40

1.6K 106 6
                                    

💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝

*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*

WATTPAD: MHIZZPHYDO

*Book 🅱️Page 11*

"What! "Dadynsu ya fad'a cikin mamaki,

"Mu gani babynmu! "Alhaji ya fad'a cikin lallashi, mak'e kafad'a tayi tana komawa baya

Matsawa kusa da ita antyn ta fara tana fad'in"Kawo ni ma na iya kosai, yanzu zan miki kosan sai na sa miki a paper! "

Babu yanda ba suyi da ita ta kawo papers din bah amma biris ta k'i saima ko kokarin gudu wa da take shirin yi, kafin su hankara har ta harci na Kare..

Guruf ka keji sun yi karo da mutum!kafin ta gama daidaitawa sai jin wata zazzafar mari tayi a kumatun ta! Turus suka tsaya cikin sanyin jiki da rashin jin dadi

Zaro idanuwa tayi cikin kid'ima da tashin hankali da kuma fusata, wanda idanuwan ta ya kyallaro mata yana zuwa neh ya sata sakin wani irin kuka mai ban tausayi

"Jakar Yarinya kawai! Ace ko da yaushe sai mun buge dake sai kace makauniya, shashashan banza mai Kama da Aliens 👽! "Kursum Ta fad'a cike da takaici

"Lafiya dai kuwa? "Inspector Nasir da karasowar sa kenan ya tambaya ganin yanda Kursum ke kwarara ruwan masifa ga kuma Nadhira a tsaye ta had'a hawaye da majina sai kuka ta keyi da duk karfin da Allah ya bata

"Wayyo mijina ta cire mun ido! "Ta fad'a lokacin da Amin ya iso  wajensu, turus yayi yana kallon kursum da ta wani kara kyau alaman hutu ya ratsa ta

Runguman Amin tayi tana sake sakin wani kukan, sai a lokacin su Antynsu su ka karaso wajen saboda guntun shock din da suka shiga!

"Zo Babynmu"Antynsu ta fad'a cikin lallashi, sake rik'e Amin ta yi da kyau ta ce

"Babu inda zanzo"

Wani irin rikitaccen tsawan da kursum ta daka ma ta neh yasa ta sakin Amin ba tare da ta shirya nan kuwa ta sake fashewa da kuka at the same time kuma jikinta na daukan b'ari

Cikin b'acin rai Dadynsu yace"DanAllah baiwar Allah ki bar ta taji da abinda yake damunta! "

Kallon dadynsu Kursum tayi a walakance wanda a wajen babu wanda bai ga irin kallon bah cos hatta Nadhira da ke kuka ta gani!

Kallon Amin tayi cikin rainin hankali ta ce"ban gane bah a ina kuka kwaso su? Ohh Kar dai wannan mahaukacin da ke zama a boy's quatars dinnan neh ya warke? "

"Ke baki da hankali neh? "Alhaji ya fad'a cikin b'acin rai, da hannu ta dakatar da shi tace

"Ina ganin girman ka sosai Alhaji saboda kaine mijin Hajiyata da kuma baban mijina! "

Jajayen idanuwan ta ta d'ago ta d'aura a kan Kursum dake zuba rashin kunya, Antynsu kan ji ta keyi kaman ta wanka ma ta Mari amma rashin kwarin jikin da ke tare da ita yasa ba ta iya aiwatar da abinda ke ranta bah

"Ina jiran amsa mijina! "

"Say sorry!" Ya fad'a cikin bada umarni yana kuma  kallon kwayar idanuwan ta irin shi miji dinnan

"Wlhy bazan ceh bah! "Hawayen da suka silalo a kumatun Nadhira antynsu tasa hannu ta share Wanda duk a kan idanuwan inspector neh

"Ji yanda yarinyan nan ta ke kallo na! Ko zaki rama marin neh saboda na ga alamun ya shiga "ta fad'a tana kallon Nadhira dake kallon ta cikin b'acin rai saboda yanayin ta bai iya b'oyewa bah

Hannunsa ya zuba a aljihun sa yana bin ta da kallon zan Kama ki kafin ya ce"Don't cross your limit Kursum, zai fi miki idan kin shige cikin gida! "

Tab'e baki tayi tare da watasawa Antynsu harara kafin ta shige cikin gida saboda a yanzu bata son wani abinda zai tab'a lafiyar jikinta kuma tasan mudin bata yi abinda ya ce bah toh lah shakka yana iya kai mata duka a gaban mutanen duniya!

