💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*
WATTPAD: MHIZZPHYDO
*Book 🅱️Page 14*
Wani irin kukan kura Inspector ya yi lokacin da ya gama karanta sak'on da aka turo mai, safa da marwa ya fara yi a cikin office din sa, nan da nan ya jik'u da zufa!....
_India..._
Duk iya kacin binciken da ya kamata a yi wa Nadhira anyi sa kuma result daya ke fitowa, wato lafiyan ta kalau babu abinda ke damun kwakwalwar ta! wanda hakan ya yi mugun basu mamaki!
Babu yanda ba'a yi wajen sa Nadhira dawowa daidai ba amma abun ya faskara har su Dadynsu sun fara tunani ko dai iska ne suka shafe ta....
Antynsu ce ta bada shawaran komawa da ita bayan an gama mawa daddynsu gwaji, amma kuma sai Likitan ya d'aura ta a kan magani kuma yen uwan Margayiya Momma sun ce abar musu ita zasu mata magana irin na su na indiyawa!
Dakyar da dadynsu ya yarda kuma akan sharadin bayan wata daya zasu dawo su d'auke ta! Wannan batun ba karamin dadi ya mawa Nadhira ba!....
Bayan shekaru biyar!...
Tsaye na hango wasu yenmata uku a cikin aji kowa da abin ya ke rike da shi , daya daga cikin su ce ta ja tsakin da ya jawo hankalin daliban da suke zaune, girgiza kai kawai suka kowa ya cigaba da abinda yake yi saboda inda sabo yaci ace sun saba da halin su yen group din Baby Nadhira!
Cikin indiyanci Nadhira ke cewa"wai miye ne kika ishe mu da tsaki ne? In kin sa nan bai miki ba zaki iya tafiya saboda daman bada igiya muka janyo ki ba! "
Harara Fatima ta maka mata tana turo bako "kutt ni kike harara? "
Nadhira ta tambaya cikin hasala da b'acin rai, ganin yanda Nadhira ta jefo mata tambayan yasa ta aza murmushi akan fuskar ta tana cewa "haba dai my dear sisto, wacce ni na harare ki"
Nadhira zata sake magana kenan wayar ta ya dau ruri, "My Husband! shine sunan dake yawo a saman screen din wayar ta
Hanyar waje kawai ta yi tana receiving call din kaman b'ata so! Sai uwar harara da dangwali da take kai wa fuskar wayan kaman wanda yake kiran ta ne a wajen
"Abar so na! "Taji ya fad'a daga dayan bangaren, jin bazata amsa ba yasa shi fad'in
"Antynki bata da lafiya fa! Tin last month akayi admitting din ta a asibiti "
Cikin tashin hankali take fad'in" miye kake cewa? "
"Baby Antynki babu lafiya sosai! "
"Shine sai yau kuke fad'a mun? Ina take yanzu!? "Ta tambaya cikin d'auriya saboda dab take da fashewa da kuka
"Ga ta nan! "Ya fad'a
"Babynmu! "zama tayi akan dakali cikin mutuwar jiki dalilin jin yanda antynsu ta Kira sunan ta Dakyar
Cikin kuka take fad'in"Miye ke damunki antynmu?"
"Babynmu danAllah ki dawo na miki kallon karshe kafin na mutu! "
Kuka ta fashe dashi tana cewa"ki daina fad'in irin wannan maganan antynmu! Bazaki mutu ba insha Allah ai cuta ba mutuwa bace! "
"Nasani Babynmu danAllah kece last wish dina please ki dawo hakan nan babu mai miki komai wallahi yanzu baki ga yanda su big daddy suka dawo ba wallahi ke karan kan ki sai kin tausaya musu! "Antynsu ta fad'a kaman ba ita a kace bata da lafiya ba
YOU ARE READING
ABAR SO
Random"ABAR SO!!!" Shine abinda NAFHIRA tace cikin siezing din breath, aikuwa arikice tajawo NAFHI kan cinyarta "Addua fah kawai zaki mana bah kuka bah, ganinan acikin abinda nafi tsana arayuwa ta (blood)wannan kawai yakara tabbatar min da babu wanda ya w...