page 36

3.6K 299 11
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

               36
"Kema Hafsat sekinyi hakuri da abubuwa da yawa yanzu, idan kika biyewa zafin bakyason Maheer kece zaki wahala, karki kuskura kiyi tunanin yin zawarci da k'uruciyarki kada kuma ki bari amiki k'wacen miji sabida wlhy ke zaki wahala, k'awarki 'yar duniya ce kuma ta fahimci wani abu yasa take miki hakan, karki bari a fahimci akwai aure tsakaninki da Maheer dan idan Aunty Nasara ta sani yanzu kuna london kece zaki wahala, Anty Nasara yayatace amma koni ina tsoron mugun halinta, wannan ya sanya nace ki rike adu'a da azhkhar, ki kuma hakura da kalmar baso a aranki ki rungumi mijinki, koba komai ke baki san komai ba akan tarayrayar maza ita kishiyraki fa? Meye bata saniba meye bata iyaba? Ki kama kanki ki kama mijinki ki cire wannan zancen na yayi  amfani da kud'i wurin aurenmi kinjini ba" D'an turo baki tayi

"Anty Fareedah agabana yake wani kakkama matarshi, yana mak'ale mata amma ni ko oho, su dinga bani wahala sekace jaka shimafa basona yake ba, so kike yace ninake binshi ina zubar da ajina, ko jiya Allah banso nayi abinda kikace ba banaso ne kurun ranki ya b'aci" Dariya Antyn tayi

"Hafsatuwalle kenan, kina bani dariya wlhy ninasan wannan k'unk'unin da kikeyi duk kishine ba komai ba, kina so kina kaiwa kasuwa" Tabare fuskarnnan tayi tamkar suna tare

"Haba mana anty wane irin kishi kuma niba wani kishi wlhy, yanzu fa dazasu wuce konemana beyiba se fitowa nayi babusu a gidan kuma ko waya be nemeniba, ni ai sanda mamana ke sokoto tana auren Baba iro naga raba kwana akeyi ko" Sosai anty Reedah tagano Nancy cike take fam da uban kishi da soyayyar da batama san tanayiba.......murmusawa tayi

"Kece zaki kirashi da kanki kimai shagwab'a akan be nemekiba, da k'afarsa ze dawo, haba mana k'anwata ni rgimar nan dukni akewa alhalin kuma bani nakar zomon ba"

"Ni se anjima anty" Dariya tayi 

"To anjima zaki kirani koni na kira"

"Duk yanda akayi anty, nafa gaya miki sun tafi abunsu kuma ke dariya ma kike ni wlhy kowama ya tsaneni, ace wai yaa Maheer yafison islam dani, ya dauke matarsa har yana ce mata wai bayaso ake bata ranta shisa ze dauketa" Rigiman hafsat na baiwa fareeda mamaki, idan ka ganta kamar bazatayi ba

"Kinga kiyi hakuri gaskiya be kyautaba, zanmq yi masa fad'a akan hakan kinji"

"Ni bance amar fad'a ba, kurun dai kice dani be kyautaba shikenan" murmushi ta qarayi.

"Be kyautaba gaskia kiyi hakuri kinji"

"To Anty nagode bye bye" kashe waya fareeda tayi tanata kwasan dariya, k'uruciya masiface kana kishi bakama san kanayi ba Allah shi kyauta.

****************
   Be ragewa ummul komai ba gameda yanda sukayi da Alhaj Baba, ya qara da cewar

" Ni nasan Allah dole ya jarabeni da masifu iri iri ummul, seda k'arfin gwiwarki nake nema ki bani, gwarin gwiwa ki kasance tare dani komai rintsi, ina cikin ibtila'in rayuwa, nasha auren mace in kuma barta da wasu k'artin banzan suna yanda sukaso da ita, abun yana masifar damuna sosai yanzu, gashi kema anaso a tattab'amun ke, wlhy tallahi ummul zan iya kashe duk wani namiji daze tab'amun iyalina, bama keba babu mace koba matata ba dazan zura ido ayi fasikanci da ita, nasan halin Alhaj Baba idan yayi niyyan yin abu, kuma nasan kema kinajin tsoro sabida haka tunda kunada en uwa Niger inaso ki koma cen keda Naja da Ummami" tausayi ya bata ta shafi kanshi

"Zan koma duk inda kace mijina, ina fatan zaka kula da kanka, kuma kana yawan yin istigfari dan Allah, kasan Allah yana yafewa bawa zunubinsa komai girmansa indai ya tuba ya dena gaba d'aya" Rungumarta yayi

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now