💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*
WATTPAD: MHIZZPHYDO
*Book 🅱️Page 19*
Ganin suna shirin kai wa kasa ne ya sa ta ture sa kadan tana mai kawar da kan ta gefe
"C'mon!"ya fad'a cikin shakeken murya
Matsawa baya tayi tana cewa"zan tafi kar Antynmu taga na dad'e!"
Ko magana bata bari yayi ba ta fice da sauri,zubewa yayi akan kujera tare da cusa hannun sa a cikin gashin kan sa....
Ranar Asabar...
A ranan ne ake shirin kai Nadhira gidan mijin ta, ko ina ka gani cike yake dam da jama'a
Hasanan Nadhira ce ta fito daga cikin d'aki sanye da wani dan uban su less mai shegen kyau da d'aukan ido
"Antynmu yarinyan nan fa tak'i shan komai sai wasa take mun da hankali"Hasana ta fad'a wa Antynsu
Wata yar uwan Antynsu mai suna Zuwaira ce tace"barni da ita abin ki!"
Murmushi tayi tare da cewa" gwanda kam bari na je na kai akwatunan ta saboda mijin ta ya ce za'a wuce mata da wasu zuwa Abuja anjima kadan"
"Toh adawo lafiya!"Antynsu ta fad'a inda A.Zuwaira ta wuce d'akin da Nadhiran ta ke....
8:00pm...
Kuka take yi sosai kaman zata shid'e ,yayin da fad'a da ake mata yake dad'a shiga cikin kunnen ta yana mai circulating a cikin kwakwalwar ta...
"Antynmu ki yafe mun!"ta fad'a cikin wani sabon kuka
Itama Antynsu fashewa tayi da kuka tare da rungumo Nadhira jikin ta sosai
Magana Antynsu take son yi amma gabadaya babu abinda ya ke da niyyan fitowa daga bakin ta
"Haba Amatullah wannan wani irin abu ne, kin wani zauna kina taya ta kuka! Ke kuma in baki mik'e sun tafi dake ba wallahi sai nayi maganin ki yanzu"Anty Zuwaira ta fad'a cikin fad'a saboda har ga Allah abun nasu tin yana burge ta har ya fara bata haushi
Dakyar aka banb'are Nadhira daga jikin Antynsu aka fitar da ita
Da driver da dadynsu sai kuma Hasana tare da Anty Zuwaira aka wuce da ita acewar dadynsu shi baya son hayaniya
Sanda aka damka ta a hannun Hajiya tukunna suka tafi tare da barin Hasana a wajen ta,dama kusan ba kawaye gare ta ba.
Angwaye na shigowa Hasana ta fara shirin tafiya saboda mijin ta zata bi su tafi gidan su...
9months later....
Lafiya kalau suke Zama da Kursum duk da dukkansu ba mai kula wani kuma babu yanda Amin baiyi da su ba amma basu chanza ba,yanzu kuma ya zuba musu ido yana son ganin iya gudun ruwan su...
Fitowa tayi da bulelen cikin ta wanda haihuwa yau ko gobe , sai yatsine fuska take yi
"Ya aka yi maman biyu?"Amin ya tambaye ta ganin yanda take ya mutsa fuska
"Wallahi sakwara nake son ci!"
Zaro idanuwa yayi ya ce"Sakwa miye?"
Turo baki tayi ta ce " sakwara"
Kallon Kursum da ta wani Sha mur akan kujera tana kallo yayi
Mikewa Kursum tayi tare da wucewa bangaren ta, da kallo suka bita inda Nadhira ta tab'e baki tana cewa
"Ni fa na ce maka zan ci Sakwara!"
"Bari nayi ordering din shi ko"ya fad'a a hankali saboda yasan zata iya cewa ita shi take son yayi da kan sa ga mamakin sa kuma yaga ta zauna tare da cewa
"Toh kayi sauri!"
Ai bai san sanda ya sake murmushi ba, wayan sa ya d'auka tare da yin ordering din sakwaran a eatry
30minutes later...
Shigowar Kursum da tray a hannun ta yasa su miyar da hankalin su kanta
"Anan zaki ci ne kokuma na kai miki kan dining??"
