page 12

3.6K 322 19
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                          12
Yafi mintuna talatin yana nazarin maganganun islam se cen ya dawo ya zauna ya muskuta da kyau yae gyaran zamansa yace

"Amma islam kina cikakkiyar sallah biyar awuni kuwa" dukda bataji dad'in maganar ba amma seta tsinci kanta da bashi amsa  kamar haka

"Ina yi mana Maheer, meze hana nayi saah na taso agidanmu an koyar dani tsare sallah akowane hali"  jinjina kanshi yae alamar gamsuwa

"Amma kuma bakyayi akan lokaci islam" shiru ta d'anyi kan tace

"Ea to anan bazanyi qaryaba wani zubin  se magrib nake yin azahar da la'asar dinma gaba daya senai maja" kalonta ya qarayi

"Amma aka gayan miko cewa haka ake sallah? Idan fa kabari lokacin sallah ya wuceka da gangan kashiga uku islma, mesa zaki miyar da rayuwarki kamar ta marasa ilmi? Kina ganin ko wannan rashin kiyaye sllah akan lokaci baze jefaki ajikin ibtila'in rayuwa ba? Ya dace ace kisan cewa ba'awa sllah hakan ai, wanda ma yake hada salloli yaushe zega time din yin adu'a tukunna ma yaushe rabonki dayin azkhar? Kokuma ki zauna kiyi karatun alqur'ani me girma tayaya zakiga haske islam?" Shiru tae tana tunani ita wlhy tun quraninta na islmaiyya bazatace ma ga inda yake ba, ko na app da ake turowa a waya bata taba ajiyewa ba kuma ita abinda yasa bata ajiyewa shine sabida yanayin abubuwan dake kan wayarta, soda yawa idan taje wurin gardawan bariki setayi kallon fina finan batsa takejin sha'awa, sannan wani zubin idan taje wurinau sesu shagala da zancen sallah ta kula dan zaman nan datae agida sosai take sallah sam bata wuceta to kenan duk musababbin shigarta wannan halin hadda mugun abun nan datakeyi....seda ya qara cewa "kinaji kinyi shiru islam nace  yaushe rabonki dayin karatun alqur'ani ko Azkhar? Hawayen dake kan fuskarta ne ya sauka tace..
" bazan iya tuna tuna tun yaushe ba Maheer" nisawa yae yace

" Manta wa da Allah tamkar qulla qawancene da sheda islam, baze taba barinki ki mori tsufanki ba, zega yanda duk zeyi ki lalata quruciyar da hannunki ta yanda tsufanki baze miki kyau ba, kazalika  koda kin mutu kafin tsufan ki shige wutar Allah, banji dad'in yanda rayuwarki ta kasance hakan ba, dukda kome kika aikata a rayuwa tare da Suraj za'a raba a baki naki kason shima yaja nashi, ga kuma haqqin ki na cutarwar daya miki gashi shine mutumin farko da kika nemi ya aureki sanda nace kiyi hakan,  ki kasance acikin istigfari ako da yaushe kije gida yanzu sena qara neman ki kuma" sakkowa tai tabi gwiwowinta tana kuka tace

"Ka taimakeni Maheer  ka rufa asirina, ka aureni wlhy idan baka banida amfani" murmushi ya sakar mata yace

"Kije gida karki damu My Islam zanzo gidan idan na dawo kinji"  godiya ta masa ta miqe yace

"Zoki karba ki riqe a hannunki banaso wata buqatar ta taso dazaki nemi wani abu awurin wani" sadda kanta a qasa tae ta kasa koda motsin kirki bare ta karbi kudin seda ya mike ya saqala mata a hannu sannan ta juya Kamala ya dauki hanyar gidansu da ita!!!!

************
         Yau auren Ummul saura sati d'aya wannan ne dalilin dayisa gidan nasu ya qara kaurewa da hayaniya da ihun mutanen qauyensu da en uwa dakuma abokanan arziqi!! Ummul na zaune tana d'aye selotop dake tafin qafarta bayan ta gama cire lallin gargajiyar data saka, farar qafarnan ta d'akko jan lalli se sheqi takeyi! Ata gefenta qawar Ummul ce Khadeeja  ke mata zuba

"Yanzu ke Nancy meya alaqanta ki da lallin gargajiya za'ai biki a gidanku? Bakya jin  kunyama kizo muje gun zarah uwar zane mana ranar laraba ta zane mana hannayen mu da qafafuwa dubu uku ce kun rabu lapia" Kallon sosai ta mata tana murmushi

