💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*
WATTPAD: MHIZZPHYDO
*Book 🅱️Page 16*
Rushing din ta suka yi zuwa asibiti cikin tashin hankali, nan aka fara bata taimakon gaggawa saboda gabadaya numfashin ta daukewa ya yi chak,in ba don jikin ta da ya dau zafi radau ba da zasu iya cewa ta mutu.
Basu gama tsinkewa ba har San da suka ga fuskar ta na sab'a nan suka shiga mamaki al'amarin
San da tayi kwanaki biyu chur kafin ta farka a lokacin har ta sha ruwa ya kai 6 harda su Karin jini saboda yanayin jikin.
"Wayyo Model face dina!"Kursum ta fad'a cikin kuka saboda ganin yanda fatar fuskar ta ya b'aci da sab'a har wani ya mutse wa yafara Kaman wacce ta shafa ruwan kwai a fuska
"It's ok dear!"Amin ya fad'a cikin tausayawa,rik'o hannu sa tayi da sauri tana cewa
"Wannan yarinyan zata iya kashe mutum DanAllah ka sake ta wallahi da wuya na iya zama da ita"
Girgiza kan sa ya hau yi had'e da share ma ta hawayen da suke silalo mata wanda Sam ita bata ma San da su bah,
"Kiyi hakuri dear nima da so samu me nasan yanda zan yi da ita Amma kuma kin ga iyayen ta Suna da Wani waje daban a zuciya ta wallahi bazan iya bah!am so sorry" ya fada gwanin ban tausayi
Jan hanci tayi cikin gajiya wa da sanyin jiki,"toh DanAllah ko zan zauna da ita ba gida daya ba!karka had'a mu saboda nasan it will be a hell for me"
Gyada kan sa yayi yana mata kallon tausayi ganin yanda ta koma lokaci guda...
Gidan Yari...
Zaune take akan gadon su tana karanta littafi,gefe guda Kuma wata ce take yin kneeling da alamun tayi laifi ne
"Ga shi nan zuwa!"wata ta fad'a da karfi da alaman tana musu gargadi ne,kokarin mikewa wacce take kneeling tayi Kaman daga sama taji Nadhira ta ce
"Kar yarda ki Mike!"
Cikin sanyin jiki ta koma tana matsan hawaye saboda daman shishigi me ya kai ta inda take yanzu duk da uwar kashedin da ake mata akan Nadhira
"Miye ke faruwa a nan?"Wani bagidaje ya tambaya lokacin da ya hango mai yin kneeling,
"Hukunci nake mata saboda haka zaka iya tafiya "Nadhira ta fad'a ba tare da ta daga ido daga karatun da take yi bah!
Girgiza kai kawai mutumin yayi tare da yin gaba saboda daman haka take,satin ta 2 a gidan yarin ammakaff wajen babu wanda bai San da zaman ta ba saboda yanayin ta....
BAYAN SHEKARA DAYA....
Sosai take cin duniyan ta Kaman ba agidan yari take bah! Iko kuwa babu wanda basu gani ba, gashi babu wanda ya isayayi complain! Asalima tsoronta suke ji saboda an basu labarin abin da yakawo ta gidan yari , kuma tin da ta shiga bata sake fita ko gaisar da mutanen gidan su bah Kaman yanda in aka kawo musu ziyara ake fita Dan Hiram mintuna goma sha biyar....
"Yau sai gida ko?"wata warder ta tambaye ta,murmushi ta sake had'e da girgiza kan ta
"Wallahi na miki murna sosai,Kuma kar ki manta da addreshin dana baki,Insha Allah zaki ga chanji sosai"
"Nagode sister!"ta fad'a had'e da ficewa daga office din.
A bakin gate ta tarar da duka mutanen gidan su harma da mutanen gidansu Amin,mutanen gidan su Big dady ma ba'a barsu a baya ba
A hankali ta taka zuwa gaban su , hawaye fal idanuwan Antynsu saboda tsananin tausayin Babynsu,girgiza wa Antynsu kai tafara alamun kar tayi kuka amma inaa abin ya fasakara ai kawai ta rungume ta tare da sakin siririn kuka itama
"Nayi missing din ki Antynmu!"
"kiyi hakuri babynmu am sincerely sorry!"
Tapping din bayan antynsu ta hau yi cikin tausayawa,ciro ta tayi tare da share mata hawayen ta tana cewa" bana son wa'inan hawayen antynmu! Karyar mun da guiwa suke yi idan na gani"
Murmushi antynsu ta sakar mata cikin farinciki, gyaran muryar da suka ji ne ya hankarar da su inda suke
"Dadynmu!" Ta fad'a kaman Mai tsoron magana ,ware mata hannu yayi ita kuwa babu kunya ta Isa gare sa tare da rungume sa
"Baki ga surakanan ki bane mara kunya?" Antynsu ta katse su
"Ohh ji son kai! Ke da kuke kukan yaushe gamo baki tina da surakan ta na nan ba sai da kika ga ta rungume ni?"dadynsu ya fad'a cikin ya mutsa fuska
Dariya dukkansu suka sa inda ta gaishe su nan su dunguma cikin mota
Girgiza kai Amin ya yi ganin yanda ta miyar da shi invisible a wajen...
Abinci kala kala aka shirya mata saboda sun san abinda zata bukata kenan a halin yanzu
"Kai Aminullah!"dadynsu ya Kira sunan sa ,cikin girmamawa ya amsa
"Je ka d'aki ka same ta naga ko gaisawa baku yi ba kuma dare na yi !”
Sosa keyar sa ya yi tare da mikewa ,hanyar inda ya ga ta shiga yayi
"Na d'auka kai jarumi ne ai ashe abin ban sani ba acikin lusaran ma kaine na farko!don dabarun ka ya kare shine zaka sa masoya na sumin karya! Ko ban fad'a maka ba nasan kasan yau wa'adin da ka d'iba mun ya kare, so duk hanyan da kasan zan iya haduwa dakai ka gaggauta tare wa in kuma ba haka ba hmmmm and karka d'auka alfarma ko umarni nake baka gargad'i nake maka! Lusarin banza kawaii...
Check on my New book: SHUGABA
_Hey 👋 fans! Show me some love by following me on my Instagram *Mhizzphydo*_ I will really appreciate it if you do!.
_Vote, Comment & Share_
YOU ARE READING
ABAR SO
Random"ABAR SO!!!" Shine abinda NAFHIRA tace cikin siezing din breath, aikuwa arikice tajawo NAFHI kan cinyarta "Addua fah kawai zaki mana bah kuka bah, ganinan acikin abinda nafi tsana arayuwa ta (blood)wannan kawai yakara tabbatar min da babu wanda ya w...