Kallon kallo aka hau yi tsakanin junan su, ganin zasu b'ata mata lokaci ya sa ta ajiye wa a kan silk rug tare da ficewa
"Zo ki ci!"ya fad'a yana jan hannun ta, fixge hannun tayi tana cewa
"In ci miye? Kasan miye tasa a ciki zaka cemun na ci? Allah ya kiyaye! Na ma fasa cin abincin "
"Wallahi nasan Kursum bazata tab'a cutar da ke ba"ya fad'a in a defensive tune
Da kyar ta mike tare da wucewa tana zuba uwar masifa, cikin takaici ya mike shima tare da wucewa part din Kursum dama kuma chan yake da kwana yau
Akan gado yasa mi Kursum na share kwalla,cikin sauri ya karasa wajen ta tare da rik'o hannun ta
Runguman sa tayi da sauri tana cewa" wallahi bazan iya sa mata ko da maganin bacci a abincin ta ba!"
Cikin rashin jin dadin abin da Nadhira tayi yace"I know!"...
Banda safa da marwa babu abinda take yi a cikin d'akin ta, duk uwar ACn dake d'akin hakan bai hana zufa karyo mata ba
Wani siririn ihu ta saka lokacin da taji kaman an zura mata allura acikin cikin jikin ta...
Fitowan ta kenan daga d'akin ta tana son dubawa ko abincin na nan ita ta cinye kar yayi waste
Kaman daga sama taji kuka-kuka, kasa kunnen ta tayi cikin tsoro saboda dare yayi sosai kuma tasan da wuya in Nadhira bata yi bacci ba
"Wayyo Allah na!"taji an fad'a cikin wahalalliyar murya
"Innalillahi" ta fad'a a rikice tare da wucewa d'akin Nadhira
Turus tayi dalilin ganin ta a kasa, kaman wacce kwai ya fashe mata a ciki haka ta karasa wajen
"Wayyo mara ta zata balle!"ta fad'a cikin kuka sosai
Ganin yanda take yi yasa Kursum rud'ewa nan itama ta fara nata kukan...
Tsaki Amin dake jiran dawowar Kursum ya ja ganin yanda ta Jima
"Daga d'auko abinci shine taje tayi zaman ta"ya fad'a tare da sauka daga kan gadon da yake...
Tin daga kofan parlour yake jin kukan su sama-sama,cikin tashin hankali ya karasa shiga cikin parlourn a zaton sa ko fad'a suka yi
Ganin basu falo yasa shi shigowa cikin d'akin,
"Miye faru?" Ya tambaya a rikice ganin dukkansu a kasa suna kuka kaman an musu rasuwa
"Ka taimake ni danAllah zan iya mutuwa inna cigaba da Zama a haka!" Ta fad'a cikin sark'ewar murya
Cikin sauri ya karasa gare ta tare da d'aukan ta yana cewa Kursum ta d'auko khimar
Wawuro khimar guda biyu Kursum tayi tare da bin bayan su da gudu...
Tin jiya ake abu daya har washe gari, banda kuka babu abinda Nadhira take yi gabadaya karfin ta ya soma karewa
"Wai ni haryanzu ana abu daya!" Wata nurse wacce daga gani babba ce a wajen ta fad'a lokacin da ta karaso wajen
"Wallahi sai raki take mana tin dazu kaman ita zata fara labourn duniyan nan"
"Erh din! Anyi rakin ,mugaye kawai!"ta fad'a cikin kuka sosai
Basu hankara ba suka ji saukan mari, zaro idanuwa Nadhira tayi cikin kidiman jin an mare ta
Wani irin nishi mai karfi tayi ai sai ga yarinya ta fad'o wani nishin ta sake yi sai ga wata ma ta sake fad'owa
Wani irin ajiyar zuciya ta sauke yayin da Hawaye masu zafi suka fara silalo ma ta, a hankali a hankali idanuwan ta suka rufe ruff....
Check on my New book: SHUGABA
_Hey 👋 fans! Show me some love by following me on my Instagram *Mhizzphydo*_ I will really appreciate it if you do!.
_Vote, Comment & Share_
YOU ARE READING
ABAR SO
Random"ABAR SO!!!" Shine abinda NAFHIRA tace cikin siezing din breath, aikuwa arikice tajawo NAFHI kan cinyarta "Addua fah kawai zaki mana bah kuka bah, ganinan acikin abinda nafi tsana arayuwa ta (blood)wannan kawai yakara tabbatar min da babu wanda ya w...