38

1.7K 104 9
                                    

💝💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝

*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*

WATTPAD: MHIZZPHYDO

*Book 🅱️Page 9*

"Bangane babu abinda yasamu kwakwalwarta bah?"Dadynsu yatambaya cikin rashin yarda da abinda doctor yafada

"Gaskiya dai nima haka bincikena yanuna min"

Caraf Antynsu tace"toh binciken ka ba daidai yanuna maka bah! Soboda nasan Babynmu bazata tab'a ignoring dinmu in hankalinta na nan bah!"

Riko hannunta Dadynsu yayi alaman ta kwantar da hankalinta kafin yace"toh munji amma gaskiya zamu tafi India domin a duba mana abinda yake damunta!"

"Toh shikenan sir! Amma ga shawara mana?"Doctor yafada yana kallon fuskar Dadynsu, gyada kai kawai Dadynsu yayi yana jiran jin abinda doctor zai fada

"Miye zai sa baza'a bari zuwa nan da Wata daya kafin atafi daita Indian bah!"

"Ohk toh!"Dadynsu yafada soboda shima sai yanxu yatina ashe bashida wasu isheshun kudi

Antynsu neh cikin rawar murya tace"Haba Dadynsu yazaka ceh kayarda da abinda yace bayan Babynmu na bukatan taimakon gaggawa"

"Ki kwantar da hankalin ki mana ai nasan abinda nakeyi kinji?"yafada cikin kulawa

Gyada kai kawai tayi cikin rashin jin dadi soboda gabadaya ba haka taso bah!....

Inspector Nasir neh tsaye agefen Nadhira sai kallonta yakeyi yana karantar yanayinta, itako tana jinjine ajikin gado yatsarta daya abaki tana tsotson Benson(lolz..)

Hada idanuwa sukayi Nadhira tajefe shi da harara chan saiga yen gidansu Amin sun shigo harda su Dadynsu da Amin ma karan kanshi

Washe baki tayi wa Amin wanda shine biggest mistake dinta wanda batasan tayi bah!

Cikin farinciki Amin yakarasa wajenta tareda zama agefenta yana shafan fuskarta cikin kulawa

Kallon su Dadynsu yayi yace"kunga tafara yarda dani yanzu!"

"Lallai kam!"Dadynsu yafada cikin murmushi inda Mumynshi sai hauna mai harara takeyi wanda ko kadan bai kula da hakan bah

Antynsu kuwa adan gefe tazauna cikin sanyin jiki tana kallon Nadhira wacce takoma mata sabuwar hallita

"Kinsan ni?"Amin yafada yana kallon kwayar idanuwanta

Washe baki tayi tana gyada kanta, dan Zaro idanuwa yayi yace

"Habawa?"

Gyada kanta tayi still yatsar hannunta nacikin bakinta tana aiki tsotso

"Toh waye ni?"

Dan zaro idanuwa tayi tace"namanta ban tambayi sunan ka bah ai"

"Toh nine mijinki!"yafada kai tsaye

Kura mishi idanuwa tayi tace"miji! Miye miji?"

"Wanda zai nayi miki wanka,wanki wanda zaina siyamiki icecream,yadinga baki abinci kuma yadinga goya ki kaman baby"

Kokarin saukowa tafara yi tana fadin"toh ka goye ni"

"A'a kibari sai anjima inda nadawo koh?"

Raurau tayi da idanuwanta kaman zatayi kuka tace"nikam yanxu nakeson kagoye ni"

"Yi hakuri mana Abar so!'

"ABAR SO!?"Tafada cikin sigar tambaya

"Erh mana ke Abar so ceh gakowa ko bakisan da hakan bane?"Antynsu tafada cikin son janta ajiki

ABAR SOWhere stories live. Discover now