page 10

3.8K 657 20
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

*Assalamu Alaikum, masoya kuma makaranta wannan littafin ina mai baku hakuri akan muhawarar danaketaji tana tashi duk inda na leqa akan wannan littafin, wasu lokutan idan zaka ilmantar ko wa'azantar kakan aniye wani selfish interest naka kayi komai dan Allah ka bari dan Allah, sabida haka kuyi hakuri dan Allah inshaa Allah i promise u guy's happy ending....Nagode*

                            10

Kujera ya samu ya zauna yace yana me mata nuni da hannu akan kujerar dake fuskantar tasa

"Ki zauna anan" miqewa tayi ta zauna tana meci gaba da sharar qwallah....gyaran muryarshi yae sanan yace

"Kinada kati a wayarki?" Kallonshi tae ta gyad'a masa kai alamar akwai yace

"Yauwa saisaita nustuwarki kar kuma kiji tsoro!! Dukkanin wani tsohon saurayi da kike dashi ko kuma wani mutumin banza dakika san kun tab'a yin mu'a mala dashi ki kirasa a waya ki gaya masa kalmomin nan dazan fad'a miki.....a yanzu kuma" da sauri ta d'ago ta kallesa ya kawar dakanshi daga dubanta yace

"Hand's free zaki saka kice da duk wanda kika kira bayan kun gaisa

" Na gaji da wannan sab'awa Allah danakeyi yanzu mijin aure nake nema dan Allah ko zaka taimaka ka aureni?" Kallonshi ta qarayi a karo na barkatai  kan tace

"Bazan iyaba wlhy Maheer"

"Idan bazaki iyaba ki tashi ki barmun gidana" Jikinta ne ya soma rawa, itada dai Nancy ta kasa gane inda ya dosa amma dai kanzil batace ba tun zuwansu 

"Kayi hakuri zan soma kiran" Wani Alhj Suraj ta kira wanda shine ya fara lalata mata duniyar ta kuma akan ze aureta yazo gidan su matashin me kudi daya gama da ita ya watsar,ya dauka suka gaisa a mutunce ta rattafomai yanda  Maheer yace tae, dariya ya bushe da ita  yace

"Haba isy...tayaya zan aureki? Bayan na sanar dake tun farko bazan iyaba, islam dazan aureki aida na aureki tun farko tunda nasan nine silar b'ata rayuwarki, wlhy a gaskia bazan iya auren matar datake yawon tazubar ba, sabida haka kiyi hakuri kije ki nemi miji daidai dake" wani baqin cikine ya tinkarota tace cikin takaici

"Amma suraj idan nime yawon tazubar ce ai kaine silar halakkkar da mutuncina ko, kakuma gujeni a lokacin dabanida wani gata se Allah yanzu yaya kakeso nayi da rayuwata?" Tsaki yaja

"Kinga islam nifa wlhy sena wulaqantaki idan kikace zaki zomun da raini, haka kurun shekaru uku bama tare se yanzu dan cikar iskanci kice na aureki? Wama yasani ko kinada qanjamau" zafi zuciyarta keyi bazata iya saurara ba ta katse kiran da saurinta ta dafe qirjinta,tausayi ta bashi yace

"Ki kira wani mana" Ba musu ta kira wank boy friend d'inta dake Arqillah Sameer yana d'aga kiran yace

"Me bani kyauta!! Ta samu ne inzo muje mu hole?" Runtse idanta tae ta bud'e su kantace 

"Sameer Dan Allah zaka iya aurena?" Wata dariya ya bushe da ita cike da shaqiyanci kan yace " ke kina tunanin aduniya akwai wanda ze aureki ne, ai daga zaran kikaji yarinya tafito yawon ta zubar tokuwa seta zubar d'in dan bame aurenta!! islam ko d'an iska baya son er iska se'a bariki" katse kiran tae ta kalli Maheer murya na rawa furta

"Kayi hakuri Maheer bazan iyaba" shima kallonta yae

"Sekin kirasu, su goma sha biyar tukunna zan barki, akwai abinda nakeso ki sani dan kiwa kanki hisabi da kanki islam" batare data qara cewa komai ba tai kiran wani!!!! Shima ya yab'a mata magana haka taita kiransu suna cin zarafinta har su goma sha biyar, zuwa wannan lokacin ta gama kaiwa qolin qoli wurin b'acin rai bata tab'a kasancewa cikin namada ba se'a wannan lokacin!! Ita dake taqama da kyau da isa acewarta seta gama cin duniyarta d tsinke sannan tae aure a lokacin da takeso sanda kuma tae ra'ayi!!! Yanzu tunkan aje ko ina taga ta kanta, kasa d'aga idanta tae ta kalli Maheer ita kuwa Nanuwabta qulu sosai da wannan tozarcin daya siyawa qawarta.....miqewa yae  tsaye ya kalleta

WATA FUSKAWhere stories live. Discover now