Zan Rayu Da Kai

1.1K 70 13
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          
loadιng...........✍🏻

                 
        🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
                      

Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
      *MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*

بسم الله الرحمن الرحيم

*Maman ƴarso🥰*
*Habeeba muhammad🥰* *wannanpage ɗin nakune inajin daɗin comments ɗinku akoyaushe Allah yabar ƙauna*🤝🏻

*saƙon gaisuwa gareku masoyana aduk inda kuke mrs Noour nayi daku,ana mugun tare*🥰🤗

5⃣5⃣➕5⃣6⃣

Da sauri ya dawo cikin ɗakin ya wuce bathroom ya kunna ruwa ya daidaita zafinsa a cikin bath ya fito ya wuce sama zuwa ɗakinsa cikin gaggawa ya watsa ruwa jikinshi ya fito ya maida jallabiyar sa yana kokarin fita Nasreen na shigowa ɗakin kowanne cikin mamaki yake duban ɗanuwansa duk da bata kawo komai aranta ba amma tayi matukar mamakin ganinsa ido biyu duba da yadda yawani firgita da daburcewa da ganinta bata amsa mishi tamabayar dayayi mata ba na lafiya kuwa,,

saima karasowa tayo gareshi ta faɗa jikinsa tana faɗin na kasa bacci pjaid na kasa bacci wallahi duk dalilin waccen yarinyar mafarki mai muni nayi akanmu ta karashe tana fashewa da kuka,,

Babu yadda ya iya dole ya rungumeta shima yanajin tsantsar nauyi da kunyarta akan saɓa alkawarin daya ɗaukar mata tabbas inhar ta gane ya kusanci zahra lallai akwai babban rikici agareshi ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi wanda ya sanyata ɗagoda fuskarta tana kallon ƙwayar idanunshi,,

Kauda kansa yayi ya jata zuwa kan gado ya kwantar da ita shima ya kwanta yana kara rungumeta a jikinshi hannunsa ɗaya kuma yana ɗan tapping din bayanta alamun rarrashi lumshe idanunsa yayi yana tuno lokacin daya ke kusantar zahra lallai ya yarda mata iri iri ne kodan itaɗin tana da cika daƙirar daya bukata ga mace ne shiyasanyashi jin banbancinsu da Nasreen,
a furgice ya ɗago zai tashi tunowa da halin daya bar Zahra,yadda ya mike a firgicen ya sanya Nasreen bude idanu dyake itama bacci bai ɗauke taba dubansa take yi cike da mamaki da tamvaya,,
Babu yadda ya iya dole ya fuske yana kashe lamp din dake kan bedside drawer ya koma ya kwanta kirjinsa na dukan da karfi tabbas yasan Zahra tana bukatar taimakonsa amma kuma bayason abunda zai haifar masa da matsala a zaman su da Nasreen din tunda Zaman Zahra na ɗan lokaci ne runtse idanu yayi gabaɗaya ya rasa natsuwar sa saiyaji yana danasanin kusantarta don yadda yakejin kin taimakamata yafi masa raɗaɗi da ciwo a zuciya fiyeda magagannun data gasa masa ɗazu,,

Duk iya yadda yaso Nasreen ta yo bacci ya koma ƙi tayi domin harga Allah bacci ya gagareta data fara runtsawa mafarkin ɗayane take yi na ganin Amjad dinta da Zahra harda ƴaƴa biyu masu matukar kyau da kama da Amjad ɗin suna cikin labbu hankalinsu kwance suna hutawa,,wannan mafarkin ne yafi komai ɗaga hankalinta arayuwa duk yadda taso tayi bacci kasawa tayi haka sukayi shiru kowa najiyo motsin kowa wanda ya nuna da alamu duk sun kasa runtsawa kowa d tunanin dayake yi,,

Tun tana kallon kofa tana zuba idanun ganinsa har baccin wahala yayi awon gaba da ita tana iya jiyo karar ruwan daya cika yake zuba daga bathdub din babu halin mikewa hartayi baccin,,

Cikin dare fitsari ya matse ta babu arziki ta farka tana motsa jikinta wata irin azaba da raɗaɗi taji sun ziyarci kwakwalwar kanta gabaɗaya ƙasanta ya dauki zafi da kyar ta iya dago saman jikinta tana kokarin zaman amma ta kasa jin wani irin nauyi a mararta runtse idanu tayi da iyakacin ƙarfinta cikin matukar dauriya da jarumta ta ruko ƙafarta ta sauke kasan gado ta kamo ɗayar ma ta sauke ta ɗauki tsahon lokaci kafin ta samu tayi dabarar mikewa tsaye jinkinta na rawa gabaday saboda zafin miƙin ciwo duk yadda taso taga ta taka kasawa tayi dole ta koma ta zauna bakin gadon ta dan huta kafin tunanin jan jiki ya zomata sauka kasa tayi cikin lallabawa ta soma jan jikinta a hankali har zuwa cikin bathroom din,,

ZAN RAYU DA KAIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora