page 8

3.7K 326 29
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                            08
Seda ya fita daga gidan yae parking motarsa ya d'aura kansa saman stiring motar ya soma miyarda numfarfashi a hankali, hannunshi yakai ya lalubi kuncinsa yaji shinwai da gaskene abinda yakeji qwallah yakeyi? Yaushe rabon da yae kuka a rayuwar sa? Ya manta whly akan wata yau gashi yana kuka wannan wace irin jaraba ce? Yafi mintun 30 a wurin  batare daya san time ya tafi har hakan ba!!!!!!

************
   Eshmal dan Allah ka kaini tasha, nahau mota akwai uzurin daya tasomun yanzun nan aka kira ni daga gida, kafita rakiyar friend dinka, namaka alqawarin zan dawo da kaina idan komai ya lafe" da zargi ya kalli fuskarta ta d'auke kanta gefe d'aya tana nazarin yanayin sa

"Ka taimaka Eshmal ka kaini kaji, wlhy akwai damuwa fa!!" Mamakin jin da yae muryanta na rawa ya kama shi,yace

"Subhanallah kaddai mutuwa aka muku" daganan ta samo qaryan dazata mai

"E mama nane batada lapia shine zanje gunta ance sosai ne" 

"Ayya toki shirya muje ko, Allah ya bata lapia amma to abincin fa, ki danci ko kadanne mana"

"Banida appetite ka kaini tashar kurun"...... Haka suka fito cikin qasa da mintuna 30 a bakin hanya ha hango motar Maheer da plate an rubuta Sidi dala range 12 wacce ta baro compound dinsa yanzu, gangarewa yae ya parka ya fito yamai knocking d'agowa yae bayan daya zuge glass din yama manta aduniyar me yake, kuma ya manta yana kuka ma, mamaki ya kama Eshmal uace

" Subhanallah friend, menene ya samu haka da sauri sauri kuka fa" se a sannan ya tuna ya share qwallan sa yace

"Kasanni da raki ai, bawai kuka nake ba muddin dai ina numfashi wani abu namun ciwo senayi qwallah, ina baro gidanka cikina ya murda shine na paka anan se juyamun yake" kallon sa yae cikin tausayi yace..

"Ayyah toka kawo na qarisa maka da motar acikin gidana sena direka gida kanka samu sauqi driver ma yaje ya miyar maka motar gida"  kasa yi masa musu tabbas ze iya fad'uwa ya mace idan yace zeyi tuqin nan.....haka ya fito ya miqa masa key ya nufi motar sa, mamakin ganin Islam yae ta sadda kanta a qasa batasan meke faruwa ba batama san da zuwan saba, kwantacciyar sumar kanta data sakko har wuyanta ya kalla ya tabbatar ita dince dan haka nata zubin yake ya bud'e gidan baya ya shige bata koda d'agoba tana cen tana kuka tana sauke numfarfashi a hankali kukan me sauti takeyi me ban tausayi, leqowa Eshmal yae yace da ita

"Sweetest barin je na sauke motar friend d'ina acikin gida nazo, cikinsa yana masa ciwo baze iya tuqi ba dan bani minti daya nai parking nazo muje" gyad'a masa kanta kurun tae, bata gano ma Maheer yake nufi ba shi kuwa ya dawo tsakiya ata bayan motar ya qura mata ido ko qiftawa bayayi har Eshaml ya dawo ya miqa masa key karba'a kurun yae ya tura aljihun gaba rigar sa

"Yaya cikin? Yana raguwa yanzu?" Gyad'a masa kansa yae ba tare dayayi magana ba, shi kuwa bayan ya saisaita motar kan titin seya d'aura hannunsa daidai ta bayan wuyan Islam yace

"Karki damu sweety, inshaa Allah  maahmaah zataji sauqi kinji, ki dena kukan nan karkizo kiyi mana ciwon kai a banza" bata d'ago ba, shi kuwa maheer yabi hannun Eshmal da kallo yanaji tamkar ya dauki adda ya datse matsa wutsiyar hannun dake gangancin tab'a masa islam d'insa....katse masa tunani ya yana meci gaba da murza bayanta a hankali yace

"Maheer ka ganta nan se kuka take tunda ka fito aka mata waya mamanta batada lapiya sosai" Da sauri ta d'ago jinya ambaci Maheer amma seta gagara waigowa ta kalle sa shi kuwa yace da kyar

"Allah ya bata lapiya, zata samu sauqine inshaa Allah" batai magana ba dai Eshmal ya qara riqo hannunta, yace

"Ki bani acc details naki zan tura miki 200k nasan aikin dakikamun ba dare ba rana yafi qarfin hakan, wannan ba ladan aikinki bane kije asiya maman me sweet magani, ladan aikinki da yamma zan tura miki" kasa d'aukar maganganun kunnuwan Maheer sukai yace cikin qarajin daya baiwa su duka biyu tsoro

"Kaiiiiii" parkawa Eshmal yae yace "Maheer lafiya kake kuwa kodai muje asibiti naga alamar ciwon cikin nan naka baze barka ka huta ba" cikkn baqin ciki yace

"Dan Allah ka kaini gida, direni gida tukunna kankaje inda zaka kaji" beyi musuba ya karkata akalar motarsa zuwa lameed'o  crescent domin diresa gida, yana tsayawa yafita a motar Islam ta bisa da kallo, had'a layi yake kukanta taci gaba dayi harya kaita tashar ya biya mata drop na qaramar mota ya bata 20k tasha ruwa a hanya yakuma yimata alert na 200k kai tsaye, yauga kud'in amma basuda amfani agareta, har suka isa sokoto kuka takeyi......

