💝💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*
WATTPAD: MHIZZPHYDO
🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟🌟G.W.F🌟
HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST
*Page 95*
"Yauwa Rafin dadi nah daman so nake ki samin Ido akan wannan yarinyar yazamto kowani motsinta akan idonki zai kasance"
Wani irin dariya tayi sannan tace"indai wannan ne karka samu damuwa…"ahankali takoma dakinta batareda ta karasa jin abinda suke fadi bah…
Wata ajiyar zuciya tasauke data shige cikin daki, tunani dayawa neh yake shawagi a brain dinta kafin tasaki wata shegiyar murmushi tana fadin
"Taab lallai kinshirya barin aikinki indai ido zaki samun, ke zanfara kawarwa tukunna…
**********
Amin kam yana komawa gida yashiga matsanancin damuwa, bayani yake bukata gameda condom dinda tasiya…
Tashi yayi yaje palour soboda wani tunanin daya darzu mishi azuciya,yakuwa ci sa'a kowa na wajen…
Sallama yayi cikin nutsuwa inda suka amsa mai hankali su yana mai komawa kanshi…
Gaban Dady yaje ya tsuguna tareda sune kanshi akasa alamun jin kunya,shiru ne ratsa wajen na mintina…
Dady ne yakatse shirun fadin"Da akwai magana abakinka Aminu"
Gyada kanshi kawai yayi still baiyi magana bah
"Kai banson shashanci inbaka da abin fada kayi gaba,kawani zo kasamu agaba kaman wasu yaranka" " mumy tafada ahasale
Cikin nutsuwanshi yace"Ayi hakuri mumy,daman… daman… nace in ba matsala auren…" sai kuma wutanshi ya dauke yana dada sune kai kasa…
Dariya irinta manya dady yayi inda Abba kuma mamakin rashin kunyan Amin yakeyi, antyn ma dariya tayi mumy kuwa kunya taji yakamata…
Dady ne yace"Nagane abinda kakeso, kaje zan neme ka"
Cikin sosa keya yace" Nagode Dady Allah yakara girma"
"Ameen" suka amsa sannan yafita daga palourn
Dady neh yamayarda duban shi zuwaga Abba sannan yayi gyaran murya yace
"Ina fatan kasan inda zancen yaron nan ya dosa??"
"Eh ranka shi dade" Abba yafada cos yana mugun ganin girman dady…
Murmushi dady yayi sannan yace "nalura baka son in cigaba da zama anan gidan fah"
"Na isa??"
"Bagashi kana kirana da ranka shi dade bah bayan ni yakamata nakira ka da ranka shi dade" dady yafada
"Toh nadaina"
"Yanxu yah kke ganin zamuyi??"dady yatambaya
"Ai duk yanda kace haka za'ayi"
"Toh InshaAllah ranar da za'ayi nasu Abdulkadir Sai ahada danasu, Sai afara shirye shirye" Dady yafada…
Wani irin farinciki yakeji acikin ranshi cos tindazu a labe yake ajikin kofa yanajin abinda suke fadi…
***********
*3 days later…*Yen kwanaki ukun datayi acikin gidan ta kara Lura da abubuwa dayawa acikin gidan,daita ake kowani abinci agidan yanz u inda kuma yanzu Maimuna ce target dinta dan haka yau tayi niyyar fara aiwatar da kudurinta akan Maimuna din.
Maimuna mah bata fasa bibiyarta bah cos itama kowani motsin Nadhira akan idonta yake amma har yanzu bata samo komai gameda ita bah,
Data fadawa Big Dady Sai yace kawai su shareta , yanxu dai zance Maimuna ta share batun sawa Nadhira ido…
Tindazu take kitchen tana taya Maimuna aiyuka inda Maimuna ta Lura Maimuna ta fiye shan coke,abu kadan Sai adan kurbi coke dinnan,
Fakan idon Maimuna tayi tazuba mata codeine acikin coke dinta ,inda tsantsan mugunta irin na Nadhira babban kwalba tazuba mata aciki, su Maimuna kam banda waka babu abinda takeyi, kuma dayake tabawa coke din baya amma tsantsan rashin Kula irin na Maimuna ko jijigawan datake yi bata ji bah,
"Nikam Maimuna wannan coke din daya rage dinnan zaki iya shan duka alokaci daya"Nadhira tafada tana nuna coke dinda ko rabi bai kawo bah,
Sanda Maimuna tayi wani irin dariya kafin tace" ke bakisan nayi course a iya shan coke bah??"
