ABAR SO 2

1.2K 19 0
                                    

💝💝💝💝💝💝
                        ABAR SO
                                    💝💝💝💝💝💝

WRITTEN  BY :NAFISAT  MA'ARUF SHEHU
                                  💋💋(WURARH)💋💋

🌟 GORGEOUS WRITERS FORUM 🌟    
             
              🌟 G.W.F 🌟

Home of gorgeous, intelligentand expert writers, we the best among the rest

*happy married life mama j , Allah ya albarkaci rayuwa aurenki,Allah yasa mutuwace kawai Mai fidda ke AMEEN*

PAGE 10-15

Murmusawa yayi saiyace "haba NAFHI ai babu damuwa"
Tsantsan mamaki neh yakamata kenan harya rike sunanta. Saitace

"Kul kadaina cemin NAFHI  sunana NAFHIRA ,ABAR SO  neh take cemin NAFHI  saikace ni sa'ar ta  dukda da hour daya nagirmeta  Ina yawan hanata Amma taurin kai gareta shiyasa nima innaga yan mutuncinta suna nan nakan ce Mata BABYNMU,"

  kawai saita yi yar dariya tare da fadin

"Kuma fah da Momma,daddynmu  dakuma antynmu sukecemata  hakan Amma Momma  tafi kiranta da ABAR SO  Kuma tafi jin Dadi in aka kirata da hakan"

"ABAR SO " shine abinda yafada beneath his breath , azuciyarshi kuwa cewa yake

"lallai kincika ABAR SO, cos kallo daya namiki son ki yamin babbar kamu"

saiyanxu yakare musu kallo  ashe twins neh dukda akwai Dan banbanci but still Ana ganewa cos NAFHI  farace irin sosai dinna Amma  ABAR SO  tafi tah kyau nesa bah kusa bah

"kayi hakuri Naga nacika kah da surutu, shiyasa muke yawan samun matsala da ABAR SO  Kuma fah wlhy bawani surutu bace Dani  bah " 

tafada tana pouting da bakinta .
             Daman Shi baya son Wanda suka cika surutu  Amma Kuma har baison tagama cos yanason yakara Sanin  more about ABAR SO  Amma saiyace

"babu damuwa NAFHI  "

harta fidda ran zai amsa sai kawai tsinkayo muryan Shi Dadi sosai taji cos ita taxata shima zaice tanada surutu neh,xatayi magana kenan taga ABAR SO  ta kwanta tawajen da take ,alamu dai Sun nuna bacci neh ya kwashe tah,  murmushi tayi tareda daura hannunta daya akanta tana shafawa a hankali..........

30 Minutes later......

Lura da yanda takeyi neh yasata kiranta cikin nutsuwa

"ABAR SO "

maganan ta neh kuma yaja hankalin Al-amin Wanda daman jiran tashinta yake. .....
Ahankali take dagowa takalleta .... kawai sai ta rungumeta tareda fadin

" am so sorry my NAFHI  baxan sake miki magana cikin fushi bah kiyafemin danAllah yar'uwata,bankarawa wlhy , I love you "

tafada daidai lokacin da NAFHI  ta dagota

" haba ABAR SOnmu Kuma babynmu kidaina bani hakuri niyakamata nabaki hakuri cos koda yaushe ina taremiki zaman window seat , kuma Insha Allah bansakewa nima "tafadatareda goge Mata hawayenta,

"say you love me too "

shine abinda  ABAR SO  tace tana kallon kwayar idon NAFHI

" I love you too "

shine abinda NAFHI  taceda ita , murmushi suka sake atare, sai Kuma tajuya wajen Wanda tamawa rashin kunya Wanda alokacin shi kuma ya kuramasu ido Kaman zai cinyesu  cos yaran Sun burgeshi sosai ......

" kayi hakuri DanAllah .... am so so sorry for being so rude ,kindly find a place in your heart to forgive me " tafada tareda hada hannayenta waje daya alaman neman yafiya ....

"Babu damuwa wlhy " yafada yana Mata murmushinsa Mai kyau ,itama murmushin tamayar Mai  tareda  rolling din anime eyes nata wanda suka sha kohl , gani yayi Kaman baitaba ganin eyes dinda sukakai nata kyau bah....

Anan Kuma talura da dimples dinshi Wanda suka lotsa sosai  daman Kuma NAFHI  neh kawai Mai dimples itakuma batada kuma tana mugun son dimples

"May I touch your dimples pls?"ta tambaye shi hade da marairaice fuska ,gyada kanshi yayi alaman eh .... ai kuwa bata yi kasa a guiwa bah tasa yatsanta daya aciki  tareda yin dariyan jin Dadi . NAFHI  kuwa da ta tsaresu da idanu itama ta tayata dariyan .... " her touch was something else " yafada   azuciyarshi sbd atake awajen  yafara jin mood dinshi  na neman chanzawa , saukar da idanunshi zuwa kirjin tah yaga breast dinta ko tasowa basuyi bah ......

