💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*
WATTPAD: MHIZZPHYDO
*Book 🅱️Page 15*
Isan su police station yayi daidai da karasowar su Antynsu, ko iskan da ta kwaso su ba ta shaka ba ta wuce su duk da Kiran ta da suka dinga yi...
Babu yanda basu yi da ita akan tayi magana ba amma ta k'i asalima ko kallon su bata yi ba har yen sandan suka koma da ita cikin cell....
Sosai ranta yake konewa in ta tina harda Antynsu acikin masu mata karya dama kuma ta riga ta san shi Amin makaryaci ne amma antynsu fah?
Ihu tasaka kafin ta fashe da kuka mai cin rai saboda yanda take ji, tinda take a rayuwan ta bata tab'a tunanin zata shiga police station ba balle a zo ga cikin cell!
Washe gari.....
Kotu ya cika mak'il da jama'a saboda hukuncin da ake son yankewa, yen uwan Maimuna har da su big daddy da familynsa, Kaii in takaita muku mutane da dama sun hallara
Gefe guda antynsu ne idanuwan ta duk ya kumbura tsantsan kuka ga Amin ma ya dawo wani kalan tausayi dashi a wajen,
Malama Kursum kuwa ido ya raina fata da jin abinda aka ce Nadhira ta aikata amma wani b'ari na zuciyan ta farinciki ne fal a cikin jin za'a yanka mata hukunci ga kuma tunanin cewan Hajiya zata sa Amin ya sake ta saboda ita a yanda take ganin take-taken sa tasan da wuya ya sake ta kuma tasan ko Karen hauka ne ya cije ta ba zata iya mata ko kallon banza ba balle kuma a zo ga tasa ta aiki!
"Hmm wane ni kalan ta Kashe ni! " shine abinda ta fad'a a sarari, juyowa Maman Ramadan da suke jiran jin laifin da Nadhira aikata tayi
"Ta tab'a kisa ne?"
Sanda ta ya mutsa fuska kafin ta ce"yo miye maraban dambe da fad'a tinda daman kisan taso yi Allah bai bata sa'a ba! "
Cike da mamaki Maman Ramadan ta kalli kofan da ake shigowa da ita,
Ganin ta da suka yi yasa antynsu fashewa da kuka cike da tausayin yarinyar ta, ko inda suke bata kalla ba aka wuce da ita cikin bar din da suke tsayawa
Shigowar alkali ne yasa kowannen su yin shuru, batare da b'ata lokaci ba Alkali ya nemi jin ba'asin zance
Nan aka fad'i komai, d'agowa Alkali yayi cike da mamaki inda kowannen a cikin court din suka fara kus kus nan Alkali ya buga guduman su
Gyaran murya yayi ya ce"Nadhira Shariff kin dai ji abubuwan da ake tuhuman ki da su! Shin kina da abin da zaki iya cewa don Kare kan ki ko kum...
"Na amince da duk abubuwan da ake tuhuma ta da shi! "Ta katse Alkalin, mamaki ne ya karo akan fuskokin mutane inda antyn su ta fashe da wani siririn kuka
"Oh Allah! "Shine abinda wannan gayen wato Ramadan wanda suka had'u da shi a filin girgi ya fad'a cike da dimbin mamakin ta saboda daman shine mai kare ta amma tinda ta riga ta amsa laifin ta babu abinda ya rage da za'a k'are!
Girgiza kai Alkali yayi yana jinjina bushashiyar zuciya irin na Nadhira! Sake gyaran muryan sa ya yi ya ce"this is my judgment! "
Ai nan ka ji Kotu ya dau shuru kaman graveyard, kowa ka gani ya zura wa Alkali ido ana jiran a ji wani hukuncin zai yanke
"Kotu ta yanke miki zaman gidan yari na tsawon shekara guda saboda kwayoyin da kike amfani da shi da Kuma miliyan biyar wa iyayen yarinyar da kika haukatar!"
Lumshe idanuwan ta tayi Chan Kuma ta bud'e tare da sakin Murmushi wanda hakan yayi daidai da bud'e inda take tsaye,fitowa tayi still da wannan murmushin a fuskar ta,Suna had'a idanuwa da mutanen gidan su ta tsuke fuskar ta Kaman bata tab'a dariya bah.
Suna isowa wajen su ta ja burki ta tsaya "kun ban mamaki,Amma ba damuwa gwanda da kuka dawo dani din!
Dan takawa tayi har gaban Kursum da Murmushin ta ya d'auke dalilin ganin ta tako zuwa gaban ta,nan da nan Wani irin tsoro ya shige ta!
Murmushin ta mai d'auke da ma'ana daban daban ta sake tana kallon Kursum da tsoro ya bayyana a fuskar ta
"Kin tina miye kika tambaye ni ranan da kika mare ni?...murmushi ta sake sake wa ganin Kursum ta girgiza kai alaman a'a..."ko zaki Rama ne? Don na ga alamun Marin ya shiga" toh bari na baki amsa ta!
Kaman daga sama suka ga Nadhira ta kifa wa Kursum wata gigitacciyar maruka a kowani side na kumatun ta,Zaro idanuwa suka yi inda polisawan suka riketa, ko barin wajen basu yi ba suka ga Kursum ta sume a wajen sumammiya
Man da nan aka rufa a kanta , polisawa Kuma suka yi waje da Nadhiran da ke ta zuba murmushi....
Hannun ta da suka yi Sab'a ta kalla tare da ya mutsa fuska lokacin da ta Tina fatar maciji ta shafa a hannun ta na musamman saboda Marin Kursum....
_Hey 👋 fans! Show me some love by following me on my Instagram *Mhizzphydo*_ I will really appreciate it if you do!.
_Vote, Comment & Share_
YOU ARE READING
ABAR SO
Random"ABAR SO!!!" Shine abinda NAFHIRA tace cikin siezing din breath, aikuwa arikice tajawo NAFHI kan cinyarta "Addua fah kawai zaki mana bah kuka bah, ganinan acikin abinda nafi tsana arayuwa ta (blood)wannan kawai yakara tabbatar min da babu wanda ya w...