🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
_________________________*Gaisuwa gareki ƴar uwa raɓin jiki tun ana ƴan yara BARIRA BASHIR,OUM ZAHRA MRS ANGON SOYAYYA,Allah yabar ƙauna,yakawo ƙazantar ɗaki*😘
_________________________7⃣1⃣➕7⃣2⃣
duban Nasreen takeyi duba irin na anya kuwa kinsan abunda kikeyi,ba zagin ko tsawar ne ya ɓata ran Zahra ba illa yanayin yadda tayi maganar cikin tsananin ɗaga muryar da zai iya tadashi ko kara samishi ciwon kai juyawa tayi ta ɗora yatsun ta guda biyu gefen wuyan shi ta cire ta maida kanshi,
towel ɗin ta ɗora a saman goshin shi tana faɗin Allah yabaka lafiya a hankali tamkar mai raɗa shi kanshi baiji abunda ta faɗa ba kokaɗan,,Ɗagowa take koƙarin yi taji an fuzgota ta baya da karfi tayi baya gabaɗaya kiris ya rage ta faɗi, Allah ya taimaketa ta dafe hannuwanta a ƙasa kanta bai bugaba sai jikinta dake ƙasa,,
"banason hayaniya pretty please "
muryarshi ta katse Nasreen daga kokarin fara zazzagawa Zahra tijara kallonshi sukayi dukkansu har lokacin idanun shi rufe suke, miƙewa Zahra tayi tana kokarin barin ɗakin don batason abunda zai iya janyo mishi damuwa ko kaɗan ne,,
Da mugun kallo Nasreen ɗin tabita tana faɗin zan dawo gareki shigeya bacin Allah ya shigo dani ɗakin dakin ƙarasa kashe shi dama abun da ya shigo dake cikin rayuwar mu kenan ta karashe maganar tana zama gefen shi dago shi tayi ya jingina kaɗan da jikinta ta ɗauki mug ɗin ta kai bakinshi,,
Maiya farune pretty yayi tambayar batareda yasha coffee ɗinba,
cikinzafin rai ta soma faɗin daga na hado maka coffee na shiga ɗaki indawo na sameta tsaye kanka maiya kawota inba mugun nufiba cikin daren nan yarinya jinin mayu marar zuciya,,bayan son magana baya sonjin anayin maganar musamman yadda take maganar da karfi har cikin kwakwalwar kansa yakejin muryar ta,,
kyaleta kawai yayi don buɗe bakinma wahala yake yimishi saidai kanshi ya ɗaure yana mamakin yadda Nasreen ɗin zatayiwa Zahra ƙarya koda idanunshi a rufe suke he can feel her presence yadda ta tsaya kusa dashi yana iya jiyo kamshin jikinta sanyin ta dabanne wanda yakan sanyashi gane kusancin ta gareshi sosai,,
a hankali ya bude bakinshi wanda yake rawa sosai ya kurbi coffe ɗin ya lumshe idanu tabbas Zahra ce amma maiyasa Nasreen ke kokarin yi mata sharri haka,tass ya shanye saboda yunwar dayake ji dukda zafi da ƙaiƙayin dayakeji a maƙoshin shi,,
yanason yin wanka da ruwa mai zafi sosai amma dole ya hakura ya kwanta ɗin don yasan indai ba kusantar Nasreen ɗin yayi ba bazata taɓa iya yimasa wanna aikin ba haka ta koma ta kwanta batareda bashi magani ba, ta cigaba da baccin ta bayan ta matsa chan gefe daban,shima baijima ba baccin yayi gaba dashi dukda har lokacin zazzabin ma gaba yayi babu sauki,,
Jiki ta a sanyaye ta koma ɗaki tayi zugum akan gado hannunta tallabe da kumatunta gabaɗaya ta shiga damuwa duk wata gajiya datakejin tanajinta a jikinta ta ƙaru sosai,
har cikin zuciyarta take jin inama itace ɗin zazzabin ya kamata ta,ta juma zaune rai a jagule kafin ta mike ta nufi bathroom ta ɗauro alwarla ta fito, doguwar riga ta sanya ta wuce kan praying mat ɗinta ta soma nafilfilu don batajin zata iya komawa bacci kuma addu'ar ta ɗaya itace Allah yasa Nasreen takula dashi ku koma yatashi garau babu wani sauran ciwo ataredashi,,
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi