🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
*Dole in jinjina muku👍🏻oum Safwan*🥰
*momy paki 🥰*
*domin kuwa comments dinku dabanne ina matukar jin dadin adduoe inku,ana mugun tare*🤝🏻😘3⃣3⃣➕3⃣4⃣
Haka ga bangaren Zahra sosai suke gudanar da shirinsu na biki dukda walima kawai zasuyi Bayan gama daurin aure,,
Kallo daya zakayi mata ka tabbatar da ita din amarya ce domin kuwa ciki da waje tasha gyara sosi fatar jikinta tayi tsantsi hade da sulbi sai kyalli takeyi har wani irin haske takara ga magungunan gyara datake sha kullum babu fashi na inserting ne kawai ba'a taba bata ba saboda batada bukatar hakan sai tsarki da ruwan dumi akoyaushe datakeyi,
butar ta daban ce inna mariyar ta ajiye mata,,Sosai yadda yake nuna mata halin ko inkulan yake damunta amma da yake soyayyarsa mai karfi ce a jinin ta take, shiya sanya akoyaushe take masa uzuri,,
Koda Aisha ta yi mata maganar akan tsoronta da lamarin Amjad din da auren kansa kada ace da wata manufa suka shirya auren,,
saita nuna babu komai zai chanza wataranan kuma ita dai zata cigaba da hakuri tareda addu'a,,Abdul majid (wato aj don mutane na rikicewa da dukarsa a Amjad saboda haka da sunan shi zamu cigaba da using)Abdulmajid dinne ma ya ke kiransu akan abunda zasu bukata ita kuwa zahra ta kafe akan basu bukatar komai dole suka hakura,,
A gajiye suka shigo gidan nasu Aisha suka zube kan gado daga amso dinki suke Wanda anko ne sukayi ita da aminiyar tata wato Aisha tunda bikin babu wani shiri basuyi anko ba na mutanen,,
Bangaren su Mama ma hidima aketayi duk abunda ya kamata anyi kudin gaisuwa dana sadaki da dan abunda baban yake da shi aka hada akayi mata saitin kujeru royal masu kyau sosai labulayya da carpets da freezer harda kayan kallo kuma baba na Lagos yace a bar masa duk shi zai yi komai yayi San barka dai dai karfinsu na talaka ,kayan kitchen nema sai a hankali basu ma daga hankalinsu ba don babu halin yin kaya irin Wanda zai dace da gidan daza'a kaita,,
Abunda yan uwa suka hada sai a siyi abunda ya sawwaka,,A ranar akayi aikin cincin dasu diblan alkaki da nakiya na gara gidan nasu yafara cika da yanuwa dukda di wasu ba kwana sukeyi ba,,
Da yammar ranar su Husna tareda yanbiyu da yayanta Yusuf suka iso,,
Kusan cika unguwar suka so yi da ihun murna ganin juna inda babu arziki Mama ta korasu gidansu Aisha dayake Mama ta sanar da hajiya su Aishan akan zasuyi zaman biki anan,,
Sunsha matukar mamaki da jin prince Amjad din zata aura don koda wasa Anty bata fada musu ba tambayoyi haka sukayita jera mata akan yadda akayi hakan ta kasance,,
Yayinda ita kuwa sai dai tayi murmushi tace ikon Allah ne kawai,,Kusan kwana sukayi suna hira babu bacci dayake Aisha tana da saurin sabo,,
Washe gari saura kwana. Biyu biki wurin gyaran kai suka nufa aka wanke mata shi da wani irin ruwan turare akayi scimin dinshi na kusan awa daya Wanda duk cikin hadin inna mariyan ne sanan aka busar mata da shi babu yadda basuyi ba akan tabar gashin ta yadda ya yi tamkar na larabawa saboda tsananin baki da sheki gashi har gadon bayanta,,
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi