sosai

"Kiyi Hak'uri anty Nasara wlhy ba laifi na bane ba, ko yanzu ina cikin tashin hankali, Inna na tace na rufewa maheer k'ofar tunda baya dawowa se dare, shine yai mun yaji motocinsa ma kaf basa gidan, dan Allah gayamun yaya zanyi" wani sanyi ne ya ziyarci Anty Nasara dama bil haq takeso ta wargaza auren, kan kuma tazo kan nanuwa dole seya auri wacce takeso ya aura d'in

"Kefa shine matsalar ki, bakida aji ko kad'an, namiji idan yace ze miki yaji aike seki dakawa shege barkono, wlhy dazaran yayi kwana biyu bezoba ki tattare komatsanki ki tafi gidanku seya nemeki da kanshi tabb" Nisawa tai

"Anty wlhy bazan iyaba, zandai iya shareshi amma ba zancen zuwa gida kam" tsaki taja ta kashe wayan gaba d'aya........bin wayan da kallo Islam tayi, ta fara tunanin wasu abubuwan game da Anty Nasara, bafa jahila bace iya, kodai da biyu take santa? Amma ko menene zata gano bakin zaren......

*********
     Yau dai jkin hafsat yayi sauk'i sosai harta soma en harkokinta, ganin nutsuwa ya shiga jikinta ya sanya umma tayi kiranta a parlor ta zaunar da ita, ta soka magana cikeda nutsuwa...

"Hafsat kinsan dai cewar koda babu auren Maheer akanki ke 'yata ce ko? Allah ne ya banike kuma nagode masa,  ba dole d'anda ka haufa acikinka shine d'anka ba koda wane lokaci Allah ze iya had'aka da yaro naka na kanka, to da wannan nakeso kibi hukuncina kimun biyayya" Tunkan a fad'i hukunci k'irjin ta ke masifan dokawa, amma ta gaza furta wata kalmar, gyaran zama Umma tayi kan tace

"A yanda na kula zaman lafiya tsakanin keda islam baze tab'a samuwa ba har abada, dalilan dazasu hana zaman lafiyan sunada yawa sosai a tsakanin ku, na farko dai kinga ni dake da kowa yasan cewan Islam tayi yawonta me muni kantayi aure, daga cikin mutanen dasukayi shaidar hakan kece mafi kusanci da ita kinfi kowa sanin wacece islam, da wannan hankalin kishiya baze tab'a kwanciya ba ace kishiyarta ganau ce ba jiyau ba akan karuwancin da kayi kafin aure yakuma kasance wai ka dawo ka auri mijinta, a iya hasashena iyalin Maheer bazasu tab'a zaman lafiya da had'in kai muddin kikaci gaba da kasancewa matar sa!!""" Da sauri Hafsat ta d'ago ta kalleta sabida yanda zancen ya doketa duka me tsanani, kawar da kai Umman tai gefe alamun itama ba'a san ranta take furta wannan maganar ba kantaci gaba

"Abu na biyu babu gaskiya ko kad'an ace mijinka ya aure k'awarka bada sanin kaba, kuma k'awance ma irin naku da islam, kinga duk inda akabi akaje aka dawo bamuda gaskia kuma mun zalinci yarinyar nan, nayi shawara da en uwana, da kuma abokanaina makusan tana akan cewar idan har ana so Maheer ya samu kwanciyar hankali da iyalansa tokuwa se an raba auren ki dashi" zamane ya gagari Hafsat ta mik'e tsaye cikin zare ido da firgici lokaci d'aya gumi ya soma tsatsafo mata , janyo hannunta umman tayi zuwa kan kujerar a kusa da ita tace

"Hafsat dan Allah ki tausayawa rayuwwar maheer, kar kwaramniya tayi masa yawa aka tsufan dole ya taso masa, keda bakida tsatso dashi ki bani goyon baya muce da Abba bakya sanshi a raba aurenku koda bayaso kodan kwanciyar hankalin dukkan ku" Duk yanda hafsat taso daurewa setaji kalama umma tamkar an watsa mata gaushin wuta a zuci, bata raba  wannan zancen na umma da labarin ranar mutuwar taba, kanta ne ya soma sara mata amma ta gagara furta wata kalmar...murya na rawa umma tace

"Karkiga kamar ina nuna sonkai ne, keda kike ta gari kece mace ta farko dazan sowa maheer amma kinga idan nace ya rabu da Islam mun cuceta ne" kallonta yanzu kam hafsat tai ido cikin ido, ita kanta umman ta hango tashin hankali shinfid'e a fuskar hafsat d'in....

***********

     Sosai Ummul ke faman yin nak'udar tsaye, koda wane lokaci cikin zullumi take da tashin hankali, ga wata k'atuwar bayarbiya dake yawan danna mata hannu ajiki da sunan wai karkato da kan baby zuwa k'asa, tana ansar uwar azaba akan hakan........ Su Maheer batare dayawa kowa sallama ba yabar garin kano zuwa chad inda shida Ameenu suka samu goyon bayan  jami'an tsaron chad d'in, da taimakon yaron Alhj Baba suka isa gidan....