"Kuyi hakuri DanAllah! "Amin ya fad'a cikin jin kunya sosai, murmushi irin ta su na manya dadynsu yayi kafin ya ce

"babu komai! "

Girgiza kai "Hmm nasan da da hankalin Babynmu wlhy bazata tab'a barin ta ta wuce haka kawai bah saboda Babynmu bata san hakuri bah all she know is _do me I do you_"

Kallon Nadhira suka yi inda suka ga har lokacin bata d'auke idanuwanta daga inda Kursum ta shige bah, tab'a da Antynsu tayi ya sata lumshe idanuwanta nan kuwa sauran hawayen da suka makale suka samu daman gangarowa

Bata bari sun yi magana bah tayi part din su da gudu tare da papern a hannun ta, da sauri Antynsu ta mara mata baya inda sauran kuma suka yi jugum kowa da sak'e-sak'en da ya keyi aransa...

Banda kai da komowa babu abinda ta ke yi a cikin d'akin, ji ta keyi idan har bata d'auki fansa toh lah shakka tana iya mutuwa, daga karshe dai ta zube akan gado kaman wata elephant duk da ba wani jiki gareta bah amma yanda ta zube a kan gadon ya jawo hakan.

Antynsu kuwa sai faman knocking ta ke yi amma Nadhira tayi biris da ita saima headphone da ta d'auko ta sa a kanta, kafin ka ce kit har bacci ya dauk'e ta!...

Kusan a zaune suka kwana ranan kuma zuciyoyin su cike da zulumi saboda basu san halin da ta ke ciki bah gashi kuma tak'i bud'e musu kofa asalima basu san ko jinsu bata yi bah!

Da safe ganin in suka biye ma ta akwai matsala neh ya sa Amin nemo mai balla kofa saboda shima bai iya bacci ko in fact ko abinci bai iya ci bah!

A kan gado suka same ta tayi kudundunu a cikin bargo sai kace a na sanyi, da sauri Antynsu ta karasa wajen ta tare da bud'e bargon, girgiza kai tayi ganin yanda zufa ya rufe ta kaman wacce aka kwarawa ruwa

Share zufan tayi nan ta ji jikinta zafi rad'au kaman wacce aka ajiye ta a gefen wuta, karasa yaye bargon Antynsu ta yi kafin ta kirawo su cikin d'akin saboda daman Kar ya zamto bah kayan kirki a gareta bah shiyasa Antynsu ta fara shiga.

Gwada temparaturen ta yayi kafin ya fice su Antynsu kuma suka yi jugum suna kallonta, ba wani dadewa sosai yayi bah ya dawo rike da Leda

Drip ya daura ma ta tukunna amma ko gizau bata yi bah!  Sanda drip din kare kafin ta farka.

Murmushi antynsu ta sake tana kuma shafa fuskarta

"Sannu! "Su ka fad'a cikin had'a baki, lumshe idanuwanta ta yi alaman toh kafin ta sake bud'ewa, drip din Amin ya cire ma ta kafin antynsu ta taimaka mata zuwa cikin toilet din.

Kaman kullum yau ma haka ta tsaya a gaban mirrorn toilet tana kallon fuskar ta, hannu ta kai ta shafa wajan da Kursum ta mare ta kafin ta saki murmushi mara saut! chan ta tsuke fuskar ta tafara kai da komowa a cikin toilet din, kwankwasa kofan da ta ji ana yi neh ya sata jan guntun tsaki kafin ta tub'e ta fara wanka...

Zaune ta ke a kan kujera tana latsa wayan ta shikuma yana kwancen a kan gado fuskarsa na facing POP da alamun tunani ya ke, kallon sa ta yi kafin ta ce "Love! Yaushe zamu koma gidan mu?"

"Aure na next week! "Ya fad'a instead of ya bata amsan tambayan ta, murmushin rainin wayo ta yi kafin ta ce

"Yaushe ka dawo Abdulkadir? Saboda a iya sani na Abdulkadir neh zai yi aure next week! "

Shafa kansa yayi kafin ya ce"erh Nima zan Kara neh! "

Ajiye wayar hannunta ta yi gabanta na dukan uku sau goma, wani yawu mai d'aci ta hadiye, cikin son daidaita kanta tace "waye neh zata aure ka? "

"ABAR SO!"Ya fad'a yana lumshe idanuwan sa kaman baya cikin fargaba

Mikewa tayi daga zaunen da ta ke, cikin rawar murya sosai tace "ABAR SO Kuma?? A ina ka same ta? "

Tashi yayi ya zaune tare da kura ma ta idanuwa sannan ya ce "A nan gidan ta ke!  Wato wacce kika mara dazu!"

"Kam bala'i!"Ta furta cikin tsananin b'acin rai da tukikin kishi, dube-dube ya ga ta fara chan idanuwan ta ya sauk'a a kan kwalban champaign dake ajiye bata yi wata-wata ba ta wawuresa tare da yin waje da mugun gudu....

_Hey 👋 fans! Show me some love by following me on my Instagram *Mhizzphydo*_ I will really appreciate it if you do!.

_Vote, Comment & Share_

ABAR SOWhere stories live. Discover now