page 28

3.9K 334 14
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
    
                            28
Washe gari tayi mamakin ganin an tasheta tun asuban fari kuma  ance tayi wanka, 6:30am suka fita susu biyu, mamakinta yanda Maheer da kanshi ke tuk'i agarin kuma babu inda ya b'ata yasan kan garin kamar cikin gidansu.... Wata Makaranta taga sun shiga me d'an karen kyau da tsari, kai tsaye wurin shugaban makarantar sukaje yamai bayanin komai da harshen turanci inda yace sesun mata interview...Ba jinawa aka kammala komai kuma kai tsaye ta lula level 1 a b'angare  low a makarantar me sunan Brilliant university makarantar su d'aya dasu Sophie kenan su suna level 3 inda sophie ke bibiyar medicine ita kuma sha'awa  ke karantar b'angaren zane zane........

***************
    A waya yake sanarwa Abba k'udirinshi nason dawowa Uk din shima, seda yayi wani dogon nazari kanya amince masa da hakan, yana jiyewa yaron fadawa business irin nashi na rashin lokacin iyali kwata kwata amma yana masa fatan alkhairi.

    Kwance yake akan kujerar dake parlor d'in yana kallon tv duka tunanin shi da hankalinshi yana gun islam, d'azu dasukayi waya yaji muryan ta cen k'asa alamun tanajin jiki b'oye masa kurun takeyi, baya ga hakan ma yanaso ya kasance tare da matarsa sabida  yana missing nata.....Lumshe idanshi yayi ya k'ara budesu a hankali acen k'asan zuciyarsa  kuwa yana wani tunanin ne na daban sam ya gagara dena tunanin daya zamto masa tamkar numfashin sa, idan Abin da yakeji gameda islam so ne to lallai ko yana sonta so bana wasa, amma inhar ya kasance abinda yakeji gameda  Hafsat shine So to kuwa da banbanci tsakanin so dakuma k'auna sabida ita har cikin jijiyoyin jikinsa yakejinta, tana masa zagaye acikin jini da b'argon sa, takasance itace numfashinaa dayake shaqa yana mata *Son so* wanda babu irin shi, yana mata k'auna  wacce mizani yayi kad'an ya aunata sabida duk girmansa ta masa nauyi, yana jin dad'in sauti da amon muryarta tamkar itace ta farko ta kuma k'arshe acikin halittun  a irin jinsinta a duniya, tafiyarta tana burgeshi takan d'auke hankalinsa xuwa wata duniyar daban yakanji tamkar bow legs d'inta sunfi na kowa   masu irin nata kyau, seyaga kamar kyau ma suka k'arawa tafiyar ta, idan yana kallon d'an siririn hancin ta seyake ji tamkar ya dinga jansa a hankali yana wasa dashi, idanta masu ruwan zaiba aciki yake k'ara narkar masa da duk wani kuzari ya rasa katab'us idan beyi tunanin taba, k'wayar b'akin idanta ke d'auke hankalinsa yayinda ya kalleshi ya hango kanshi aciki, seyaji inama zata bashi aronsu su zame masa madubi dan harga Allah yafi ganin kyawun kanshi acikin d'igon bak'in idan nata, Duk sanda kumatunta ya lob'a kuwa idan tana cin abinci ko dariya kota yamutsa fuska, jiyake yi tamkar yaje ya sanya dan manuninsa acikin ramin yana mata wasa dashi, sumar kanta ke k'ara hura wutar abubuwan dake damunsa akanta, yakanji inama ace ze samu damar shinshinar sumar kan nata, ya shak'i k'amshin kan nata yanayin kwanciyar sumar nata yana nuni sosai da tsantsar tsafta kota yanda yake zuba sheqi......yarasa makama ya rasa madafa, ya ayyanewa ranshi komai nata burgeshi yakeyi daidai da yatsun hannayenta dake zara zara da nails masu kyau farare masu d'igon ruwan zuma a k'asan su, lumshe idanshi ya k'arayi a karo na barkatai, wannan yarinyar tana shirin wargaza masa lissafi,tanaso ta rikita tunaninsa ta tarwatsa masa kansa......da wannan ya miqe domin barin gidan kwata kwata, sabida harga Allah yana so ya yakice ta a ranshi, tasan sirrin islam!! Tasan wacece islam koda yayi nasarar auren ta baze tab'a nasarar zaman lapiyar su, ita islam bazata ji dad'in rayuwarta kishiyarta tasan seda ta gama yawon duniya aka aureta kuma sanin na sosai ba rumours ba, ita kuwa Hafsat zata dinga goranta mata hakan koda wane lokaci kuma yasani a wurin yara ma se ansamu haka ga Islam na shrin soma zazzaga masa yara agida......

******************
     Matashiyar dake tare da ummul ce tace da ita cikin fusata

"Baiwar Allah kinfa isheni da tambayoyi marasa kan gado!! Bake bace mace ta farko data fara zama anan gidan tare dani, kece ta biyar idan ma zaki kwantar da hankalinki ki kwantar dan bakida hanyar fita daga nan gidan, nida kaina na gudu yakai so bakwai amma da k'afana nake dawowa sabida wannan gidan dakika gani duk kyawun shi a jeji ne muke rayuwa, wanda bashida farko bashi k'arshe dubin duniya idan zakiyi bazaki gane komai ba ta inda ze sadaki da wani gari ko k'auye..... Idan kika kwantar da hankalinki kina haihuwa zasu maidaki inda kika fito, dama kwad'ayi ne ya kawoki kuma nasan kinci naki rabon da duk wacce bataci ba bata zuwa nan, sabida haka dan Allah da manzansa ki rufawa kanki asiri ki nutsu ki haife musu yaron cikinki ki huta da rigima" kallon rashin fahimta ta mata, ta rud'e sosai dajin wai yaron cikin ta zata haife musu!! Suwa?... Ta tambayi kanta, bak'in ciki tamkar ze kasheta da rud'u ta kuma durk'usa mata

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now