49

1.3K 77 7
                                    

💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝

*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*

WATTPAD: MHIZZPHYDO

*Book 🅱️Page 20*

Zaune take akan gado tana bawa daya daga cikin babyn ta nono, gefe daya kuma Kursum ne zaune rik'e da dayan babyn

Amin da bakin sa yak'i rufuwa tin jiya ne ya shigo cikin d'akin da paper a hannun sa

Kallon su yayi ya ce"Mu tafi in kun gama shirya wa"

"Ga su ka fitar sai ka dawo ka karb'i babyn"Kursum ta fad'a tana kallon babyn hannun ta, d'aukan bags din su yayi waje dasu

Ji ta ke dama y'ar ta ce,sosai take cike da nadama, dawowar Amin ne ya hankarar da su

"Muje ko"Ya fad'a daidai ya karb'i babyn daga hannun Nadhira, sannan suka fice daga ward din

"Oops danAllah ina zuwa!"ta fad'a lokacin da suka iso gaban motan

Cikin mamaki Amin ya ce"Ina kuma zaki je?"

"Zan duba wata ne"ta fad'a tana kokarin barin wajen,

Straight inda tasan zata same ta ta nufa, a zaune ta same ta tana duba abu a takadda

Bata yi wata-wata ba ta karasa wajen tare da d'auke ta da wata gigitacciyar mari

Zaro idanuwa mutanen wajen suka yi cikin kidima,bata gama d'agowa ta kara mata wani marin

A razane matan ta karasa d'agowa tana kallon wacce ta mare ta, kun san kuma mari daya ake iya ramawa saboda in biyu aka maka firgici da mamaki bazai bari ka rama ba

"A lokacin da na ke nakud'a kin san wani irin wuya na ke sha da zaki mare ni?daga gani ma baki san zafin haihuwa ba! Saboda da kin san zafin haihuwa da ba zaki mun koda tsawa ba!"tana gama magana ta fice daga wajen inda ta bar mutanen wajen a freeze

Runtsa idanuwa matan tayi cikin tsananin firgici, a hankali ta bud'e  idon inda mutanen wajen suka hau jimamin abinda ya gama faruwa yanzu...

Da murmushi ta tare su tare da shiga cikin motan, sannan suka wuce

Ko kwana biyu basu kara ba suka wuce Bauchi saboda daman su Antynsu sun so zuwa tin kafin ma ta haihu amma suka ce da zaran ta haihu zasu dawo...

Anyi suna lafiya inda yara suka ci sunan Momma da Nafhira,

After 6month...

Yara sun kara girma Masha Allah har sun koma Abuja ma

Abin da yake basu mamaki bai wuce yanda Momma bata kuka ba kuma bata fara rarrafe ba kaman yanda sisto take yi ba(Momma ake cewa Nargis, Nafhira kuma ana Kiran ta da sisto)

Gabadaya yanda yarinyan take yi bai yi kama da wanda normal mutum ke yi ba

Sosai abun yake basu mamaki nan suka garzaya da ita asibiti inda doctors suka ce basu ga abin da yake damun ta ba

A haka suka koma gida cikin rashin jin dadi

"Miye likita ya ce??"Kursum dake zaman jiran su da Sisto ta tambaya

Dan kwallan daya taru  mata ta d'auke cikin rashin jin dadi take cewa"wai basu ga abinda ke damun Momma na ba!"

"Sai ku shiga ko?"Amin ya fad'a....

Bayan Shekara daya....

Duk maganin da ake yi wa Momma babu wanda yake aiki saboda yarinyan bata kara girma kullum a kwance take , bata kuka bata komai sai dai dariya kawai

Nadhira kullum cikin kuka take gashi ta Riga da ta bada Sisto ga Kursum wato Halak Malak wanda hakan ba karamin faranta ran mutanen familyn su yayi ba saboda ganin Nadhira ta yi turning into new leaf

"Baby miye zai hana akai yarinyan wajen malamai a mata Addua?"Kursum dake mawa Sisto kalaba ta fad'a a hankali gudun kar a gwatsale ta

"Ohh wallahi kin kawo shawara, bari in ya dawo sai na fad'a mai" Nadhira ta fad'a

Amin na dawowa kuwa ta fad'a mai nan yayi na'am da shawaran

Ba b'ata lokaci ya fad'a wa Alhaji a gida akan a je musu wajen Malamai....

"Wai fa dole sai sun ga maman yarinyan kafin a iya yin komai"yaji Alhaji ya fad'a daga dayan bangaren,cikin ladabi ya ce

"inshaAllah gobe zamu taho"

Nan suka yi Sallama inda ya ce wa su Nadhira su shirya washe gari zasu koma Bauchi

_BAUCHI_

Bayan sun isa Alhaji ya gayyato Malamin har gida, ba b'ata lokaci ya nemi ganin Nadhira

Cikin nutsuwa ta yi Sallama tare da gaishe da su cikin ladabi inda su kuma suka amsa mata

"Baiwar Allah miye kai ki?"shine tambayan da Malam ya jefe ta dashi

Check on my New book: SHUGABA

_Hey 👋 fans! Show me some love by following me on my Instagram *Mhizzphydo*_ I will really appreciate it if you do!.

_Vote, Comment & Share_

ABAR SOWhere stories live. Discover now