35

1.6K 127 7
                                    

💝💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝

*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*

WATTPAD: MHIZZPHYDO
🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

*Book 🅱️Page 6*

"karfe 11 zaku zoh"

Tana gama magana ta katse kiran batareda ta Jira yayi magana bah,sanda tagama tattara abubuwan ta sannan tasauke ajiyar zuciya tana mai kwanciya akan gadon...

_9:05pm_

Zaune suke dukkansu a parlourn suna kallo kaman yanda suka sabayi kowani dare.

"Babynmu yasu antynku?" Mumy ta tambaya tana kallon Nadhira dake zaune kusa da big dady tana mai tausa

Murmushi tayi tace" duk suna lafiya tama ce na gaisheki mantawa nayi"

"Ayyerh to ina amsawa"

"Kuma tace nagaisheku" tafada tana kallon su Faty"

Batareda sun kalleta bah suka amsa, bata damu bah soboda bayau suka saba bah, tabe baki tayi azuciyarta tace" zaku gane kurenku neh ai"

Shafa kanta da big dady yayi neh yasata dawowa ahankali tace" kaima tace in gaisheka kuma namaka ya jiki gobe zasu zoh dubiya"

"Zasu zoh kuma?" Mumy ta tambaya soboda bata gane kalman zasuxo din bah

Murmushi tasake sakarwa tace" erh mana itada Salim"

"Aww sai yanzu nagane"

Murmushi tasake yi azuciyarta tace" badai da Salim bah saidai da Baban Salim dakanshi"

Haka dai suka tab'a hira sama-sama sannan kowa yawuce dakinshi...

_11:00pm_

Shine abinda agogo dakinta yabuga, lumshe idanuwanta tayi sannan tayaye bargon data rufe kusan duka jikinta dashi.

Zata sauka daga kan gado kenan tayi bang bang bang ana buga kofa,

Tsaki taja tana fadin" wa'inan basu iya aikinsu bah wlhy"

Mikewa tayi tanufi wajen Window , cire glass din tayi sannan tadira abinta tareda miyar da glass din kaman yanda yake,

Harta wucesu tabayan flowers basu sani bah, wajen gate tanufa taga baba maigadi ayashe akasa da alaman sun Shaka mai hoda neh

"Ti..ti..ti..ti..ti"tayi da bakinta sannan ta tsuguna agabanshi tace" yi hakuri"

Sannan tamike tafara nufan inda ake buga kofa

Karar takalmin ta na
contrast-lace ankle boots neh yamiyar da hankalin wasu gardawa biyar kanta,

Kallonta sukeyi daga sama har kasa yanda tayi shigan wandon da riga Leda  wato patent leather dress fuskarta kuwa mask neh shima baki,

"Waye neh" mumy ta tambaya cikin rawar murya jin bugun kofan bana masu hankali bane, basu gama karemata kallo bah sukaji anyi magana

"In baki bude kofan nan bah zamu cinnawa gidan nan wuta" wani mai katon murya yafada

Atsorace Mumy ta zaro Ido jikinta na wani irin b'ari, hannunta na rawa ta bude kofan, bata gama budewa bah aka bangaje ta.

Ganin barayine yasa Mumy tasake wani kuka,

"Shihh" wani acikin su yafada yana kama bakinshi tareda nuna mata bakin bindiga, ai tsit kakeji kaman ruwa yacinye ta,

Muryan Nadhira da ta samawa kanta mazauni akan kujera sukaji tace" banason bata lokaci , kuje ku sauko min dasu"

ABAR SOWhere stories live. Discover now