💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*
WATTPAD: MHIZZPHYDO
*Book 🅱️Page 10*
Cikin azama Nurse ta taro ta gudun karta karasa kasa ta shiga uku, dariyan da Nadhira ta fashe da shi neh ya dawo da hankalin mutane kan ta
"Babynmu! "Antynsu ta kwala ma ta Kira daga baya saboda daman basu san lokacin da ta fito bah
Juyawa ta yi wajen Antynsu tana nuna ma ta Maimuna da rabin jikin ta ke kwance ajikin nurse kafin ta ce" kin ga ta kwanta a kasa koh? Nima na kwanta? "
Da sauri Antynsu ta girgiza kai tare da riko ta ganin Nadhira na shirin kwantawa a kasa,
Cikin kwantar da murya"Muje koh za'a sallame mu neh sai mu koma gidanmu koh ba haka bah? "
Ba ki ta washe tana Gyada kan ta Wanda yayi daidai da isowar wasu nurses da stretcher, daukan Maimuna dake sume suka yi a kai kafin suka wuce da ita in da aka bisu da kallo...
"Wayyo Allah ta cuceni! Ta tarwatsa rayuwanmu gabadaya!! Allah ya.. "Mummy ba ta karasa magana bah suka ji sallama a bakin kofa
Share hawayen fuskarta tayi da khimar din ta tana mai kallon fuskarta Faty da ke rizgar kuka, ita ma Maryam kukan ta ke yi amma na tausayin yar uwarta ya fi yawa
Cikin sanyin jiki su Antynsu suka karasa shigowa, Nadhira ceh ta je ta zauna a kan gadon da big daddy yake duk da hanatan da akayi amma ta k'i, kallon sa ta ke kaman mai son yin magana chan ta sauka daga saman gadon ta koma wajen Dadynsu da ke zaune akan wheel chair din sa
Ya mai jiki suka musu sannan suka musu sallama a kan an sallamesu, shidai inspector yana zaune yayi shuru amma har lokacin nazarin Nadhira ya keyi kuma gani ya keyi kaman lafiyan ta kalau...
"Oga ai duk in da ku ke tunani toh yarinyan nan ta wuce tunaninku , ni abinda ya fi cin mun rai shine wasa da hankali na da tayi!"ya karasa magana cikin takaici da b'acin rai har da buga table sai kace ba'a gaban dan Sanda ya ke bah
Zufan kan goshin sa ya share cikin damuwa da gajiyawa ga kuma Commissioner of police ya sa baki a cikin maganan kuma ya ce dole sai sun nemo wacce ta aikata wannan danyen aikin!
Numfasawa yayi ya ce "Yanzu kana nufin babu abinda za mu iya yi don musan waye wannan yarinyan!? "
"Gaskiya babu amma ni fa naso gane wani abu dangane da wannan al'amarin! "Kala ya fad'a with full confidence
Gyara zama inspector ya yi ya ce "Fad'a muji! "
K'awar da kai Kala yayi yace"gomnati ta hana aikin banza dan haka ka bani karan sigari na zuk'a na san kwakwalwa ta ma zata fi daukan charji!
Murmushi inspector yayi saboda daman an bashi labarin Kala da kyau kuma yanda ya ke haka aka bashi labarinsa
"Jirani ina zuwa! "Ya fad'a tare da ficewa daga d'akin horon da suke, da kallo Kala ya bisa had'e da sakin murmushi da shi kadai yasan ma'anar sa...
"Ga jakan Babynmu na d'auko daga chan din"Amin ya fad'a lokacin da ya ajiye jakka
"Miye kaje yi a crime scene? Hajiya ta tambaya a tsorace
"Kai Hajiya! kawai fah mun wuce ta anguwan neh shine na ce why not na taho mata da abubuwanta tin da ina da tabbacin babu abinda zai sake kai ta wannan gidan! "Ya fad'a yana sakin murmushi
Girgiza kai Hajiya "Allah ya shiryeka!"
Hanyan waje ya nufa yana cewa"Ameen Hajiyarmu! Bari na kai mata shi part dinsu"
A pallour ya sameta ta zabga uban tagumi kaman mai tunani, a hankali ya karasa in da take tare da cire tagumin da tayi nan kuwa ta fasa ihun tsoro, cikin sauri ya rufe mata bakin ta saboda baya son taja hankalin mutane!
Cikin dariya ya ce"Ke ni neh mijin ki!"
