🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
7⃣7⃣➕7⃣8⃣
Babu yadda Ammy batayi magiya da ban hakuri ba amma daddy yakafe sam akan hukuncin shi karshe ma sai abin yaso ya koma kanta akan daddyn yana ganin kamar saken datake yiwa Amjad da Nasreen ɗinne ya sanyashi bijerewa maganar shi,
haka ta mike fa koma ɗaki rai ajagule,tabbas tasan tanada laifi akan ratuwar amjad ɗin musamman ma ga Nasreen saidai abunda daddy bai gane ba shifa ɗan yau zafi da hargagi baya kwantar dashi akoyaushe cikin yi musu addu take baga taɓa gazawa ko gajiyawa ba maiyasa zai yanke wanna hukuncin mai tsauri wanda take ganin tamkar ita ya yankemawa batajin zata iya jure rashin jin ɗanta koda a waya ne,
sai yanzu take danasanin gayama daddyn abunda yafaru ta gwammace ace da ɗan bayero gakirata ya gayamata bata faɗa mishi ba har saitaje ta duba shi amma babu yadda ta iya bata da ikon dawo da hannun agogo baya,,Ranar kam babu wanda ya iya bacci cikakke cikinsu musamman Ammyn kwana tayi kan sallaya tana roƙon ubangiji ya sauƙaƙa abun haka daddyn ma duk yadda ya hasala ranshi ya bacii saigashi ya ƙasa baccin shima dole ya miƙe ya yo alwalar ya soma roƙon ubangiji akan samun lafiyar su,
Afnan ma ta daɗe tana nafilfilun da roƙon ubangiji akan lafiyar bro ɗinta da Zahra,,Sai ƙarfe goma na safe ta yi juyi da ƙyar tana buɗe idanun ta dasuka kumbura sukayi jajur farar fuskarnan tata tayi jajur saboda kuka, kallon gefen dayake kwanciya tayi hawaye ne suka taro idanunta ta mike da sauri ta daɗa toilet tayo wanka tareda alwalar ta fito kai tsaye wurin mirro tawuce tayi shafa ta sanya powder da light janbaki a bakinta ta nufi drower ta fito da kayan ga sanya doguwr budadɗiyar riga ce ta material yard wacce ta kama ta daga sama,iyakarta ƙasan gwiwar ta tagaba tabaya kuma ta sauka har ƙasa tana jaa kaɗan,open net top ta ɗaura akan rigar datafi ƙasan kirjinta ba ta sanya hula wacce ta kama gashin dokin dake kanta dashi duka ta feshe jikinta da turare,
sannan ta sanya hijab dogo har ƙasa tayo sallar asubahi cikin yan mintuna ta idar jakarta taɗauka da gyalenta ƙarami datayi rolling a kanta ta fita cikin sauri ta shiga motarta saida ta tsaya wani wurin abinci ta siya bugger da coffee ta koma mota ta soma ci don yunwa takeji sosai rabonta da abinci tun cake ɗin da amjad ya sanya mata a baki,saida ta cinye duka sannan ta kama hanyar asibitin,,Bata sami damar ganin shiba saboda likitocin dake kanshi suna sake dubashi,
ta kusan three hours zaune kafin suka fito offince ɗin likitan ta sake komawa yayi mata bayanin an samu cigaba alhamdulillah kanshi lafiya lau hakama karayar angyarata kuma suna saka ran andace saidai bayanshi anan matsalar taje wato ƙashin mahaɗar kugunshi saudai zasuyi iya kokarinsu akai,
godiya sosai tayi ma likitan cikie da kwarin gwiwa ta fito zata tafi sai kuma ta tuna da zahra tamkar zata koma ta tambaya sai kuma ta fasa tana fatan Allah yasa ta mutu kowama ya huta,Motarta tashiga tana sake ƙara gwara kiran layin MG ɗinsu karo na ba adadi hartayi ƙarar ta gama bai ɗauka ba dole ta nufi wurin aikinsu,,
tun kafin ta ƙarasa ciki ta tambaya ko MG ɗin yana nan akace baizoba ma ɗan jimm tayi kafin ta shiga motarta ta wuce gidan shi kaitsaye,,knocking tayi sau biyu aka buɗe kofar sanye yake da singlet da ƙaramin boxes iya cinyarshi bata hanya yayi ta shiga batareda wata damuwa da yanayin dayake ba,
a ɗaya daga cikin kujerun parlon ta zauna ya ƙaraso ya zauna kusada budurwarshi dake kwance kan kujera itama da ƴar singlet da ƙaramin boomshort,
gaisawa sukayi tana mishi ya jiki da bada hakuri,
murmushi yayi yana faɗin babu komai, komai ya wuce ai ya miƙe ya zobo mata juice haɗe da sirkin giya a ciki ya kawo mata yana binta da wani mayatacen kallo, amsa tayi tana mishi godiya ta ɗan kurɓa ƙadan ta ajiye suka cigaba da tattaunawa akan aikinsu,,
ta jima a gidan kafin ta tafi gida tunda ta shiga ta kwanta a anan parlon ƙasan wani bacci mai nauyi ne yayi gaba da ita,,
VOCÊ ESTÁ LENDO
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi