💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*
WATTPAD: MHIZZPHYDO
*Book 🅱️Page 17*
"We thought kin chanza! Ashe we're all mistaken!ina fatan kinsan Wanda kika gama magana dashi yanzu? Amma kuma kike threatening din shi?why won't you change fisabilillah ehen? Wallahi ina jiye miki ranan da zaki mawa wata wacce ramokon ta ya Fi naki ne!" Amin da ya gama Jin abubuwa da ta ke cewa akan waya ya fad'a mata cikin takaici da b'acin rai
Ganin zata yi magana ya sa shi ficewa daga d'akin cikin fushi inda ta bishi da Kira amma ko amsawa Bai yi ba
Koma wa tayi tare da zubewa akan gado tana furzar da iska Mai zafi
Amin kam ko sallama Bai samu ya musu ba ya fice abinsa saboda B'acin rai...
After a week....
Nadhira ta murmure har k'iban ta ya dan dawo,
Ganin Amin Bai kara zuwa ba ya sa abin damun ta sosai ,kuma in ta Kira wayan sa baya d'auka don haka yau ta kuduri niyyan zuwa gidansu
"Antynmu! Zanje gaida su Hajiya!"ta fad'a daidai ta fito cikin shirin ta na fita anguwa
Kallon ta antynsu tayi cikin mamaki ta ce"Ban gane zaki je gaishe su ba ke da muka saka ran mika musu ke nan da sati"
Zaro idanuwa tayi tace" what?"
Girgiza kai antynsu tayi, zata yi magana kenan suka ji dadynsu na cewa"kar dai kin manta da auren Aminullah da ke kan ki!"
Ya mutsa fuska ta hau yi cikin takaicin jin wai ta manta da auren masoyin ta dake kan ta
"Maza-maza ki shige cikin gida yanzu!" Dadynsu ya fad'a cikin bada umarni
"Ohh Allah ai wannan gaisuwan na daban ne saboda a yanzu ba'a matsayin surka zan je musu ba! Zan je musu a matsayin babyn da suka sani don in nuna godiya ta Gare su a kan abubuwa da suka mana"ta fad'a cikin marairaice fuska
Da hannu dadynsu ya rike kai alamun ya gaji kafin ya ce"ki Kira mijin ki ki fad'a mai toh!"
Murmushi ta sake tana cewa"ai na Kira sa kuma ya ce nazo!"
Ganin antynsu na bin ta da kallon rashin yarda ya sa ta Fara kokarin fita tana musu sai ta dawo...
Sosai suka yi mamakin ganin ta amma suka basar, har kitchen suka shiga ta taya Hajiya girki kuma Hajiya tayi making sure bata fita ko d'aga ido daga kan Nadhiran ba saboda acewarta bata yarda da Nadhira ba!
"Ni wai su Kursum ba sa nan ne?”Nadhira ta katse shurun su tana kallon yar aikin gidan
"Anty Kursum bata nan!"
"Amin fa?"ta tambaya da sauri ganin Hajiya ta bar wajen
Cikin ladabi ta ke cewa"Yana d'akin sa ,shine ma ya aike ni na had'o mai tea"
"Tea da uwar ranan nan?"ta tambaya cikin mamaki
Girgiza kai tayi tare cewa"Don't worry kawo na kai mai!"
Ba tare da musu ba ta mika mata tray din ita kuma da amsa da murmushi a samar fuskar ta
Sanda ta gama daidaita nutsuwar ta kafin ta shige d'akin ba tare da ta kwankwasa kofa ba
Fitowar sa daga bayan gida kenan ya fito daga wanka,daga shi sai towel a kugun sa
Mamakin wacce ta shigo babu sallama ne ya kama sa saboda a iya sanin sa Kursum sai dare zata dawo
Jin kaman ana kallon sa ya sa shi fadin "ke yaushe na Fara irin wasan da ke da har zaki shigo dakinmu kai tsaye"
Murmushi ta sake jin yanda ya wani juya mata baya,ajiye tray din hannun ta tayi tare da cire khimar din jikin ta(karku manta Khimar sister ce)
A hankali kaman tsoron kasa ta Fara takawa zuwa wajen sa
Bai hankara ba kawai yaji hannu na yawo a jikin sa, zabura ya yi tare da juyowa da sauri
Caraf idanuwan su ya sark'e a na juna, matsawa yayi baya kadan yana kare mata kallo saboda sam ba shi da labarin tana cikin gidan su
"I really miss you" ta fad'a tana kokarin runguman sa,matsawa ya yi baya da sauri yana bin ta da kallon da ke da wuyar fassara
Cikin tsare gida ya ce"Why are you here?”
Rola idanuwan ta tayi tace" wannan wani irin tambaya ne Amin?"
Ganin ta sake nufo sa ya sa shi dakatar da ita da hannu yana sake fad'in" na ce miye kawo ki"
"Am s..."
Cikin tsawa ya katse ta da cewa"just answer me"
Kuka ta fashe mishi dashi tare da zubewa a kasa tana fad'in" bana son ana min tsawa bana so!"
Tsaki ya ja tare da shige wa cikin d'aki abin sa nan kuwa ta kara volume din kukan ta ganin ko rarrashin ta Bai yi ba
Mikewa ta yi tare bin sa d'aki cikin kuka, a zaune ta same sa akan gado ya dafa kan sa da alamun akwai abin da yake damun sa
"Kayi hakuri mijina!"
"Ba ni zaki bawa hakuri ba! Wa wannan mahaukacin zuciyan naki zaki bawa hakuri! Haba baby abin naki yayi yawa ai! Baki ganin zan iya hakura da ke akan wannan al'amarin?"
Check on my New book: SHUGABA
_Hey 👋 fans! Show me some love by following me on my Instagram *Mhizzphydo*_ I will really appreciate it if you do!.
_Vote, Comment & Share_
YOU ARE READING
ABAR SO
Random"ABAR SO!!!" Shine abinda NAFHIRA tace cikin siezing din breath, aikuwa arikice tajawo NAFHI kan cinyarta "Addua fah kawai zaki mana bah kuka bah, ganinan acikin abinda nafi tsana arayuwa ta (blood)wannan kawai yakara tabbatar min da babu wanda ya w...