🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
5⃣7⃣➕5⃣8⃣
Jin ƙarar horn na motocin ya sanya Afnan mikewa a zabure ta kwaso tanufo waje Ammyn ma miƙewa tayi cike da ɗokin ganin nasu ko Allah zaisa tayi gani mai kyauta nufi waje a dai dai baƙin kofar parlon ta tsaya jiran ƙarasowar su,Afnan kuwa har parking lots ta karasa cikin gudu da tsananin murna da kanta ta buɗe motar dasuke ciki ɓata fuska tayi ƙadan tana zavgawa Nasreen harara dube duben motar ta somayi yayinda shikuma Amjad ɗin ya zuba mata ido cikeda mamakin yadda ta nuna batayi murnan ganin shiba ma balle Nasreen da dama lallaɓawa sukeyi,,
Nan take hawaye ya soma cika idanunta cikeda shagwaɓa ta kyaɓe baki tace bro where is she,,
Kallon ta yakeyi cike da mamaki dama duk wannan ɗokin na Zahra ne tsaki yayi ya soma kokarin fitowa hannunsa rikeda na Nasreen suka raɓata suka wuce ko kallon arziƙi bata samu ba wurin Nasreen,
Wani irin baƙin cikine ya lullube zuciyarta wanda ya sanyata fara zubda hawaye jin an dafata a kafaɗa ta baya ya sanyata juyowa tana kallon ta wani irin ihu ta saki cikin tsalle ta faɗa jikinta ta rungume cikin tsananin murna,ihun nata ne ya sanyasu tsayawa suga waigo suna kallonsu tsaki Nasreen tayi tana han hannun Amjad ɗin zuwa ciki shikuwa tsananin mamakin irin wannan murnar yakeyi tamkar waɗanda suke ƴan uwa waɗamda suka daɗe basuga juna ba,,Da sauri Afnan taja baya tana kura mata idanu murmushi Zahra ta sakar mata cikin ƙarfin hali hannu Afnan taɗora bisa wuyanta tsananin zafin dataji ya sanyata riko hannunta ta matsa da sauri ta riko gefen jikinta ta soma jera mata sannu,
Aikuwa taji daɗin hakan datayi mata don dama tunanin ta ɗaya kar Ammyn ta fahimci halin datake ciki haka ta tattaro duk wani ragowar karfi da dakiyarta ta soma takawa cikin son daidaita tafiyarta wanda hakan datakeyi takejin tsananin raɗadi da azaba har cikin kwakwalwar kanta,,a haka suka karaso wurinsu Ammyn dasuke tsaye tana jiran karasowar su yanayin yadda taga rikon da Afnan tayi mata ya sanya gaban tafaɗuwa ta kurawa Zahra idanu cikin son gano meke faruwa amma dayake da duhu bata iya ganin kwayar idanunta saidai tafiyar datakeyi da kyar wani irin kallo ta watso wa Amjad ɗin me cike da tuhuma da tsananin bacin rai babu shiri yayi ƙasa da kansa yana kokarin raɓata ya wuce itama gaba tayi ta ƙarasa wurinsu tana riƙo ɗaya hannun Zahra zafi taji zau a hannu wanda ya sanyata rikicewa ta soma yi mata sannu tareda amsar riƙon daga Afnan ta rungumo Zahra jikinta zuwa kan kijerar parlon ta zauna da ita tace maza ta kwanta,,
Ko kallon inda suke batasakeyi ba ta mike ta nufi kitchen ta hado mata tea mai kauri ta dawo ta taimaka mata tamike zaune taso bata abaki amma Zahra ta hana ta amsa hannunta na ɗan rawa saboda zazzabi a hankali ta soma kurba don yunwa takeji sosai tun karin safe gashi har isha'i tayi ta sha kusan rabi kafin ta soma kokarin ajiye kofin da sauri ammyn ta karɓa tana mata sannu maganin zazzabi da Afnan ta kawo ta balle ta miƙa mata ta shanye da ruwan tea ta koma da baya ta jingina da jikinta da kujerar tana lumshe idanu cikin tsananin ciwo,,
kaita ɗakina yanzunnan "ammyn ta faɗa tana mikewa tayi gaba babu yadda ya iya dole ya mike ya isa gaban Zahra ya kamo hannunta ya ɗora bisa kafaɗarshi ya sunkuya ya ɗaukota ya rungumo da jikinta a hankali ya lumshe idanun yana jin wani irin shock tun daga tsakar kansa har zuwa tafin kafarsa cije lebe yayi ya soma takawa ya wuce Nasreen dake zaune tamkar zata haɗiye zuciya ta mutu shikuwa yadda yakejin tsananin zafin jikin nata yana shigar sa ya sanyashi tsunduma cikin tunanin batareda ya tuna da zaman Nasreen ɗinba harya haura sama,,
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi