end

2.3K 81 6
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          
loadιng...........✍🏻

                 
        🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
                      

Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
      *MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*

بسم الله الرحمن الرحيم

1⃣0⃣0⃣
🔚🔚🔚

Komawa yayi ya zauna kan kujera tare da harɗe kafa ɗaya kan ɗaya yana kallon mom ɗin yadda take kicikicin ɗagata ranshi na kuma ɓaci wallahi ba'ayi macen dazata zageshi yyi hakuri ba balle harta yiwa uwarshi rashin mutinci ba,gaba ɗaya sai yaji yana danasanin auren ta,shi kwatakwata ma baiyi burin auren macen dayayi tarayya da ita before marriage ba yaso inyagama varikin shi yanemi yarinya ƙarama nitsattsiya ya aure,lallai amjad kayi kokari da hakuri da wurin jure zama da Nasreen"Mahfuz yaketa saƙa hakan cikin ziciyar shi(ya manta dacewa faɗar ubangiji mazinaci baya auren wata mata face mazinaciya ƴar uwarsa,don haka writers mu gyara mu daina ƙaryata faɗar ubangiji,muna faɗin tantiriyar ƙaruwa tazo ta auri natsattsi wanda bai taɓa sanin ƴa mace ba kuma harya zauna da ita zama na har abada cikin soyayya da ƙauna,muna kokarin nuna cewar hakan yanada kyau ayi bariki sannan yarinya ta samu mijin daya kasance abun alfahari da ba kowacce nutsattsiya zata iya samun shiba,wannna zancen babu faɗakarwa cikinsa sai dai nishaɗantawar kawai,Allah kasa mu dace🤲🏻)
Wayar mom ɗince tayi ƙara da sauri ta ɗauka tana faɗin shigo ciki,wanda ko bata faɗaba mahfuz yasan likitan ne ya ƙaraso,saida ta nuna mashi bacin ranta kafin yaɗauketa daga ƙasa ya kaita bedroom ya kwantar ya fito dukda jinin dake fita daga kanta da bakinta bai sanyashi jin tausayin taba ko ƙaɗan cikin zuciyarshi,,

Mom ɗin da kanta tayiwa doctor jagora har ɗakin sanna ta fito ta samu wuri ta zauna kusa dashi tana dubanshi na wasu ƴan mintuna kafin ta soma faɗin"sam banyi mamaki da faruwar haka daga gareku ba saidai van tsammaci zuwan hakan da wuri ba,yanzu kai mahfuz har zaka iya auren matar aminin ka da kuka taso tare har zaka iya cin amanar shi mahfuz bayan kasan yana sonta tana sonshi saboda tsautsayi daya faɗa kanshi wanda zai iya samunka kaima ta gujeka,wallahi ka ɓata wayonka duk abubuwan da kuka aikatan tun tana da aure babu wanda ban samu labarinshi ba don haka ka gaggauta samun shi ka nemi gafararshi data ubangiji ka yaye wa kanka wannan masifar ta neman ƴaƴa mutane wanda kanada halin auren huɗu ba balle ɗaya cikin su kuwa dole zaka iya samun wacce zaka samu nutsuwa da ita ɗari bisa ɗari,wallahi mahfuz kaji tsoron Allah duniya gudu takeyi fiye da yadda kakae tunnin akoyaushe ina tunasar da kai hakan amma kana watsi da zanccen na bayan kai yakamata kayiwa mutane wannan nasihar duba da abunda ya samu abokin ka cikim ƙanƙanin lokaci"
Ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kai ganin yadda zancen nata bata ga alamun yana shigarsaba"shikenan dama ni bawannan ya kawonin ba abunda ya kawoni shine maganar aure,Aure bakeso ka ƙara "ba ƙaramin girgiza shi zancen ta yayi ba kallonta yakeyi cikeda mamaki a iya lissafin shi baifi wata biyu da sati ɗaya dayin auren shiba sannan har take maganar ya ƙara aure,
Jinjina kai tayi tana faɗin "yes aure zakayi dole don wallahi vazan zauna da yarinyar nan ba ita kadaini da kaina zan nema maka mata ƴarinya ƙarama wacce ruɗin duniya baya kanta tazo ta haifin jikoki ba wacce nasan zaman dazatayi da kaiba ce don haka ka shirya sake ƙara aure cikin watanni uku masu zuwa,abunda yasa har na gaya maka shine don hakkin kane amma bawai don beman shawarar ka ba don haka saika sanar da matar taka inta samu lafoy,ni kaga tafoya ta saimunyi waya"harta ɗauki jakarta ta rayata ta fice bai iya cewa komai ba,kwantar da bayanshi yayi kan kujera yana rufe idanun shi,

Yana nan zaune har likitan ya fito ya shaida masa ya gama tasamu bacci yanzu yaso yayi mashi nasiha akan halin da matarsa take ciki,amma ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga mashi hannu sama,kafin ya sauke yana nuna mashi ƙofar fita,doke ya juya ya fice yana mamakin hali irin na ƴaƴan masu dashi,ana barci ya ɗaukeshi yana saƙawa da warwara yadda zai yi maganin Nasreen.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 10, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ZAN RAYU DA KAIWhere stories live. Discover now