Itakuma tashagala da taba dimple dinshi " Dan Allah muyi hoto Amma fah zakasa dimples dinka su lotsa " tafada hade dah lalubo tablet nata Wanda zallan hotuna sukeyi dashi cos both of them are photo- holic and  also photogenic .......

Wani Dadi neh ya ziyarceshi jin zasuyi hoto da ABAR SOnshi.....niko nace taya tazamo tashi? .... hotuna sukayi su biyu kafinnan tajanyo NAFHI  sukayi su uku ,bayan sungama neh take kallon yanda sukayi kyau " wlhy kai kyakyawa neh" shine abinda ta furta ... "ai kema kinada kyau sosai "  shima yafada.."ai daman babynmu  kyakyawa ceh na bugawa  ajarida" sai kawai dukkansu sukasa dariya ... haka suka dinga hira har plane nasu yasauka, yana sauka kuwa cikin sauri suka isa wajensu Momma  da antynsu  awajen arrival departure. ....  harya Kama hanya yatina da abu ai dasauri yakoma ...... yana Hango su yasauka ajiyar zuciya, cikin takun kasaita yakarasa wajen su tareda gaishar da momma  amutunce ta amsa Mai Kuma cikin sakin fuska.

Sunajin muryan shi suka juyo cos daman Sun  basu bayaneh ... " haba kannena yanxu tafiya xakuyi bamuyi exchanging din contacts bah"..... lokacin kuwa Momma da antynsu Suna magana .... "lah ai bamuda numbers" atake kuwa murnan shi yakoma Amma saiya Kara cewan "Dan Allah kudan tsanmin hotunan damukayi" yafada cikin sigar tsokana , darawa sukayi cos yabasu dariya..... sharing din hotunan sukamasa, daganan Kuma suka rabu,  yatafi cikeda kewar ABAR SOnshi dakuma yar'uwar tah sukuwa basu Wani damubah .

*********************************
Ajiyar zuciya yasauke  hade dah daukar wayarshi a kan bedside drawer ,power button yadanna atake kuwa hotonda sukayi da ABAR SOnshi yabayyanaa screen din phone dinshi " I'm really missing you sunshine ,yaushe xamu hadu"? Yafada hade da goge kwallar idonshi alokacin dayake sauka daga kan gado , toilet yafada bayan ya ajiye wayar hannunshi

WAYE AL-AMIN

AL-AMIN ABUBAKAR SULAIMAN   da neh awajen Alhaji ABUBAKAR SULAIMAN Wanda yakasance sha'araren Dan kasuwa cos duk fadin Nigeria an San dashi , mutumne Mai mutunci,tausayi Kuma bashida kyamar talaka kowa nashi neh shiyasa yakara kima a idon jama'a.

Al-amin Wanda abokanshi kekiran shi da amin  ,kyakyawa neh na karshe ,haddadden gaye Mai ji dakanshi, kudi,kyau uwa uba ilimi both arabic da boko  Dan kwalisa yayi karatunshi a Cambridge university inda yakarance medicine  harPHD yanada  Kuma shi visiting consultant neh , Ana gayatar shi garuruwa da dama ......shekaru hudu kenan yake neman ABAR SOn shi Wanda suka hadu acikin plane , bayan mummynshi baijin zai sake son wata sai gashi  yayi  Gamdatakar  da Wanda tasace zuciyarshi acikin seconds da Abu wuce goma bah . Auren hadi akayi Musu da ummulkursum  inda tadage wai inbah shi suka auramata bah xata  shiga duniya  ai kuwa mumy tarude  kuma ta tilasta wa amin sai ya aureta.  Sam kursum bata cikin kalan matan da  yake so Amma haka ya daure yabi umarnin mummynshi , yanda mumy ta fahimce Dan nata baison  auren yasa ta Mai alkawarin duk randa ya samu choice nashi zata amince yakara auren.....

Wannan kenan

Babynmu  shine abinda wannan matar ta kira daidai Kuma lokacin Wani karamin yaro Wanda baxai wuce shekaru hudu bah yafito daga wani daki  Sanye da uniform, da alama dai islamiya zashi " salimunah Ina yayarka ?" Matar ta tambaye  yaron "babynmu  tana zuwa Antynmu , wai daman cewa nayi tasa kohl a idonta shiyasa takoma " yafada tareda goge takalmin da yagani akasa Wanda nasan baxai wuce na babynsu bah  ,kawai saigata tafito Sanye da katuwar farar khimar  har kasa , ajiye takalmin yayi akasa daidai  wajen kafar yayar tashi  kallonshi. .....

💋💋 WURARH  💋💋

ABAR SOWhere stories live. Discover now