41

1.6K 99 6
                                    

💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝

*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*

WATTPAD: MHIZZPHYDO

*Book 🅱️Page 12*


Cikin tashin hankali ya bi bayan ta da mugun gudu shi ma cikin son ya cimmata amma abin ya faskara saboda har ta sauka daga matakalar benen tayi waje cikin mugun speed daga gani ma stairs uku-uku take tsalakewa ,straight boys quatars ta nufa,

Dadynsu da kuma Alhaji dake zauna suna tattaunawa akan yanda Dadynsu dakuma Nadhira zasu tafi India saboda sun samu papers din da ya ke hannun ta dukda uban mamaki da zulumin da zuciyarsu ke ciki game da inda Nadhira ta samu papers din!

Gani suka yi an wucesu fhew kaman guguwa, nan suka Kara ganin Amin shima ya taho da gudu yana faɗin

"She's Harmed! "

"Waye? "Suka tambayesa cikin haɗin baki amma ko amsawa bai yi bah asalima ko juyowa bai yi bah, suma basu yi kasa a guiwa bah suka mara mai baya!

Gani ya yi ta fito daga wani ɗaki tana shirin buɗe dayan daga gani neman Nadhiran ta ke yi

"Dan kaza Kazan ki Ina ki ke? "Ta faɗa cikin karaji hawaye masu zafi na silalo ma ta saboda kishin da ke addabar zuciyar ta, wuff ya yi ya rike ta ta baya tare da fara kiciniyar kauce kwalban a hannun ta wanda hakan ya yi daidai da shigowan su dadynsu

Yana karɓan kwalban ya juyo da ita tare fizgewa ta yi tana ihu har san da antynsu da Nadhira suka fito a tsorace, tana haɗa ido da Nadhira ta yi kan ta tana mai jijiga kafadarta

"Wai yar ke dinnan neh daman ki ke neman kwace min miji? Waye ya baki wannan confidence din? Kin san ni kuwa? Wlhy Ina iya kai sunan ki wajen malamai su haukatar mun da ke! Ke bama haukataki zan sa su yi bah kashe ki zan sa suyi in yaso daga iyayenki har shi mijina suyi rashi! "

Afirgice dukkan su suke kallon ta barinma Nadhira da idanuwan ta su ka yi jazir kaman garwashin wuta.

Zata sake magana kenan ta ji saukar wata gigitacciyar Mari a kumatun ta! Ai a saba'in ta saki Nadhira hawaye na zubo mata kaman an buɗe famfo

"Ka Mari ni? Ko da yake ba yau ka fara duka na a kan ta ba! Wani tsaya ma tukunna laifi miye na yi maka? Fine na san ba ka taɓa sona bah! Yes nasan da hakan amma Ina laifin me son ka? Laifi ne don naso ka? Tell me" ta fad'a gwanin ban tausayi haɗe da zubewa a kasa tana fashewa da kuka mai cin rai

Gabadaya wajen babu wanda jikin sa bai yi sanyin ba hatta ita Nadhiran

Zama suka yi inda Kursum sai share unstoppable hawayen fuskar ta ta keyi, ita kuwa Nadhira kaman wata mage haka ta kanainaye Antynsu cike da tsoro ga idanuwan ta da suka yi ja saboda har yanzu tana jin sautin muryan Kursum a cikin kunnenta

"Gaskiya lamarin da ya farun nan ban ji dadin sa ba ko kaɗan!"Alhaji ya faɗa cikin Nuna rashin jin dadin sa kaman yanda ya faɗa a zancen sa

Juyawa wajen da Kursum ke zaune ya yi yace"Kursum wannan da kika gani kanwa ce a gareki! Kuma ba cikekkiyar lafiya gare ta ba saboda matsalar kwakwalwar da ta ke d'auke da shi wanda mu ke adduan Allah ya dawo ma ta da tunanin ta nan kusa! Kuma shi ƙarin aure ba haramun ba ne! Ya hallata saboda fiyeyyen hallita Annabi Muhammad (SAW) ma ya kara aure kuma ya kuma umartan mu da mu kara in har zamu yi adalci a tsakanin s.. "

Katse Alhaji Kursum ta yi da faɗin"Amin ba zai tab'a yin Adalci ba! Tin kafin nasan ta ido da ido ya ke nuna mun cewan ita ya ke so! Tin ban san ta ba ya ke duka na saboda ita Ina kuwa ga ya aure ta? Na tabbata kashe ni zai yi saboda ita daga karshe kun ga kuwa in na fara kashe ta ban yi laifi bah!I hate her right from the begining! ke Abar so ko? Aww na tina ma kunce mahaukaciya ce it...