"Zanjene ai kurun dai dama dole wannan nake farawa dashi, shisa ma nakeyi da wuri danna cire a tare" murmushi tama tai ta sunkuya sosai tace

"Wai nikam Hafsat Anya ke ba balarabiya bace? Wlhy danice ke da duniya seta gama ganin wannan surar tawa, sumar kanki kawai seta b'ata wa mutum lokaci wurin kallon ta nifa aduk cikin jikinki banga inda Allah ya kuskure miki ba dama kuma shiba me kuskure bane yasan daidai...ummul ita muke zuzuta kyawun ta amma wlhy Nancy bawai buzuwa ba babu wanda baze yarda cewar keba balarabiya bace idan ya ganki" sakin lallausan murmushi tae .

"Khadeejahh abeg jeki kiyi sallah abinki" ta qarashe maganar tana dariya......itama khadeejan juyawa tae tana fad'ar

"Anyi baqi daga Niger naga wata mata me kamarki ga alaama maman kice" murmushi tae ta zata wasa ne yasa bata kulata ba seda ta gama tae alwahala ta nufi d'akin Baba Azumi.....

Acen ta tarar mamanta da qannin ta sunzo mata...Baba iro ne ya aika suzo dan ya bata haushi sabida taga yayi kudi data gujesa, acewar sa dan bashida kudine taqi zaman aure dashi yayanshi dayakeda abin hannunsa ai basui haka ba ta zauna..... Murna a wurinta ba'a magana  sam, mamanta ma taji dadin ganin ta se yare sukeyi na Buzayen Niger  Baba Azumi se harare harare takeyi tana yatsina fuska!!.....

**********
      Duk saurin datake   ya hanata d'aukar niqafin ta ayau dinnan, dama wasu lokutan takan fita acikin unguwarsu hakan......murna sosai takeyi tanaso taje ta siyawa mamanta Lemu tasani akwai lemuka agidan taga ko abinci ba'a baiwa har qannin taba, bazata jira yaran su mutu ba da yunwa murnan ganinsu ya hanata shiga b'acin ran an hanasu abinci.....a qofar gidansu tae karo da Mahal da Maheer a tare suna hira sun haye saman motarsu ta baya sunata tafa hannu suna murna qirjinta ne yae mugun dokawa ganin yanda dukkaninsu suka zuba mata ido tamkar wacce qwai ya fashewa a ciki haka ta dinga wurgo qafarta  tana kusanto gate din gidan dauke da ledar lemo a hannunta...kanta qaraso Ameen yayi parking zuqeqiyar motarsa ya fito ga mamakin ta wata qara suka saka shida Maheer ya diro daga motarsa yana  ihun "MAZAJE!!!!!" Suka tungume juna bayan sun tafa yace

"Ango kasha mai" dariya Amin yae "Tunkan akai Amaryar kake cewa nasha mai ya akai ka gane gidan harka rigani qarasowa" kallon Mahal yae yace

"Wannan yaron ne qani nane dan wurin qanwar mahaifina ne anan suke zama shine muna tare dayaji kana kwatantamun yace ya gane wurin" murmushi yae shima

"Ohk sannunka shima semuje dashi ai, wannan al'adar ta sakkwatawa dame tae kama ace se an maka taron en mata sun fadi adadin kudaden dasuke so ka basu" dariya Maheer yae yace

"Tunda al'adar suce aisemu hakura, namata waya tace suna masaukin baqi  na waje muje kawai" wucewar Nancy ne ya dakatar dasu duka ukun suka bita da kallo, dukse ta tsargu aciki Mahal ne kurun yasan fuskarta amma Maheer da Amin basu santa ba bata fata su santa ma se idanta da suke gani..... Maheer da qirjinsa ya ninka dukawa ganij cikin idon daya taba sani yace da Amin

"Aboki ko wannan ce amaryar?" Dukan bayansa yae

"Ko alama tawa matar taci uwar wannan a kyau da komai, baka ganin wannan da yanayin qauyawa" dariya sukai dukkansu ya sake cewa

"Qanwar matana ce fa, nasha ganinta da wannan kayan na jikinta so am sure itace ma" kallon sa Maheer yae

"Kayan kawai fuskar fa?" Be kulasaba sukai ciki ita kuwa se d'aga qafa takeyi zuwa cikin gidan kamar zata kifa.

Mom Nu'aiym.

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now