ABAR SO 22

1.3K 69 0
                                    

💝💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝

*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*

WATTPAD: MHIZZPHYDO
🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟

               🌟G.W.F🌟

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

*Page  89-90*

"Big Dady neh yace yakamata kizo" wani irin dadi taji tindaga tsakiyar kanta amma Sai ta daura fuska  tareda fadin maganar dayasa kowa yin tsit awajen

"Nima kashe ni yakeson yayi kenan??" Wani munafikin hawaye tashare harda Jan hanci sannan tacigaba

" Ba damuwa zanje yanda yabukata amma inhar ban dawo da raina bah ina rokon kowanne daga cikin ku ya yafe min!!!" Tana gama fadin hakan  Sai tayi cikin gida da gudu

"Kutimelesi gaskiya baby drama queen ce taab"shine Hasana ke fadi acikin ranta

"InshaAllah babu abinda zai mata, Hasana ki bita cikin gidan koh" Dadynsu yafada wa Hasanan,dama kuma abinda take jira kenan amma Sai tace

"Daman fah Zan muku sallama ne cos naga dare nayi kuma ana rasa abin hawa anan"tafada hade da kallon Abdul ta gefen ido Sai akayi sa'a Shima din kallon nata yakeyi

"Ga Abdul Sai ya kaiki in kinshirya tafiya"mumy tafada cikeda jin kunya take fadin toh kafin tabar wajen,daganan babu kuma wanda yasake magana  cos kowa da abinda yake sakawa aranshi

"Amma Allah yayi munafika anan"Hasana tafada lokacin da taci karo da Nadhira tana rawa

"Am extremely happy besty, daman yanda za'ayi nafita nake nema gashi da kanshi ya gayyato mutuwar shi"

"Bangane mutuwar shi bah" Hasana tafada afirgice

"Ke kinsan miye ake Kira da kisa kuwa,kinsan hunkuncin wanda yayi kisa amusulunci kuwa toh let me tell you in baki sani bah duk wanda yakashe wani tabbas Shima kashe shi Za'ayi, koh kina son akashe ki kema??"

"Toh shima ai naga har rayuka biyu yakashe arana daya ba'a mishi komai, koh hakan na nufin yaci bulus kenan??"

"Sakkayyar Allah fah wani Babban abu ne in bai gani aduniya ba ai in ya hantaya lahira zai gani,amma pls karki ce zaki kashe narokeki cos bazamu so jini yahau kanki bah please" Hasana tafada cikin sanyin murya

"It's okay bazan kashe shi bah amma gaskiya bazan kyaleshi bah,zan bashi live to remember"

"Ohk ,nizan tafi"

"Jirani nakwashe kayana saimu tafi tare"haka ta tsaya har tagama kwashe kayyayakin ta  sannan suka fita.

Ganin dasukayi  Nadhira tafito da kayyayaki yasasu sauke ajiyar zuciya cos har Big Dady yasake Kira akan lallai taje ranan.

"Zantafi "Nadhira tafada

"Allah yataimaka and behave your own self there" Dady yafada

"InshaAllah" sannan tarungume Antynsu harda Sumba tabawa Antyn a cheeks dinta

"I will miss you Antynmu" tafada tana mai share guntun hawayen ta all the same time tana share hawayen antynsu,sanda kowa agurin yaji tausayin su dakuma jinjina irin soyayyar dake tsakanin su biyu cos in ba'a fada bah you will think she's her sister  nan kuwa amatsayin uwa Antyn take awajen Nadhira

"Allah yabiya ki da gidan Aljanna amaryata" Dady yafada acikin aranshi cos yasan dawata daban ne amaryan nashi to ba makawa yarshi tashiga gari amma ji yanda take nuna tsantsan so ga gudan jini Nargis dinshi daya rage

ABAR SOWhere stories live. Discover now