page 19

3.3K 319 20
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

                       19
Kai tsaye fareedah gidanta ta nufa tae wanka tae salla ta zauna ta qurawa wannan pic d'in ido ita sam ta kasa nutsuwa akan wannan maganar, yaya zaka dauki rayuwar d'an uwanka musulmi ba komai ba? Ko rayuwar arne babu wanda yace  ka dauka ka kashe kace kaci bulus maganr nan da daddy keyi akan qyamatar talakan da Anty Nasara keyi har yaje wannan wurin!! Yasha yin fad'a akan korar mutanen datake yi  idan sunzo masa, yakance mata yana tausayin ta kar wata rana wannan qiyayyar datakewa talaka ya janyo mata wata musibar, gashi yanzu ta fara gani tunkan aje ko ina, sabida tsabaragen iskanci da sonkai gashi nan ta soma safarar mutane....."Bazan iyaba!!!" Ta furta a sarari da d'an qarfi ladiyo me mata aiki tace

"Na'am hajiya, Magana kike ne?" Murmushi ta sakar mata na yaqe tace....a gayawa d'an liti ya shirya zan fita, wayarta ta d'auka tawa Maheer waya yana d'agawa suka gaisa tace

"Kana ina ne zamui magana dakai ne"

"Shirin zuwa sokoto nakeyi ko ince nama kammala sokoton zani"

"Idan na roqi aron awa daya zamui magana ban takuraka ba maganar tanada muhimmanci ne" murmushi ya sakar mata tamkar tana gabansa

"Ba komai anty Reedah bari nazo"

"Ka zauna kawai ni ganinan tahowa gidan naku" sallamah sukai ya zauna a parlor part dinshi yana nazarin dalilin reedah nasan ganin shi cikin gaggawa haka, yaga dai dazu dazun nan suka rabu, shikamma zewa sokoti shigar dare dan yanzu qarfe biyu ta kusa haka ya zauna wurin 30mns kanta iso........ Quryar dakinsa  taja shi mahaifiyarsu nata murmushin ganin ana gudunta da zanje ta wuce dakinta abinta..... Zama sukai sannan ta kalleshi

"Sorry lele na b'ata maka lokacin ka ko?" Kallonta yae bece komai ba ta zaro wayar ta, ta lalubo hoton dayake tare da Nancy sunsha kyau kamar ango da amarya an dauki hoton daidai lokacin da dukkansu suka daga qafarsu daya da zummar takawa suci gaba da tafiya kana ko wannensu dauke yake da murmushi a fuskarsa se glowing sukeyi........ A hankali ya karb'i wayar ya qurawa hoton ido hoton ya masa kyau ainun ya burgeshi hanun shi yakai ya miqa dan ya tsarsa d'aya  ya tab'a saitin dimple nata d'aya daya lob'a besan yaushe hawaye ya zubo masa ba harga Allah wani tausayin ta yaji ya kamashi sabo fili, farkon b'atanta yakansa hotunanta da videon rwarta agaba ya dinga kalla amma yanayin azabar dayakeji a zuci game da ita ya sanya ya dena amfani da wannan wayar zuwa wata, akwai wani waya dasukai da dare shida ita sanda ya mata hidima a gun finner take mai godiya mistkenly ya danna record sanda suke wayar bemasan ya shiga ba se daga baya dayake duba wayanshi yaji shima yakan kunna ya dinga sauraro gwanin tausayi😭😭....... Kallon sa Anty Fareedah keyi cikeda mamaki ya shagala da kallon hoton amma ya gagara ce mata cikanki!!! Matsawa tayi kusa dashi ta riqe hannunsa d'aya ya d'ago ya kalleta tace

"Wacece wannan Mahi?" Ta kirashi da sunan dasuke masa wani zubin ko ince yakusa ya zama sabon en gidan wato mahi......

"Anty qanwa tace, kuma kusan watanni biyu yanzu kenan da b'atan ta, ko bekai biyu saura kad'an....ta b'ata b'at anty wlhy, an nemeta an rasa sama da qasa" qura masa ido tae na wasu en daqiqu bilhaq kuka yakeyi kuwa lallai ta b'aci sabida tun suna yara maheer yakeda qarfin hali wani zubin komai girman dukan dazasu masa baya kuka harya girma kuwa baka ganin kukansa sabida dauriya har wani zubin sukan ce masa Biggest soldier.....hannu takai ta share masa qwallan sa akwai shaquwa me tarin yawa tsakanin sa da Fareedah tare suka tashi shekaru biyu ne a tsakanin su Twin brother take kiranshi shima yace mata twin sister har a waya haka sukai saving number's na juna.....

