💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*
WATTPAD: MHIZZPHYDO
🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟🌟G.W.F🌟
HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST
Wannan page din naki neh
Meemertjj, ina miki murnan gama book Allah yasa mu amfana da darasusukan dake cikin littafin Allah yakuma kara basira... Ina yinki irin over dinnan*Book 🅱️Page 1*
Nadhira batayi la'akari da cewan hospital sukeyi bah ta kurma wata iriyan wawaiyan ihu ai basu hankara bah suka jita akasa
Mumy kam mutuwan tsaye tayi sanadiyar hango big dady kwance akan gado
Su Maryam da Fatima ma kuka sukeyi kaman ba gobe
Dakyar aka fita dasu daga dakin while Nadhira aka dauko ta akan gado
Ward akayi da Nadhira inda su mumy suka mara musu baya cikin tashin hankali
Taimakon gaggawa aka shiga bawa Nadhira cikin sa'a kuwa ta farfado
Tana farfadowa tafara"Kukaini wajen big dady"
Allura aka tsikara mata nan da nan bacci ya kwashe ta sai uwar zufa dake tsatsafo mata akan goshi da hanci
"Zan iya magana dake hajiya?" Yatambaye ta ganin halin datake cikin
Gyada mishi kai kurum tayi tareda bin bayan shi aka bar su Maryam tareda Nadhira
Zama doctor yayi akan kujeran shi tareda nuna wa mumy wajen Zama da hannu
Zama tayi ita din mah, cire glass din idonshi yayi gyaran murya yayi yace" sannu Hajiya , wato dazu neh aka kawo mijinki rai a hannun Allah sakamakon accident din da yayi"
Hawaye mumy ta share da gefen khimar tareda da Jan hanci tace" amma inace baiyi wani muni bah?"
"Maganan gaskiya hajiya saidai ayi hakuri amma kafarshi guda daya tasamu matsala sosai don haka sa hannun ki kawai muke bukata anan sai muyi mishi aiki"yafada tareda mika mata wani farin paper mai dauke da sunan hospital din
Cikin dauriya mumy tace" dole neh sai an mishi aiki neh??"
"Gaskiya yana bukatan aiki cos a halin yanzu sosai kafan zai na takura mishi"
"Kuna da kayan aikin neh anan ko za'ayi referring din mu?"
"Erh akwai kayan aiki kuma a halin yanzu akwai visiting doctor akasa"
Wata iriyan huce ta fesar sannan ta dauke biro tareda signing pepern da ya bata
Fita tayi daga cikin office din tayi ward dinda aka shiga da Nadhira
Har lokacin baccin wahala takeyi sai ajiyar zuciya mai karfi take saukewa akai akai...
Dishi dishi take kallon ceiling,waro idonta tayi dakyau cikin son sanin inda take
Nan kuwa ta tariyo abinda ya faru , gefen ta ta kalla ta hango su azaune jugum kowa yayi tagumi sun lula duniyar tunani
"Alhmdllh"ta furta ahankali tareda sakin wata munafukar murmushi na jin dadi
Saisaita kanta tayi kafin takira mumy ahankali
Dada matsawa sukayi kusa daita ahankali tace"ina big dady nah yake??"
Cikin jarumta mumy yace" aiki za'ayi mai zuwa anjima"
"Aiki!???"
"Erh wai kafarshi ya samu matsala"
Acikin zuciyarta tace"Masha Allah One done two more left" afili kuwa tashin hankali neh ya bayyana afuskarta tace"pls mumy kukaini naganshi"
Inspector Nasir dinda tin da tafarka yake kallon duka reactions dinta yakaraso gurin su yace"hajiya zaki iya kaita taganshi"
Tsarguwa tayi da irin kallon dayake mata wanda yasa takusa rasa nutsuwar ta amma kasancewan ta shu'uma yasa ta waske
Ganin yanda tasha mur yasashi shan mamaki tareda dora shakku akanta
Agefen gadon zauna bayan sun fita yace"wace ita??"
"ABAR SO kenan"Maryam tafada
"ABAR SO kuma??" Ya tambaya cikeda mamaki ganin hakan ba ainihin suna bane
"Mind her not sunan ta Nadhira but ana kiranta da either ABAR SO or Babynmu"
Gyada kai yayi yace" Allah sarki maybe itace auta ma naga yanda tashiga tashin hankali dalilin ciwon dadyn ku"
"No yar kanin dady muce ita mata dadyn ya rasu"
Kura musu ido yayi yace"haba dai??"
Ya mutsa fuska Fatima tayi tace"kwarai dagaske kuma bata Jima da dawowa gidan mu bah amma abin mamaki tinda tashigo abubuwa marasa dadi suke faru agidan mu"
Gyara zaman yayi akan gado alaman he's interested in hearing labarin su"bangane abubuwa marasa dadi bah?"
Ba bata lokaci maryam tafara zayyano mai abubuwan da suka faru"nikam in dady ya warke gaskiya zamu mishi magana akan yakoma gidan su
Dawowar su Nadhira neh yasa su yin shiru, ganin still wannan suspect look din nan nasamar fuskar Inspector Nasir yasa ta lumshe anime eyes nata wanda yayi daidai da gangarowan hawayen daga samar fuskan ta.
"Oh Babynmu kidaina kuka mana"mumy tafada daidai ta zaunar da ita daga inda Inspector Nasir ya tashi
Maimakon tayi shiru saita kara volume din kukanta tareda runtsa idonta dakyau
Ganin zakuwarta tayi yauwa yasa yace"Miyesa kike kuka? Pls kidaina kukan nan
Dago idonta tayi takalle shi wanda daman shine abinda takeson ji daga gareshi
Maganar ta sukaji tace" bangane miyesa nake kuka bah?? Kana nufin wannan ba abin kuka bane awajen ka?babana yan...
*Ina mana barka da Sallah in advance... Allah tlyasa muyi sallah lafiya*
*Vote,comment&share*
*Mhizzphydo*
YOU ARE READING
ABAR SO
Random"ABAR SO!!!" Shine abinda NAFHIRA tace cikin siezing din breath, aikuwa arikice tajawo NAFHI kan cinyarta "Addua fah kawai zaki mana bah kuka bah, ganinan acikin abinda nafi tsana arayuwa ta (blood)wannan kawai yakara tabbatar min da babu wanda ya w...