page 23

3.8K 356 30
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                           23
Bayan sun kammala wayar ne kuma tana tsakiya da kukanta mahaifiyarta ta shigo ta zauna gefen gadon ta kalleta

"Salaha lapiya dai? Kukan me kikeyi ne haka?" Share hawayentabtae tace tana murmushin yaqe

"Dad'i nakeji zakuji dad'in rayuwa ta dalilina akan auren da zanyi Inna, Maheer ne ya bamu gidansa daya tashi yace mu zauna anan garin, be furta yace kyauta bane amma dai yace mui mooving ciki Inna bakiga gidan ba ya had'u wlhy gidan  masu kud'i ne fa" murna innar ta shigayi tana rarrashi akan abin farin cikine ta dena kuka kantace da ita

"Dama Nikuwa salaha cewa nai zancen kawo kayan lefe naji shiru har yanzu, en uwa sun soma tambaya kinsan mutane" Murmushi tayi

"Bam masa magana ba tukunna amma barin masa waya" Yana wurin Hafsat ya kasa ya tsare seda yaga farfad'owarta yana tsakiyan mata sannu yaji qarar wayansa.....Ganin islam ce ya sanya ya fita waje

"Baby" shine abindabya furta bayan d'aga wayar

"Ina wuni honey?" Yana murmushi yace

"Lapia lau my baby, hafsat fa ta farfad'o" se yanzu ta gane dalilin dinga fadan shi d'azu akan bega hafsan ta farfad'o bane, farin cikinsa yanzu kuma akan ta farfad'o ne

"Alhamdulillah Allah ya qara mata lapia" shine abinda ta furta tana murmushi

"To Babyna how far meye a qasa" sakon barkwancin da yae ne ya sanya ta saki jikinta takumaji sanyi a ranta, itadai tana matuqar qaunar maheer...

"Honey dama cewa nai zancen kayan lefe najiku shiru kasan a nan kafin biki ake kawo wa" Dafe kansa yae shap yama manta

"Dan Allah baby kuyi hakuri, kinsan Allah wlhy na manta ana lefe a aure ma, kumafa umma na kullum setayi maganar ranar da twin tamun magana ranar aka samu labarin hafsat duk wannan abun ne ya mantar dani yanzu kinsan meze faru,barin wa umma waya inyaso kinga sena kiraki back yanda mukai" Bataso jin hakan daga gareshi amma setace.

"Ba komai dear, sena jika" haka ta ajiye wayar ta kalli mamanta

"Ammm Inna wai akwai shirin dasukeyi amma ze kira mamanshi yaji inyaso seya kirani muji yaushe zasu kawo" murmushi uwar tayi

"To kuma zancen kud'in saka lalle da wankan amarya shifa yaya za'ayi? Ko kaya zasu kawo ne?" Nanma yaqe tayi tace

"Na manta dubu dari ne ya bayar suna nan acikin jakana" Gud'a uwar tayi ta karb'i kud'in tafita waje tana murnar an musu qoqari ta samu kudin yin kayan tuya na gara!!...

****************
     "Ummana yaya maganar kayan lefen nan ne wai, kinga ni na shafa wlhy" Dariya tae har yana jiyo sautin muryanta tace

"Mahi auren nan sekace dole aka maka, waya tab'a manta kayan lefen matarsa? Kaga nifa enkai lefe nakan hanyar sokoto yanzu ma haka sun mun waya akan suna kan hanyar shiga layin su a unguwar....dama Fareedah bata sanar maka ba tare fa suka tafi, itada qawata da qanwar mahaifinku" Daria yae

"Nayita neman layinta beje ba kuwa, to Allah ya qara girma ummana nagode sosai"..

           Kallon kayan aketayi ana mamakin had'uwarsa da uwar dukiyar da aka narka zani babu na qasa da dubu 25 komai yaji, tsayawa fad'ar dukiyar dake cikin kayan lefen ma bata baki ne, Islam tasha mamakinsa har taji kunyar hakurin data kasayi tayi kiranshi sabida kamma su gama wayar aka soma sallama ana shigo da kayan.

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now