Tunda Ummul ta samu damar sakawa me tsaron k'ofar datake ciki maganin dasuke saka mata ta dinga bacci se kuma baccin ya sureshi......... Matsalarta masu gadin k'ofar, hakan baze hanata neman mafita ba harse ta cimma burinta na barin gidan, zuciyarta ce take azalzalar ta akan lallai tabar gidan inba hakaba su hallakata ita da d'an cikinta, duk wanda ya sace mutum harya bari ya ganshi kuma ba manufar alkhairi bane a ranshi toko tabbas ze aikata kisa akan wannan mutumin kodan gudun tonuwar asirinsa akan lamarin......... Tana zuwa k'ofar parlor taga ba kowa, wannan ne ya bata damar soma tattaki cikin sanda da zumar barin gidan gaba d'aya, tafiya takeyi cikin sand'a har tazo farfajiyar gidan tana tafiya tana waige waige, me gadin data hango ne ya miyar da gabansa gabas yana rik'e da bindiga ya bata damar sauya akalar tafiyarta zuwa back yard na gidan ta b'uya, acikin shuke shuken furan nin dake zagaye  da bayan gidan ta b'uya atakure ga maran ta yana mugun murd'a mata sosai se gumi take had'awa.....batafi mintuna ashirin da b'uya a wurin ba taji ansoma d'aga murya ana nemanta...duk duka gigice wani har kusa da ita yake be ga ko alamar taba, wannan ya sanya  ta k'ara tsorata sabida taji suna cewan yace da zaran an ganta indai ta gudu to a harbeta!!!!!..... Kaf masu tsaron gidan ficewa sukayi daga gidan zuwa nemanta haik'an!!!! Sun tsorata sosai da rashin ta har me gadin, jn shiru ya sanyata fitowa tana ganin k'ofa a bud'e ta arce dama da yamma ne.....

Koda su Ameen suka iso babu kowa agidan gasu da tawagar en sanda, a tsammaninsu an musu munafurcine an sanar da zuwansu amma kankance kwabo meye harsun dawo gidan gasu aciki su a waje, haka aka dinga harbi suda police  an kashe kusan fiye da rabinsu, sannan aka damk'e sauran amma tashin hankalin shine babu Ummul babu alamar ta........hankalin Ameen yayi mugun tashi har baya ganin meye a gabanshi, kuka ya somayi sabida last hope d'inshi kenan, baya tsammanin bayan iyayen kud'in daya kashe da kuma zurfafa binciken dayayi akwai wani binciken daze k'arayi akan lamarin Ummul, a yanda yake lissafi EDD d'inta saura kwanaki uku in hakane watak'il tama rage EDD d'in ta  haihu an kashe masa ita an kashe kuma Babyn ta, yasha kuka da k'yar Maheer ya rarrashe sa.............

      Ummul kuwa koda ta fito taga acikin garine tan gararas se kurun ta arce..... Tayi tafiya me nisa, abinda yafi bata wahala shine cikinta, ga kuma babu mejin yarenta se d'aid'aiku gashi france suke amfani da ba English ba, ta kula mutanen garin ma basuda tausayi mafiya akasirin su, tayi kuka harta godewa Allah, ga dare yayi ga yunwa, ga ciwon baya ga batada ko sisi!!!!

************

     Mik'ewa kurun Hafsat tayi batare data ce kanzin ba ta mik'e da gudu zuwa d'akin ta.... Rufe d'akin tayi ta soma kuka tamkar ba gobe, tayi kukan harta gaji sabida harga Allah a matsayin macuciya tale kallon umma, seda aka gama yaga mata rigar mutun ci sannan ace za'a saketa?" Kiran wayan maheer tai amma baya tafiya ko nan da cen, batada labarin ya tafi chad ma....rana kam wuni tai tana kuka a d'aki ko abinci bata nema ba, bugun duniya umman tayi amma tak'i ta bud'e d'akin.

***************

       Tafiya ummul keyi batare datasan ina take wurga k'afar  taba, yunga ga azabar tafiya, ta kulama ta soma barin cikin garin zuwa jeji jeji..... Karene ya bita da gudun fanfalak'i se surfafa gudun takeyi tamkar ba gobe, karo tai da wani abun atake ta fad'i wurin a sume!!!!!

Mom Nu'aiym

Fan's kui hak'uri, munata bikine nima ba haka nasoba ko kad'an wlhy, amma kuyi hakuri inshaa Allah tunda gobe wunine kawai zakuna samun daily update. ..dan Allah ku gafarci er mutan galadanchi.love u..

Meenaty wannan shafin nakine ina miki son so fisabilillah...k'aunarki agareni babu ya ita...

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now