"Watch your mouth!"ya katse ta cikin tsawa wanda ya sata firgita bama ita Kadai ba har da mutanen wajen gabadaya, cikin kuka ta miƙe tana cewa

"Allah,kasan ba zaka hana ni magana bah! Kuma na faɗa Allah duk ranan da wannan mahaukaciyan ta tare a gidan ka to ka tabbatar washe gari za'a yi jana'izar ta! "

Miƙewa ya yi da sauri tare da nufan in da ta ke wanda hakan na nuna alaman mazge ta zai yi,Muryan Dadynsu neh ya katse sa da faɗin

"kar ka kuskura ka taɓa ta!"

"Barshi ya taɓa ni wlhy da babu abinda zai hana ni ramawa a kan wannan mahaukaciyar sa!"

"Fita a nan!"Ya faɗa yana nuna ma ta kofa trying to be calm,hanyan waje ta nufa tana magana kasa-kasa, sanda ta isa bakin kofa sannan ta juyo cikin ɗaga murya ta ce

"Ke mahaukaciya!wallahi kika kuskura tsautsayi ya sa ki ka shigo gidana to sunan ki Sorry!" Ta faɗa haɗe da ficewa da gudu

Murmushi Dadynsu ya sake saboda sai yanzu ya gane matsalar dukkansu biyun!ya gane cewa Kursum ko kadan bakin ta baya mutuwa ko da kuwa wuƙa za'a sanya a wuyar ta ,shi kuma Amin ba shi da hakuri ,murmushi ya sake sakewa a karo na biyu lokacin da ya haɗa ido da su Antynsu da ke kallon sa barinma Nadhira da ke kallonsa kaman eyes na ta zasu faɗo! yasan duk kuri Kursum ta ke yi saboda yasan halin ƴarsa

Alhaji ne ya sauƙe ajiyar zuciya mai karfi saboda sosai maganan kisan da Kursum ke cewa zata yi ya addabe zuciyar sa,kallon Amin da kan sa ke sunkuye ya yi ya ce

"Gabadaya ban ji dadin abin da ka yi yanzu ba"

"Babynmu, muje ko!"Antynsu ta fad'a saboda ganin bai dace ace su zauna sauraren faɗan da za'a yi ma Amin bah

Bayan sun tafi ne Dadynsu ya ce"Wa ya ce ma ka ana dukan mata!gaskiya na sha mamaki! kuma nima ban ji dadi bah! yanzu haka ka ke son na baka auren ƴata? anya za ka yi adalci kuwa?"

Mikewa Alhaji ya yi fuskar sa na nuna seriousness a kan maganar da zai yi,cikin isa da nuna cewan shi din uba ne a wajen Amin ya ce"Maganar auren an soke sa har sai sun sasanta da matar sa! kuma sai ta yarda ta karɓi Nadhira da hannu biyu a matsayin a bokiyar zama"

wani irin faɗuwar gaba da tashin hankali ne ya ziyarci zuciyar Amin nan gaban sa ya hau dukan fat fat fat kaman zai fasa kirjin sa ya fito,wani yawu mai ɗaci ya haɗiye yana kallon inda baban nasa ya ke wayam ya ga baya wajen nan ya fahimci ashe ya fice ne!

Kallon wajen da Dadynsu ke zaune ya yi,murmushi Dadynsu ya sakar mai ya ce "do as he say!"

Wani huci ya sake yana lumshe idanuwan sa saboda yasan abu ne mai matukar wuya Kursum ta yarda da batun sa ,he's so confused

"kar ka bada maza mana Aminu!"

"bansan ya zan yi ba ne ta amince wlhy da wuya ta amince!"ya faɗa kaman zai yi kuka

Dafa sa Dadynsu ya yi ya ce"ni zan faɗa ma ka yanda za ka yi kuma ta amince"

waro idanuwansa ya yi ya ce"dagaske?"

"inshaAllah!"

wani farin ciki ya ji ya lullube sa nan ya hau washe bakin sa kaman gonar auduga , a wajen kafar dadynsu ya zauna tare da kallon fuskar sa yana jiran jin abinda Dadynsu zai faɗa....




_Hey 👋 fans! Show me some love by following me on my Instagram *Mhizzphydo*_ I will really appreciate it if you do!.

_Vote, Comment & Share_

ABAR SOWhere stories live. Discover now