"Toh taya za'ayi nasani inba gwada min kikayi bah??"
"Tsaya kisha mamaki" Maimuna tafada tana kafa goran abakin ta , tsantsan hadama ko irin kwarewan nan batayi bah,gyatsan da Maimuna tayi bayan ta ajiye gora neh ya katse mata mamakin ta.
"Ya Kika gani??"tafada tana dage mata gira
Dariyan jin dadi Nadhira tayi sannan tace " wlhy nadauka bazaki iya bah, barina dauko miki nawa kisake sha mugani"
Dadi kaman ya kashe Maimuna cos daman kullum guda biyu take sha arana amma gashi yau garabasa tasamu zatasha guda 3,
Fita Nadhira tayi straight dakinta ta nufa sanda taboye kwalban codeine dinda ta juye mata dafarko abayan gado sannan tasake fitowa dawani again sanda tadan zubar da kadan kafin tasake zubawa aciki(nace kaii Nadhira ke muguwar karshe ceh…) sanda Tajijiga dakyau sannan tayi takoma wajen uwar kwadayi
"Gashi harna bude miki"tafada tareda mika mata,karba tayi sannan tace
"Kin kyauta wlhy" aranta kuwa fadi take ashe Nadhira akwai mutunci(nace Maimuna kenan hhh),
Kafa goran tayi abaki amma ko rabi batayi bah tafara ganin Zion,wani irin zumm zumm take jin kanta na mata,
Ajiye goran tayi tafara ganin Nadhira shida shida, dagudu Nadhira tashige dakinta takwaso kwalaben codeine taje tazube su acikin sif din Maimuna,
Lokacin datakoma kitchen din ta tarar da Maimuna cikin maye,cikin muryan Masha ya tace
"Miye Kika samin a coke??dayake bata gama loosing sense dinta bah
Dariya mara sauti Nadhira tayi sannan tace" duk abinda naga zai zamemin matsala a harkan dana sa agaba toh lah shakka kawar dashi daga hanya nakeyi"
Wani irin sarawan da kanta yayi yasata sakin wani irin dariya amadadin kuka,
Jin dariyar da akeyi yayi yawa yasa mumy dakuma su Fatima saukowa daga sama cikin sauri,hanyan kitchen din da suke jin dariya suka nufa,
Turus sukaja suka tsaya SAKAMAKOn ganin Maimuna akasa,itakuwa Nadhira takurewa tayi jikin garu,tana ganin mumy tayi wajen ta gudu sannan tace
"Mumy bansan miye ke damunta Sai fadin maganganu maras a dadi takeyi akan itada big dady"
"Wlhy son Alhaji nakeyi irin sosai dinnan…"suka tsinkayo muryan ta tana fada,tana tashi tayi tana layi …
Mumy kam notin kanta taji yana neman kwancewa cikin dauriya mumy tace
"Wani Alhajin kikeso??"
Wani irin dariya tayi sannan tace "wani Alhajin kuwa baya…
*Comment,*
*Vote&*
*Share**💋💋 wurarh💋💋*
YOU ARE READING
ABAR SO
Random"ABAR SO!!!" Shine abinda NAFHIRA tace cikin siezing din breath, aikuwa arikice tajawo NAFHI kan cinyarta "Addua fah kawai zaki mana bah kuka bah, ganinan acikin abinda nafi tsana arayuwa ta (blood)wannan kawai yakara tabbatar min da babu wanda ya w...