🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
*🤸🏻♂🤸🏻♂🤸🏻♂💃🏻💃🏻💃🏻Barkanmu sisters da dawowa,ina yiwa daukancin musulmai baki daya murnar barka da sallah,Allah ya maimaita mana💃🏻💃🏻*
3⃣5⃣➕3⃣6⃣
Manyan tsadaddun motaci ne daga gidan ammyn suka debesu zuwa gida,,
bangaren Ammyn aka sauki baki harda Zahra a wani bangaren dake gefe daga parlon kasa,,kofa ce daga gefe inka bude dan karamin parlone dauke da kaya sai dakuna biyu da bayi a kowanne daki tamkar dakin baki haka yake,,
chan cikin kuryar dakin aka kai Zahra datake lullube aka zaunar da ita bakin gado kuka takeyi sosai Wanda ta rasa dalilin yin hakan tunda hancin motarsu ta kutsa gate din gidan kuka mai karfi ya kwace mata,,
Masu tarbar amarya yan uwan ammyn da daddyn suka shigo suna lallashinta tareda bata baki akan hakane dama kowacce ya taji lokacin rabuwa da iyayen ta,,
Nan da nan aka shikasu da kayan abinci dana sha da kayan ciyeye iri iri kafin suka fita don su barsu ,iyayen zahran ma kowa sallah ya mike yayi ita kuwa tana rike jikin Aisha suna matsar kwallar sai ajiyar zuciya take saukewa akai akai,,
Sai da sukayita lallashi kafin ta iya mikewa ta nufi toilet tayo alwarla lokacin da ta fito kowacce na cin abinci hijab ta dauka ta tada sallah,,tana idarwa ta haye gadon daga gefe ta kwanta ,babu yadda basuyi ba amma taki cin komai koda ruwa ne saima rufe fuskarta datayi da hijab din jikinta,,
Zuciyarta chunkushe take dawani irin dunkule a kirjinta gaba daya tsoro da tausayi hade da tunanin inda zata dosa a gaba ya mamaye zucoyar ta da kwalkwalwar ta sai yanzu zuciyar ta ke tunashe ta da anya batayi ganganci ba kuwa da kawo kanta zaman aure ga inda batasan matsayin taba balle darajar taba,,
Ajiyar zuciya ta sauke a boye don tuni da wani sashe na zuciyarta dayayi mata akan dubbin irin so da kaunar datake yiwa Amjad dinta murmushi ta saki a hankali tana tuno ranar dayazo gurin ta kafin biki babu komai zan yi hakuri koda kuwa kallon sa nakeyi a kullum ya ishi zuciya ta samun nutsuwa da kwanciyar hankali,,
Sallamar ammyn ce ta dawo da hankalinta ga dakin sake dukunkunewa tayi tanajin tsananin kunya da nauyin ammyn koda ta rufe fuskarta tana iya hango tsantsar kamannin su da Amjad din,,
Sake gaidasu Ammyn tayi tareda tambayar babu wata matsala suka amsa da aa babu komai suka dora da yi musu godiya tareda adduoe,,
Ina yarta wa take dafatan taci abincin ko Ammyn tayi tamabayr tana Karasawa kusa da Zahra,,
Hajiya kaka ce tace inafa ta Sanya koda ruwa a cikin ta tana aikin kuka,
Waro idanu ammyn tayi tana fadin aa ba zai yuwuba maza a tasheta zama da yunwa babu dadi bari inje a hado mata tea yanzun nan tana gama fadar haka ta mike tayi kitchen da kanta ta hado ta dora a tray ta kawo da kanta ta ajiye a kan bed side,,Tashi maza yata ki shanye shi yanzu nan ai kinzama yar gida kuma don haka baa zama da,,
Dole babu yadda ta iya ta mike daka kwanciyar datake tadan yaye rufe fuskar datayi kadan ta amshi mug din da Ammyn ta miko mata ta soma a hankali ,,yawwa yata ko kefe Ammyn ta fada tana mikewa sallama tayi musu tana kara jaddada don Allah ta shanye tea din,,
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi