💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*
WATTPAD: MHIZZPHYDO
*Book 🅱️Page 21-END*
Kallon juna aka hau yi a cikin palourn cikin mamaki abin da Malam ya fad'a
Ita ma Nadhiran zaro idanuwa tayi tana girgiza kai alaman bata gane miye yake nufi ba
"Ki tuna da kyau akwai wani abun da kika yi wanda sam-sam bai dace ba!"Malam ya fad'a ganin she's confused
A hankali ta ce"Ni babu abinda nayi sai ko acikin rashin sani ne!"
"Da sanin ki kika aikata abinda yayi sanadiyar ciwon wannan yarinyan!"
Cikin kidima take kallon sa barin ma yanda taga Amin ya kure ta da ido yana kallon ta
Cikin rawar murya take cewa"taya za'ayi nayi abinda zai yi sanadiyar jefa diyata a wannan halin?"
"Zaki bada amsa ne kokuma zaki tsaya tambaya!"Amin ya fad'a cikin takaici da b'acin rai
Malamin ne yayi gyaran murya yace"zaki iya tuna lokacin da kike nakud'an wa'inan yaran dakuma ranan da aka sallame ku?"
Wani yawu mai d'aci ta had'iye tana kokarin saisaita kan ta, ga wasu zafafan gumi dake karyo mata
"Hmm , mari na tayi!"ta fad'a cikin rawar murya tana kokarin miyar da hawayen ta
Runtse idanuwa Amin yayi saboda ya gane sauran abin da ya faru
"Da ta mareki sai akayi Yaya?"Malam ya sake tambayan ta
"Ramawa nay..."
Bata karasa ba taji an rufe ta da wani shegen duka,
Dakyar aka samu aka kwace ta a hannun Amin da ran ranshi ya kai kololuwa wajen b'aci
"Haba dai ! Ai bakamata ace ka dake ta ba!"
Hawayen takaicin da zubo Masa ya share cikin d'auriy yace
"Da kun bari na koya mata hankali, fisabilillah ace babu abinda ta sani sai ramuwa haba!"
"Ya isa Aminullah, abinda yakamata yanzu shine muji abinda Malam zai fad'a saboda wa'inan abubuwan da kake yi will not solve anything"Alhaji ya fad'a a hankali
Nadhira dake rakub'e a jikin Kursum ne ta kara sautin kukan ta saboda dukan ba karamin shigan ta yayi ba! Har wani ciwon ciki ta fara ji saboda ya same ta a cikin
"Shin kinsan wacce kika mara kuwa?kinsan wace ita?"Malam ya tambaye ta
Girgiza kai Nadhira tayi cikin tsananin tsoro da tashin hankali
"Toh wannan matan nada Iskokai wanda basu da sauki ko kadan,in ta matan ne babu matsala saboda mai yafiya ce, dakyar a mata abu ta rama, amma lokacin da kika je mata, akwai iska a jikin ta lokacin , ke kuma cikin rashin sa'a kika maresu ke azaton ki ita kika mara!"
"Wayyo Allah na!"ta fad'a cikin kuka sosai,
"Alhmdllh dai nasan a yau komai zaizo karshe da yardar Allah" Malamin ya fad'a yana bud'e jakan sa
Nuna kan sallayan da shimfid'a yayi tare da cewa"A mik'o min yarinyan nan"
Cikin rashin kwarin jiki Hajiya ta mik'a ta wajen da Malam ya nuna
YOU ARE READING
ABAR SO
Random"ABAR SO!!!" Shine abinda NAFHIRA tace cikin siezing din breath, aikuwa arikice tajawo NAFHI kan cinyarta "Addua fah kawai zaki mana bah kuka bah, ganinan acikin abinda nafi tsana arayuwa ta (blood)wannan kawai yakara tabbatar min da babu wanda ya w...