Turo baki tayi har hawaye sun fara taruwa a cikin idanuwan ta tace"kaiii mijina shi ne ka bani tsoro? "
"Am sorry dear!"ya fad'a yana jan kumatun ta, murmushi tayi mai itama ta ja nashi kumatun kaman yanda ya mata
Dariya suka sak'e lokaci daya, zama yayi a gefenta yace"za ki sha ice cream?"
Gyada kai tayi murmushi kan fuskarta na d'adduwa,
Mikar da ita yayi yace "Oya gashi kai ciki sai ki d'auko khimar din ki mu tafi Havila ko ba haka bah? "
Murmushi tayi ta nufi cikin gida da abinda ya bata ba tare da ta duba miye bah!
Akan gado ta cillar tana had'a rai kaman an mata laifi, chan ta zauna akan gadon tare da fashewa da kuka mai cin rai.
Chanza channel ya yi daga cartoon zuwa ball, yana gyara zama ya ji kukanta cikin sauri ya shiga d'akin har yana bugewa
"Miye faru? "Ya tambaya yana rungumanta a jikinsa
Cikin shesheka ta ce"Ba Antynmu bane tindazu bata dawo bah kuma ta barni ni kadai a gida! "
Daukanta ya yi ya ajiye ta a kan cinyarsa tukun yace"ina ce ke ne Kika ce bazaki bisu bah? "
Lafewa tayi a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya kaman wacce ta yi tsere, duba fuskarta ya yi ya ga tayi bacci! Mamaki neh ya kamasa amma sai ya kawar tare da shimfid'a ta a kan gado sannan yayi tafiyarsa.
Bud'e idanuwa tayi sannan ta zauna a binta akan gadon tana karewa d'akin kallo kaman yau ta fara shigan sa...
"A ina kika samu wannan Baby? "Antynsu ta tambaya cikin mamaki
Kwantawa tayi abin ta tana mai turo baki, ganin yanda ta yi neh ya sa Antynsu matsawa wajenta tace"haba Babynmu yanzu baki son na kaiki Havila shan ice cream 🍦 kenan?"
Dasauri ta mike tana fad'in "zan sha kinji! Ki kai ni!"
"Oya fad'a min in da kika samu wannan abin? "Ta tambaya cikin lallashi ga wani irin fari cikin da take jin ta a ciki
"Mijina neh ya kawo wancan jakan jiya shine fah na bud'e na gani! Ki bani ma akwai wata mai kosai naga a irin wannan ta ke sama mana in muje siya kinga kuwa basai ta sa mana a nata takkadan bah tin da nima ina da nawa takkadan koh? "Ta fad'a tana mai fauce papern hannun Antynsu
Zaro idanuwa Antynsu ta yi cikin damuwa ta ce "no wannan baza'a ba ta bah! Ki kawo kinji? "
Mak'e kafada tayi tana turo baki had'e da mikewa tana cewa"ni bazan ba ki bah! Ai nawa neh kuma wa mai kosai zan bayar ta bani kosai mai yawa tinda haka naga ta yi wa wani yaro! "
Cikin tashin hankali ta ce "Ki rufa mana asiri kikawo danAllah "
Tafiya ta fara ta ce"Oho bazan bayar bah! "
Biyo ta antynsu tayi tana "Baby kizo mana! "
Wajen dadynsu da kuma Alhaji ta nufa da gudu tana cewa"ni dai wlhy wa mai kosai zan ba wa! "
"Miye faru neh Babynmu "Alhaji ya fad'a cikin kulawa
Kafin tayi magana Antynsu tace"cewa tayi wannan papers din zata bawa mai kosai! "
Dadynsu neh ya ce "Toh ai ba wani abu bane tinda zallan papers neh! "
Murmushi shimfid'e a samar fuskarta tace"ba zallan papers bane! wlhy signed will din Dadynmu neh a hannunta! "
*Wattpadians DanAllah ina bukatan Followers dakuma votes pls*
*Vote,comment&share*
*Mhizzphydo*
YOU ARE READING
ABAR SO
Random"ABAR SO!!!" Shine abinda NAFHIRA tace cikin siezing din breath, aikuwa arikice tajawo NAFHI kan cinyarta "Addua fah kawai zaki mana bah kuka bah, ganinan acikin abinda nafi tsana arayuwa ta (blood)wannan kawai yakara tabbatar min da babu wanda ya w...