PAGE 75+76

1K 50 1
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          
loadιng...........✍🏻

                 
        🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
                      

Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
      *MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*

بسم الله الرحمن الرحيم

*Har ƙarshe ɗedicated to u my ukteey karkiyi fushi da hakurin Zahra🥺*
_love u so much oum sultan_🤩

7⃣5⃣➕7⃣6⃣

Shiru yayi yana dubanta cikin kwayar idanunta  cikin tsananin mamakin abunda ta faɗa ɗin tabbas abunda yagani ɗin kenan,ji yayi zuciyarshi ta yi rauni damuwa da baƙin cikin da ke cikin kwayar idanun nata sun sanyashi shiga wani hali wanda shi kanshi bazai iya faɗin wani hali bane yana daijin zuciyar shi tamkar zata tarwatse ga tsananin bugu takeyi mashi cikin sauri da karfi,

Lumshe idanun yayi cikin rashin sanin abunyi ganin haka ya sanya Nasreen kamo ɗaya hannunshi cikin nata cikin ƙarfafa shi,a hanakli ya buɗe idanunshi akan Nasreen ɗin yana kallonta kai ta jinjina mishi cikin lumshe nata idanun,
tana kallon sanda ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ya ɗaga speker ga bakinsa tareda lumshe idanun sa ya soma waƙa cikin sanyi jiki da zuciya harda muryar,,

Da sauri Zahra ta ɗago kanta data duƙar tana kuka kallonsa take cikin ƙunar rai da tsananin tausayinsa wasu zafafan hawaye ni suka soma biyo ƙuncinta zuciyarta zafi take mata tamkar ana ruru wuta a ciki,,

Murmushi Nasree tayi maikamada naci nasara,don ta riga ta gama cika bakin zaiyin dukda Zahra taso kawo matsala amma alhamdullilah yanzu zata tantace itace rayuwar shi domin kuwa tariga tagama karantar yanayi da idanun Zahra son Amjad ɗinta takeyi,shiyasa tayi Alƙawarin komai rintse saita var gidan cikin ƙanƙanin lokaci ko kuwa ta sanyawa zuciyarta bakincikin dazai sanyata bugawa ta mutu,
hannun Nasreen ta sanya ta sakalo nashi hannun cikin tsananin farin ciki yadda tage gano tsantsar bakinciki a idanun Zahra ga kuma guest ɗinta yadda suke ta tafa musu tasan ta wuce raini yanzu ta gama yardarwa zuciyarta itace rayuwar Amjad,Amjad nata ne babu wata wacce zata iya rabasu komai abunda ta taka kuwa,,

Zame hannun sa yayi daga na Zahra ya rungume Nasreen a jikin shi zafafan kalamai na soyayya dayake rero mata a waƙa ya sanya Zahra miƙewa daga ɗurkushen datake ta fice daga wurin dagudu saboda kukan daya taho mata mai karfi,saida takai wurin da motar su take sanna ta zube a ƙasa tana dafe da zuciyarta kuka take sosai tamkar ranta zai fita kusan minti huɗu tana haka kafin ta somarage kukan dayaki raguwan saima ƙarawu da ƙarfi ta soma faɗin"maiyasa zuciyata zakiyi min haka?wane laifi nayi nake fuskantar wannna jarabawar haka?
maiyasa Amjad zaka kasance wanda baya tausayi?maiyasa zaka ɓata mana rayuwa maiyasa,"
hannunta ta ɗaga sama tana matsanancin kuka take faɗin "ya Allah kaikace mu roƙeka kaiɗin maji roƙon bawa ne ban gazaba ban kuma gajiya ba bazan kuma rage ko dainawa ba amma ayau ina roƙon ka ya ubangiji la yaye min ƙaunar wannan bawan naka a raina ko da ƙadan ne,ya Allab ka kawo min ƙarshen wanna damuwar da baƙin ciki kafin ya zamto ajalina"

hannun ta zameyi zuwa ƙasa bata damuba da komaiye a wurin ta kwanta tareda dafe saitin kirjinta ta haɗe jikinta wuri ɗaya tana cigaba da kukan sosai batareda damuwar kowani zaizo wurin ba,daga inda take tana iga jiyo sautin muryar sa wanda ke ƙara sanyata higa damuwa da hana kukan nat tsayawa,

Ta dade a hakan kwance wurin taji an dafa mata kafaɗa da sauri ta buɗe idanunta dasuke mata zafi da raɗadi tana dubanshi cikin tsoro taja baya tana tire hannunshi daga jikinta,,

ZAN RAYU DA KAIWhere stories live. Discover now