Zan Rayu Da kai

1.3K 61 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          
loadιng...........✍🏻

                 
        🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
                      

Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
      *MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*

بسم الله الرحمن الرحيم

6⃣3⃣➕6⃣4⃣

"har kinkai matsayin da zan hana kiyi mai kike ɗaukar kanki ne ko kuwa don kin gwada taki rashin tarbiyyar kwananki na ɗaga miki ƙafa batareda ɗaukar mataki ba kar ki ɗauki hakan ki ɗin wata ce ko kinada wani daraja ko ƙima ne wannan ya zama na karshe da zan ƙara cin karo da wannan abubuwan a matsayin binci na,,ya faɗa cikin ɗaga murya tamkar zai daketa,,
tunda y fara maganar bata ɗagoba dukda tsananin zafin datakeji na abinci har saida taji yahi shiru kuma cikin maganarsa na karshe ta fahimci abunda tayi wanda ya sanya zuciyarta yin sanyi take taji gabaɗaya haushin kanta ya zo mata a hankali ta buɗe baki tace don Allah kayi hakuri banida sanin bakason kalar wannan abinci…

Katse ta yayi jikinsa har yana rawa tamkar zai kai mata nushi yana bibbuɗe idanu yace are you trying to say pretty zatayi miki ƙaryane ko kuwa isƙanci ne da rashin tarbiyyar ne kiƙe takamar nuna wa mutane,,
kanta ne ya kulle da maganar sa gabaɗaya bata fahimci abunda yake nufi ba amma haka ta daure ta ba bashi hakuri muryar ta na rawa cike da tsoron yanayin sa,,

Hannu ya ɗaga mata alamun baya buƙata ya jiya ya wuce sama batareda ya tsaya sauraron taba kallo tabi bayanshi dashi har ya shige sai alokacin wasu zafafan hawaye suka soma zubo mata maiyasanya a matsayinta na matarsa ta kasa gane abunda mijinta bayaso anya kuwa soyayyar data ikrari agareshi bata samu rauni ba kuwa,
dariyar da Nasreen takeyi ne ya sanya ta ɗagowa tana kallonta cikeda mamakin dariyar datakeyi wani irin juyi tayo cike da jin daɗin ta samu nasara ta watsso mata kallon sama da kasa ciken kyaɓe fuska a wulaƙance ta wuce sama dukda taso ya wanwanketa da mari amma babu laifi hakan ma yasata jin ɗadin nangaba zatayi abunda zaiyi mata fiyeda marin,,

ta jima a wurin tsaye batareda ta iya motsawa ba tana aikin tunanin da kuka chan kuma ta ɗago tana duvan agogo goma da kwata lissafin lokaci ta somayi cikin sauri sauri ta nufi kitchen Allah yasa tana xa nuƙakkun kayan miya data ajiye na gobe Allah yasa kuma bai fara ƙankara ba da sauri ta ɗiba daidai yadda zata yi amfani dashi ta kunna gas ta dafa masa couscos jelof cikin yan mintuna ta zuba a plate ta sanya spoon ta ɗauko wani plate ɗin ta rufe ta ɗora a ɗan madaidaicin tray fa nufi sama kirjinta na bugawa don batason ganin wa idanunta ko sauraron abunda zai iya tarwatsa zuciyar ta jimm tayi a vakin kofar vedroom ɗinsa tana sake sake harta juya zata koma sai kuma fa kasa tayo tsayi don tasani ita kanta bazata iya runtsawa ba cikin kwanciyar hankali hardai bai ci abinci bataso tasanadiyyar taya kasance ya kwana da yunwa dukda batada tabbacin yayi azumin arfa davarace ta faɗo mata cikin sauri ta nufi gaban tv stand ta janyo drower dake jiki ta ɗauko pen da yar paper ta yaga tayi rubutu layi biyu ajiki ta koma ta ɗaura takarda akan tray ɗin taɗauka ta ajiye bakin ƙofar ɗakin knocking tayi da ɗan ƙarfi har sau biyu,tamkar baza'a amsa ba saikuma taji yace waye sake knocking tayi da karfi batareda tace komai ba ta juyada gudu ta sauka ƙasa,,,

Bude kofar yayi a fusace amma yaga wayam babu koya sosai ransa ya baci don yasan su uku ne cikin gidan nan gashi ga Nasreen kuma Zahra ce kenan kwafa yayi yana shirin juyawa yaga tray ɗin a ɗan gefen kofa ta ajiye,saida yayi jim na wasu saconni kafin yaɗuka ya ɗauki takardar dake kai ya soma karantawa kamar haka,,

_Ɗan adam ajizi ne baya wuce yin kuskure ka yafemin laifin danayi bisa kuskure batareda nasan hakan zai bata rankaba_

Maimata abunda kd jiki ga soma yi tamkar mai bitar karatu mai take nufi da hakan tana nufin batasan bayaso bane ko kuwa Nasreen ɗinsa ce zataiya mata karya harda shi,,

ZAN RAYU DA KAIWhere stories live. Discover now