🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
*wayyo sister comments ɗinku da adduoe na sanyani jin daɗi sosai fiye da yadda kuke tunani,ina matuƙar godiya ga masoyana aduk inda kuke,Allah yabar ƙauna,sone na fisabi lillah💯❤*
*wai mai kuke nufi ne da Nasreen eyeeh,gabaɗaya kun haɗe mata kai fans guda uku kawai😭,gaskiya bakuyi mata adalci ba,da sannu zatayi maganinku in mijinta ya warke🤺*
*Dedicated to all muslim sisters masoyan Annabi,*🤝🏻
8⃣7⃣➕8⃣8⃣
Kukanta ne ya cika ɗakin wanda tun tanayin shi haryaci ƙarfinta a ƙaramin dukan kirjinta maganar tayi ba sallati kawai takeyi tana kiran sunan Allah lokaci ɗaya tana neman fita hayyacin ta,hakuri doctor ɗin yasoma bata don bashida abunda zai gaya masu duk wani kokari sunyi shi amma basuda yadda zasuyi,,
Nasreen kam baƙin cikin kukan da Zahra keyi ya hasala ta maiye abun kukan a wirin Zahra ko ita batayi ba batajin kukan ai zai iya bashi lafiya tunda magana ta ƙare miƙewa tayi tana kuka sosai tabar office ɗin kai tsaye motar ta ta shiga ta wuce masaukin su ba tare da wata damuwa ba ta wuce ɗakinta,
su mom basa nan don haka ta wuce ɗakinta tayo wanka ta kwanta akan makeken gadon ɗakin hankalin ta kwance don tana shiga mota tadaina kukan,,tunanin Mahfuz ta somayi yadda yaso rungumeta ɗazu ya sanyata jin tsannin sha'awar datake dannewa tsahon lakacin da batada miji,
da kyar ta iya daurewa batareda ya samu abunda yakeso daga garetaba don kon hannunta daya riƙe saida tayi mashi warning mai tsauri,amma yanzu gaskiya bazata taɓa iya wanna zaman ba domin bazata iya riƙe kanta ba,juyi tayi tana shafa cikin ta a hankali take shafa cikinta tana faɗin
"kayi hakuri babyna dole mom ɗinka zata rabu dakai wanna shine gatan kawai da zanyi maka but your mommy loves you so much"
rintse idanun ta tayi tana tunanin yanayin tsari da kyau irin na Mahfuz duk da bai ko kama ƙafar Amjad ɗinta ba,amma yana da kuɗi da gata kuma ga iya wanka shima sosai,a haka har bacci ya ɗauke ta.Zahra kam tashiga wanin hali na tashin hankali tsantsar tausayin ya sanyata shiga wani hali,mikewa tayi tsaye da ƙyar tanajin zuciyarta tamkar an daure mata ita tafiya ɗaya biyu ta ji numfashin ta na sama wani irin jiri taji yana ɗibar ta nan take ta tafi luuu ta faɗi kan kujerar dake bayanta,
Sai lokacin doctor da su Aj suka ankara da ita da sauri doctor ya danna wani wuri a jikin table ɗinshi tamkar bottom yana ƙarasawa inda take koƙarin dagota Mahfouz yakeyi cikin sauri Aj ya dakatar dashi ta hanyar riƙe hannunshi daidai lokacin kuma wasu nurses guda biyu suka shigo a guje don haka Aj saiya soma tafiya hannun shi riƙe dana Mahfuz wanda duk kunya ta kamashi suka fita daga office ɗin suka zauna kan fararen kujerun dake jere ta wajen ƙofar ɗakin,,taimakon gaggawa suka soma bata cikin kwarewa dayake Allah manya taimaka yasan kan problem ɗinta,sun jima kafin suka samu numfashin ta ya dawo normal bugum zuciyar ta ya daidai ta saidai jinita daya hau sosai lokaci ɗaya,Allaurar vacci sukayi mata aka ɗorata akan wani gadon na marasa lafiya aka fito da ita zuwa rest room daban duk anan hawan yake,
Aj ne ya tashi ya shiga wurin likotan don jin abunda ya sameta yayin da shi kuwa Mahfuz dama yake nema na barin asibitin nan take ya miƙe ya wuce ya shige motar dasuka zo da ita dayake tashi ce ya wuce hotel ɗin dasuka sauka,
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi