ABAR SO 33

1.7K 96 1
                                    

💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝

*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*

WATTPAD: MHIZZPHYDO
🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

*Book 🅱️Page 3*

Afirgice tadago kanta dalilin jin muryan shi, waske wa tayi ta ciro albasa guda daya daga inda ta boye sannan tattaro jarumtar ta tace

"Aww daman zanci neh"

Gyada kanshi yayi yace"ko zan iya sanin amfanin shi??

Rolling din idonta tayi tace" yana reducing stomach upset(ciwon ciki. Ko bahaka bah??) Yana da kyau da masu Asthma,zazzabi ,tari ,rashin son cin abinci (Wato loss of appetite), hawan ji..."

Katseta yayi da fadin"Ya Isa hakan nan malama"

Murmushin gefen baki tayi tareda wuceshi,bayan ta yabi da kallo sai kawai ya girgiza kanshi cos yarasa miyesa kwatakwata zuciyar shi bata gama yarda da yarinyar bah

Har takai bakin kofan shiga cikin hospital din sai taja ta tsaya waigawa tayi caraf idonta ya harba da dustbin

Karasawa wajen dustbin din tayi sannan ta bare Albasan ta, boyewa tasake yi kafin ta bar wajen

Isowan ta yayi daidai da fitowa su Amin, wajen su doctors din suka karasa cikin sauri harda su tuntube

Handkerchief Amin yazaro yagoge zufan goshin shi sannan yace"mudan je cikin office"

Ganin Bai basu daman magana bane yasa suka mara mai baya

Gyaran murya Amin yayi yace"sakamakon hatsarin dayayi mijinki ya samu mumunar matsala a kafan daman shi kuma munyi iya kokarin mu ganin komai ya daidai ta amma unfortunately Allah bai bamu sa'a shiyasa muka guntule mai kafan...

Agigice mumy tace"What??"

"Take it easy hajiya"ya fada in calming tune

Zaro Ido Nadhira Tayi cikin tashin hankali tace"Kana nufin kun yanke kafan shi kenan"

Cikin tausaya musu yace"erh but everything will be fine"

Kuka sosai sukeyi Nadhira kuwa harda shidewa daga baya kuma sai tayi shiru

Kamata Mumy tayi nan taji jikinta yayi zafi irin sosai dinnan hankalin mumy sake tashi yayi ganin da kyar Nadhira ke tafiya tallafa mata suka yi suka fita daga cikin office din kuwa ward din da aka chanza mai...

Hannunshi tarike gam hawaye na tsiyaya daga kwarmin idonta harda su tofa mai Addua su  mumy ma kuka sukeyi suna mai Addua...

'''30mins later'''

Antynsu neh suka shigo da sallama itada Salim da basket a hannu.

Amsawa sukeyi inda antynsu ta karaso tareda musu ya mai jiki kasancewan shi kadaine acikin
dakin wato single exclusive room

Wajen Nadhira ta karasa tareda kamo hannunta Jin jikin ta rau yasa antynsu kallon ta cikin mamaki

Cikin tausayawa tace"Miyeke damunki Babynmu ko daman baki da lafiya neh?"

Kallon su suka miyar wajen Nadhira din sai a sannan suka lura da yanda idonta yayi jawur

"Subhanallah jiyanda idonki yayi jah" mumy tafada

Shigowan Amin neh ya katse su ,ko amsa gaisuwan da Amin yake mata antynsu batayi bah tace"Dan dubamin Babynmu ko lafiyanta lau naji jikin yayi zafi sosai"

Cikin sassarfa yakarasa wajen ta tareda da hannunshi a wuyarta domin Jin temperature dinta.

Dasauri yadauke hannunshi yana kallonta kara kai hannunshi yayi ya rike nata yana feeling pulse dinta

Wayan shi ya dauka yakira nurse akan tazo cikin minti daya ta iso

"Tayani kama ta" yafada yana tallafo Nadhira

Fita daita sukayi inda take tafiya da kyar cos badan an tallafa mata toh lah shakka faduwa zatayi

Consultant room aka shiga inda ta kwantar daita akan gado

"You can go" yafada cikin tsare gida ganin yanda nurse din ke binshi da ido.

Tsaki yaja bayan nurse tafita tareda karasawa inda Nadhira take baikai ga fara dubata bah yaji an kwankwasa kofa

Gyara tsayuwar shi yayi sannan ya bada izinin shigowa

Inspector Nasir neh dakuma Antynsu neh suka shiga

Musabaha sukayi inda yafara duba Nadhiran

"Baby!!" Yakira sunanta tareda kafeta da ido

Yamutsa fuska tayi batareda ta kalle shi bah

"Miye ke damunta Amin" Antynsu ta tambaya cikin son danne gutun murmushi dayake son kufce mata

Pupping face dinshi yayi kaman zaiyi kuka yace" jininta neh yakeson hawa fah gakuma zazzabi"

"Subhanallah" Antynsu da Inspector daya kafe Antynsu da ido suka furta atare

"Allah sarki kowani irin so take mawa wannan bawan Allah oho" inspector yafada azuciyarshi yana mai jin tausayin Nadhira sosai

Karasawa wajen gadon Antynsu tayi tareda kai hannunta jikin Nadhira tace" Babynmu bude idonki ki kalle ni cos ni banyarda dake bah"

Cikin sauri ta bude idon jin abinda Antynsu ke fada agaban inspector Nasir da sauran kiris tasa ya mance da babin ta

Ahankali tace" miye kike nufi??"

Kefta mata ido Antynsu tayi cos haka kawai taji bata yarda da Nadhira bah itama cikin sigar da Nadhira tayi magana tace" kin fini sanin abinda nake nufi"

Rolling idonta tayi cikin muryan tausayi tace" Yanzu an yankewa big dady kafa daya kenan??"

"Oya we should all go out she need to rest"Amin yafada da sauri cos bayason tana daga hankalin ta.

Batareda sun sake magana bah suka fice gabaki daya tareda rufo kofa

Lumshe idanunta tayi tareda sakin murmushi kafin ta zura hannunta cikin khimar dinta

Zaro albasa daya tayi daga hammatan ta tace" kwalliya ta biya kudin sabulu"

Sake miyarwa tayi tana jin hucin zafin jikinta na karuwa cos dan cire albasa daya datayi yasa taji dan dama dama dazu

Jitayi zafin ya isheta hakan nan yasa ta mike tsaye tareda nufan dustbin

Albasa dadaya taciro daga kowani hammatan ta ta yasar dasu acikin dustbin sannan takoma kan gado

Ko minti biyu...

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*

ABAR SOWhere stories live. Discover now