page 2

1.7K 79 1
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          
loadιng...........✍🏻

                 
        🌐 Zãn Rayu da kai
                      

Story_oum zahra
Written$edit__pheeymarrh
      MRS NOOUR
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me @pheeymarrh

بسم الله الرحمن الرحيم

3⃣➕4⃣

Ya dade kwance cikin bathtub yana tunanin hali irin na Nasreen a koyaushe gurin sanin hakkin da kulawa da d'a namiji yake bukata a zamantakewa na  aure sune abubuwan da bata daukesu da wani muhimmanci ba  abu dayane zakaga tana rawar jiki akai shine wurin biyan bukatar ta,,cije lips dinsa yayi tareda jan numfashi,,ya d'auki tsahon wasu mintunan kafin ya fito daga cikin bathdub din yayi wankan tsarki ya fito,,

Kallo daya yayi mata ya kauda kansa ransa a dan jagule har ya kai gaban mirrow saiya dawo ya karasa gaban gadon ya dan duka kadan tareda sanya hannu yana dan bubbuga bayanta alamun tashi,,

Da kyar ta iya bude idanunta cike da bacci tana jan tsaki da karfi baby lafiya kuwa ta fada cikin muryar bacci tana sake gyara kwanciya,,

Tashi maza kiyi wanka ya fada yana juyawa,,

Wani tsakin tasake saki da karfi ta mike ta dauki yar rigar baccin nata ta fice a dakin tana kunkuni,,

Sosai ransa ya baci amma bai nuna ba saima cigaba da sanya kayan sa dayayi yasan hakan ce zata faru bayason abunda zai bata masa rai don bazai iya kwana da ita ba batareda tayi wanka ba wanda yasan dama hakan bazai taba faruwa ba a gurin Nasreen din,,
jallabiya ce baka mai tsantsi ya fisa dan turare kadan jikinsa ya wuce wurin pmat dinsa yafara sallah,,

Seven am daidai dan karamin golden alarm clock dinsa yashiga bugawa sannu a hankali,ya dan jima yana kara kafin ya miko hannusa ya danna daya daga cikin madannan agogon wanda yasanya kidan dake fita ya tsaya,saida ya bata wasu yan sakwanni kafin ya yaye duvets din daya rufe har fuskar sa yana kallon daki,a hankali ya sauke kafarsa bisa laullasan rug din dake malale gefen gadon ya mike tareda shiga bathroom,,

Bai dauki wani dogon lokaci ba ya fito yayi shafansa tareda gyare kan nasa sets din wasu riga da wando sports wears ya dauko farare khal ya sanya ya fito ya sauka kasan benan maaikatan gidan sai mika gaisuwa sukeyi yayinda shikuma saidai kawai ya gyada kansa har yafice baitsaya bin takan Nasreen ba don yasan lokacin tashin ta baiyi ba yanzu,,

Nan ma harabar gidan gaisuwar cedai akai tayi masa suma din dai gyada musu kai kawai yakeyi,,

Tsaye ya tadda D'anbayero yana jiransa harya bude masa murfin motar ganin fitowar sa fara ce khal sai sheki takeyi kirar ferarre mai matukar kyau da tsada,,

dukawa yayi ya gaishesa kansa duke sai lokacin yayi motsa baki ya amsa a hankali labbansa ne kawai suka motsa banda sautin muryar sa zama yayi a gidan baya D'anbayero ya rufe murfin motar ya shiga gefen driver ,driver ya ja motar cikin nutsuwa suka nufi babban gate din dake gidan,,tareda Karin wasu motocin har guda biyu Bayan su ,,

Prince jaid gymnasium center suka nufo,,da sauri masu tsaron kofar suka wangale musu gate din suka shige suna mika gaisuwar su cikin girmamawa,,

★★★★★★★

Lumshe manyan fararen idanunta tayi a hankali na wasu seconni kafin ta bude su a kansa tana kallon kwayar idanunsa kamar yadda nasa suke kan nata kasa jurewa tayi da kallon nasa ta kauda kanta ga kallon shuke shuken dake wurin tana murmushi a hankali,,

ZAN RAYU DA KAIWhere stories live. Discover now