Tana isa gidan su innar ta dake wanke wanke ta miqe da plate a hannu tace

"Ernan bikin nan har an gama, bacewa kikai se litinin ba?, naga duk kin kumbura a fuska wani abin ne ya faru?" Lumshe idanuwanta tae tace

"Ba komai innah zazzab'i nakeyi yasa na gudo gida kai tsaye ba'a gama bikin ba yau asabar ake wuni, gibe bud'an kai" jinjina kai innan tayi tabi bayanta har d'akin, bayan sun zauna a bakin gado tace

"D'azu lamimi tazo nemanki, wai yaronta baida lapiya babu kud'in dazata kaishi asibiti nace bakya gari amma na bata dubu d'aya" murmushi tae na yaqe tace,tana kwanciya

"Akwai kud'i a jakana ki aika mata dubu biyar yau bana jin dadi innah, karki bari su faruk su tasheni idan na shiga d'akina" batace komai ta miqe tana murna yau tasan zasuci kaji tunda Islam taje biki......

***********

     Part d'insa ya wuce yaje yayi kuka harda majina, yanawa islam wani irin so dabesan dame ze fassara saba, wannan abu da idansa ya gane masa yau besanya yaji ko gyazau ba game da yanayin dayake ji akan qaunar islam, b'acin ransa d'aya ta karya masa alqawari ta siyar masa da jikinta me tsada arha banza, awurin fasiqan bariki tausayinta yakeji yanda ta lalace, batun yauba ya kula Islam tana yawon banza amma babu abinda yafi dakar mar zuciya kamar wannan mugun abin dayaji yakuma gani, be shigar kallewa islam jiki yanzu ba, be shirya ganinta a yanayin daya ganta ba yau, dama yayi niyyan auren ta koda kuwa karuwan ci take aganinsa yayi jahadi!! Menene ke shirin faruwa da soyayyar sa? Yayi kukan harya gaji bame rarrashin sadole yae shiru!!! Yakoma kukan zuci...

**************
       An kammala gyaran gidansu Ummul, ya dawo acikin jerin gidajen da ake lissafawa na masu kudi acikin unguwar ta lowcost, su ummul sun tare hatta Nancy ta samu an ware mata d'aki d'aya dayasha ado da kayan more life, wannan karon kam har qaramun plasma ne manne a d'akin na Nancy da wardrop gado dai set dan Niger me kyau!! Duk wannan daular duniyar nancy batajin dad'in zaman gidan nasu ko kad'an cikeda tashin hankali take na rashin Maheer, yaudai tayi shirinta tsaf na soma zuwa Catering school na billy galadanchi wanda takeyi a unguwar su na arqilla, acikin gidanta take koyarwar ta gaji da zaman ko oho datake agidan nasu, ada takanyi girki yanzu kuwa en aiki sukeyi an zauna daula, tanajin labarin wannan me koyarda girki ta ruga tae registration domin tana qaunar fannin girki gashi ko alihi bata iyaba banda abincin gargajiya daba laifi Baba Azumi ta koyar dasu!!.....a daidaita ta hau har zuwa gidan domin yaune zasu fara tarigada tayi registration da kud'ad'en da Maheer ya bata kanya bar garin.....tana sauka adaidaita wayanta ya soma bulayin neman dauki...dakatar da komai tae ta d'auki kiran na qawar ta islam

"Hafsat nashiga uku na" shine abinda ta furta tana kuka, hankalin hafsat ya tashi tace tae hakuri zata zo gidansu idan ta kammala da school aikam ana idarwa ta wuce gidansu nanuwa.....babu abinda ta b'oye mata komai seda ta sanar mata dake faruwa from A to Z abinda ya faru, nanuwa kanta ta girgiza  tace

"To yanzu dai Islam kiyi hakuri na san zezo miki jibi saturday semu bashi hakuri" kallinta tae

"Tun ranar yau kwanaki kusan 5 be qara kirana ba, ni kuma gagara kiransa" shiru Nanuwa tae kan tace

"Zezo miki a lokacin dabakiyi tsammani ba ina gaya miki karki damu kinji?" Haka tae ta bata baki har yamma kanta wuce gida akan washe gari juma'a zata dawo...

Mom Nu'aiym

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now