"Twin kuka kuma, menene tsakanin ka da wannan yarinyar da kakewa b'atanta kuka, am pretty sure cewan she's not d first person daka samu labarin b'atan ta"

"Anty Reedah wlhy mutunci yaufa muna tare gobe aka ce dani ta b'ata kuma shikenan fa anty ko labarinta babu, gwanda ace ta mutu ai ko" tausayin sa taji

"Qawar kace?" Qwallan shi ya sanya yatsa ya d'auke

"Qawar islam ce, kuma student d'inane, beside munada shaquwar wuni d'aya a tare, bama wannan ba kallon sister na nake mata tamkar ke da sauran en uwana ina qaunar yarinyar nan" shirune ya ratsa  d'akin na wasu en daqiqu ya nutsu sosai yana kallon fuskar ta....muryan reedah ya tsinkaya tana magana

"Twin akwai damuwa fa" kallonta yae

"Mecece damuwar Twin sis?" Sadda kanta tae a qasa

"Anty nasarace tasanya aka........."daga nan ta kwashe komai ta gaya masa tun yana gane zancen ta har ya zamana meji amma kurma sam baya ganewa, babu dalilin aikata hakan agun anty Nasara sabida selfish interest nata kawai  seta b'atar da d'an adam qwaya d'aya jal!! Jejin Amanawa!!! Ya nanata hakan a zuci se kuma ya miqe kamar wanda aka tsikara ya kalli reedah

" Anty fareedah wannan yana nufin kenan tuni Hafsat ta mutu aljanai ko namun jeji sun cinye ta ko?" Riqo hannun sa tae

"Calm down twin pls, inshaa Allahu Allah baze bariba wanda suka kaita cen ai muta nene, suba sun dawo ba? Inshaa Allah yanda suka dawo haka zamu nemota ta dawo itama kaji" duk da AC dake bayarda ni'imtacciyar iska me dad'in qamshi hakan be hana shi had'a gumiba,  ya kalleta a karo na barkatai yace a yamutse

"Anty Reedah da tana raye aida an ganta tuni kusan watanni biyu fa cur?" Tausayi ya bata ta kula cewar akwai shaquwa sosai a tsakanin su kasa magana tae ya sake cewa

"Barinje in gayawa umma wlhy Anty Nasara seta gane kuskurenta har daddy zan kira yaji wannan rashin imanin da ta yi" miqewa tae ta riqeshi

"Karka soma zo muje gidanta kabi komai a hankali kaji"  haka sukaje gidan a hanya se rarrashin sa takeyi  har suka isa....

****************
   "Amma anty binta hakan yayi kenan, da islam d'ince se ki mun asarar ta,kina nufin kenan dan abinda nakeso yana talaka bazaki tayani sonsa ba matsayina na d'an uwan ki" harara ta wurga masa

"Dan ubanka ninace maka abinda akayi laifi nane? Na samar da reedah dataje ta d'akko ka y'ar akuri ce ta aikata waidan yarinyar taganta karta tona azaci mudin masu garkuwa da mutanene, cewa fa kurun a tsoratar da ita ta fasa auren ka ni meye laifi na sema dana  dawo ake gayamun" kallon ta yae cikeda takaici da baqin ciki mara misaltuwa yace

"Ba wannan ba yanzu ha d'amu da qawar taki ta nuna mana yaran da inda suka kaita nida kaina zan shiga neman ta da police" da dauri ta d'ago ta kalleshi

"Da police kuma kanada hankali kuwa sekaje a riqa cewa wai yayarka me en ta'adda wlhy kayi kadan tunkan ba qanwar uwarka bace ba seka qyaleta ai" kallonta yae har idanshi ya kad'a yae jajir se zare mata su yakeyi ita kanta ta tsorata da yanayinsa ya dauke qafarsa d'aya ya d'aura kan d'aya yace

"Anty Nasara ki sani wlhy baki kaimun cenba, na rantse da wanda rayuwata take hannun sa  akan Hafsat zan iya yanke jinin dake yawo nawa acikin naki, zan yanke alaqa dake ta har abada, zan rabu dake rabuwa me girma zan nisanceki nisan ci me tsanani wlhy summa tallahi zan tsaneki tsana mafi muni a rayuwa!!! har a wurin Allah banida laifi idan nayi hakan sabida   baki d'auki rayuwar d'an adam a bakin komai ba, zan kuma gayawa  Daddy zan sanar masa  cewar bakida imani yanzu kin sauya daga Fatima Bintar daya haifa kin zamo me kisan kai me gardawa,gwara miki tun wuri ki dawo hayyacinki zan rufa miki asiri na hana en sandan dogo bincike na binne sunanki kimun bayanin su dan naje nemanta da kaina" Mamakin kalaman sa ya sanya ta gaza furta koda kalma d'aya ta hango haqiqancewa a kalamansa iyakar gaskiyar sa kenan fa!!   Reedah ce ta tare

*look twin beje cenba abin sam ko kad'an beyi nisan daze cenba, ke kuma Anty dan Allah ki had'a mu dasu waike ko haqqi bakya tsoro" nisawa nasaran tae tace ba damuwa zan hadaku dasu yanzun nan amma dai kaikam ka bani mamaki ta yanda zaka fifita wata bare akaina har kana rantsewa akan datse zumuncin mu akanta lallai da mugun abinda ta maka" bece mata kanzil ba harta had'asa dasu.

Mom Nu'aiym

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now