🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
9⃣➕🔟
Kusan a tare suka fito dukkansu sanye cikin kananun kaya Wanda sai karamin gyale data dora aknta ba tareda ta rufa ba Wanda kusan gwara babu dashi da kansa ya ja motar suka fita a gida sai dai suka biya babban shopping malls yayiwa su Ammy siyayya kafin suka wuce masaukinsu ,,
Kokarin sakin fuskar tayi don bata son bacin ransa yadda ya tsare ta da idanu yana kallon duk wani motsi nata Afnan ce ta rugo da gudu da bude kofar don tasan bro dinntane,,
Aikuwa da sauri ta fada cikinshi tana cike da farin ciki tana fadin welcome bro jaid,peck yayi mata a gefen kumatun ta fuskarsa dauke da murmushi,,
Janye jikinta tayi tana soma Jan hannun sa zuwa cikin gidan jin yaki motsawa yasanta juyowa tana kallonsa yadda ya bata rai yana kafeta da idanu ya sanyata kwabe fuska tana fadin sorry bro hannu Nasreen ta kama tana kokarin kakalo murmushi tace sannu Nasreen,,Sai da ta yatsina fuskar kafin ta gyada kai tana cin magani,,
Shi kansa yaji zafin abunda Nasreen din tayi balle Afnan dake kiran kiris aikuwa uwar hararar ta zuba mata Bayan ta kwafi idanunsa ta ja shi da sauri zuwa ciki tana kwala kiran Ammyn,,Kwafa Nasreen tayi tana tana danne fushin ta a ranta tana fadin zakiga ne da sannu wallahi,Bayan su tabi zuwa cikin parlon dayake hotel ne babba na masu kumbar susa sosai inkana ciki bazaka taba cewa ba gidanka kake ba babban plat ne sosai Wanda yasha kayan more rayuwa na jin dadi da kwanciyar hankali,,
Zama Nasreen tayi a daya daga cikin manyan lumtsattsun kujerun dake parlon ta dauki daya daga cikin jaridun dake kan center table din parlon ta soma karantawa,,
Minti kadan suka fito dukkansu Ammyn sanye da hijab jikinta suka zauna suma bisa kujerun ,sannu Ammy kuna lafiya Nasreen din ta fada fuskar ba yabo ba fallasa,,
Lafiya lau dear da fatan kuna lafiya ko,,
Jinjina kai tayi tana kawai kusan gaba daya hankalinta na kan jarida dake hannunta,,
Shiru sukayi dukkansu Afnan na kara zabga mata harara,,yayinda shi kuma ya danne bacin ransa ya soma tambayar Ammyn yaya daddy suna lafiya,,
Sai dare sukabar wurin su Ammyn yadda Nasreen ta matsa mai akan tafiyar badon yaso ba don jirgin sassafe zasubi zuwa Holland,,
Har suka isa baice mata kala ba itama bata damu dayace dinba don tasan abunda zai fada bazasu kwashe da dadi ba shiyasa Sam bata son yana kaita gidan nan har yanzu komai na hausawa Ammy takasa dainashi shiyasam tasu batazo dayaba musamman wannan fitsararriyar kanwar tasa Afnan,,
Duk yadda yaso nuna mata fushi nunawa tayi Sam bata gane abunda yakeyi ba tashiga kashe shi da salonta har ya bada kai bori ya hau,,
Toilet ya nufa Bayan komai ya lafa yana mamakin hali irin na Nasreen,,
Zata nuna mai tsananin so da kauna amma kuma dukkan yan uwansa da wadanda yake Hulda dasu bata son suna rabarta balle ita ta rabesu wannan otace kawai babban matsalar Nasreen din lumshe idanun sa yayi a hankali tamkar maijin zafi a idanun ya shiga tunanin yadda suka hadu,,
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi