page 24

3.9K 355 41
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                           24
Se yamma ya qara yin waya gidan nasu aka kawo abinci, sukaci sannan suka nufi asibiti wurin Hafsat.... Bayan sun tsaya yamata umarni da taje ciki yana zuwa, kifa kanshi yayi saman Staring motar tasa ya runtse  idansa, yana da damuwa sosai akan yanayin daya riski Islam, ya sani ya shiryawa hakan kuma ya tabbatar wa kanshi ya samu gamsuwa me tsanani a tattare da islam to amma ya rasa dalilin damuwar sa akan riskarta matsayin cikakkiyar budurwa, yana ganin hakan baya rasa nasaba ne da kasancewar sa me tsananin kamun kai da kame jikinsa ga matan banza, ya sani Fasiqi se fasiqa amma a wannan lokacin yana kyautata zaton banda wacce ta tuba! Yana kallon islam a matsayin mace mafi tsarki aduniya baya jeranta ta a matsayin  fasiqan mata, kasancewarta kamilalliya a yanzu Allah ne ya masa zab'inta kuma shine yawa alqawarin bazata tab'a ganin wani wulaqanci daga wurin saba danwai be sameta a matsayin budurwa ba, yawa kanshi alqawarin har abada indai ta wannan  b'angaren ne bazata tab'a ganin wata alama daga gun saba ta rashin jin dad'i koya wulaqanta tata ba har abada......cikin damuwa yace

"Allah ka sanya islam ta shiryu kenan har abada, dazan samu wannan dana riqe islam har abada,idan zan iya bada shaida a lahira dasena bayar da ita acikin mata mafi salihanci na duniya"...... Kashe motar yae ya fita waje ya nufi d'aki, acen ya tarar da islam zaune tayi tagumi ita kuwa Nancy ta qurawa tv dake d'akin ido tana kallon wani film...gashinan an sato wani yaro yanata tattalin qwacewa shima seya raja'a da kallon cen kuma se aka qwalawa yaron kwalba akai nan take ta qwalla qara me tsanani ta had'e da dafe kanta, atare sukai wurinta suka ririqeta se ihu takeyi, Islam kuwa  itace tae qarfin halin fita waje neman Dr., a d'aya b'angaren kuwa  likitan dayake wani dakin duba patient qaran dayaji ya gayyato sa zuwa d'akin, seda sukai karo da islam da sauri yanufi kan Nancy ta gagara nutsuwa ta kwantar da hankalinta se ihu take, cikin gaggawa ya sanya aka kawo masa allurar bacci ya danna mata kana ya nemi ba'asin yanda abin ya faru....Bayani Maheer ya masa, yae murmushi ya dafa kafad'ar sa

" karka damu  inaga mun soma samun nasara zata samu memory d'inta, hopefully ma yadawo gaba d'aya" Nisawa Maheer yayi

"Allah yasa hakan, daka duba qafanta  naga tayita jijjiga" Nanma murmushi yae

"Lapia lau qafan take karka damu kaji" bece komai ba ya miyarda dubansa zuwa gareta yana nazarin yanayinta,se yamutsa fuska takeyi  dukda bata cikin hankalinta alamun akwai abinda ke damun ta.....

*Bayan sati hud'u*
      Acikin wa en nan satitiitkan Hafsat ta samu sauqi sosai, kuma tana magana sedai abinda muke tsammani na dawowar memory d'inta abin ya faskara ci gaba d'aya ne ta soma yin magana, kullum Maheer da islam wurinta suke wuni zamu iya cewa rayuwar amarcin Islam ya k'arene awurin sintirin asibiti da jinyar Nancy, Baba azumi dai taqi zuwa haka Ummul laulayi takeyi me matuqar bata wahala yayinda take samun tsananin kulawa awurin Ameen....Batada kowa  se islam da Maheer su kad'ai ta sani su kad'ai take gani, acikin satin nan d'aya jal gaba d'aya  islam bata zuwa asibitin   sabida zazzab'in datakeyi, damuwa sosai take ciki akan yanayin yanda Aunty Nasara ke mata wulaqanci da nunin wariyar launin fata, a shekaranjiya ta sanar mata karta yadda tayi ciki ta haife musu dan tsohuwar karuwa tayi kukan wannan maganar harta godewa Allah amma sam bata gayawa Maheer ba, wannan dalilin ne ya sanyata jin zazzafan zazzab'in daya kwantar da ita, tayi dana sani me tsanani na  halin rayuwar data aikata a baya, ta kuma kasa sanarwa kowa dama ace Hafsat d'inta nada lapia dama ace 'yar uwace bata rasa tunanin taba data gaya mata ko zata samu sassaucin abin da takeji......

***************
    Maheer yayi wata shaquwa me tsanani da hafsat da har  bayason zuwa sokoto kullum idan zeje seyasha fama, ganin tana masa rigima ya sanya yau yace baze ma sanar mata ba ya shirya ta tafi abunshi ya barta da islam, se dare ita kuma ta barta da Inna wacce dama hayarta sukayo domin tana kwana tare Hafsat d'in.....kwana biyu hafsat bataga maheer ba ta soma yiwa islam rigima akan yaa maheer kamar yanda taji qannin sa na fad'a idan sunzo mata dubiya... Da q'yar islam ta shawo kanta ta dena rigimar hadda kukan ta kuwa, abun ya matuk'ar dami islam, ta kasa gane alaqar zuciyoyin biyu, shima a b'angarensa hakanne ko waya ya kira Hafsat ze fara tambaya' yauma kamar kullum tana tsakiya da tunanin nan wayarta ya shiga ruri ko bata duba ba tasani Maheer ne ko daga yanayin waqar dake tashi....karawa tayi a kunne bayan data d'aga kiran a hankali ta furta

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now