.🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*
Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*بسم الله الرحمن الرحيم
9⃣1⃣➕9⃣2⃣
Ya kamata ki tashi haka pretty ina buƙatar yin wanka,banyi sallah ba valle cin abinci please tashi haka ki taimaka min,
Jujjuya kai ta soma yi tana faɗain ohhh my god baby daga dawowa baka ganin halin dana ke ciki,mai kake so inyi maka ɗaukar ka zanyi komai na wannan ciki danake fama,meye amfanin wheel chair ɗin tsaki tayi da ƙarfi ta juya chan ƙarshen gadon ta sake lullubewa don bacci takeji sosai ga kasala datake damunta,
Tunda ta fara maganar bakinsa ke buɗe yana binta da kallon cike da mamaki ranshi a bace, taya take nufin zai iya yima kanshi ayyuka daya sabayi,yau kawai yanemi taimakon ta ta ƙasa yimashi a haka zata iya cigaba da rayuwa dashi,saurin kauda zancen yayi yana tausar zuciyar shi da koƙarin yimata uzuri tunda tana ɗauke da cikin shi,zai bata lokaci yasan prwtty ɗinshi bata iya fushi ko kyaleshi cikin damuwa,juyar da keken yayi ya nufi toilet yayo wanka da alwarla a zaune akan keken ya fito ya nufi drower ya ɗauko jallabiya ya sanya ya koma inda yakeyin sallah yayi sallolin shi harsa azahar dabai samu damar yiba,saanan ya buɗe ƙofa ya fita daga ɗakin,dai dai kan mataƙalar step yatsaida keken yana kallon steps ɗin tabbas indai ba kashe kanshi zai ƙarasa yiba babu yadda zai iya sauke kanshi ƙasa yaci abinci,Zahra ce kawai ta faɗo mashi arai take ya lumshe idanu yana jin kewar ta tabbas da tana kusa dashi babu abunda zai nema ya rasa,
"Ya jikin " ya tsinkayi sanyayyar muryar Zahra cikin kunnenshi da sauri ya ware idanun shi akanta sanye take da babban hijab har ƙasa hannunta riƙe da ɗan matsaikacin tray wanda bisa ga dukkkanin alamu abinci ne,
Yanayin yadda yake binta da kallo ya sanyata yin ƙasa da kai murya na rawa ta soma faɗin "ga abincin kayi hakuri na ɗauka kaci tun ɗazu"Juya keken yayi baya batareda yace mata komai ba don haka sai kawai tabi bayanshi har cikin parlon ta ajiye mashi abinci kan table ɗin dake kusa dashi ta juya ta fice zuciyar ta na bugawa so take ta tambayeshi in yana buƙatar wani abu amma ta kasa saboda yadda ya tamke fuska,
Shi kuwa amjad haushin aje mashi abincin ne datayi batareda ta bashi a baki ba shiyasanya shi haɗe fuska wanda ya rasa mai yasa yaji zuciyar shi tayi zafi da hakan,ya jima zaune yana tunanin ta kafin ya buɗe abincin ya soma zuciyar shi tunkushe sam saiyaji tamkar ba abincin ta yakeci ba vacin yunwar dayake ji tabbas da zai bar mata annan ne domin tagane laifinta,,Ita kuwa Zahra direct kitchen ta nufa ta soma kokarin ɗaura girkin dare tana tunanin irin zaman dazasuyi bata son cika chusa kanta a inda batada wata daraja musamman yadda tafi kowa sanin halin rashin mutinci irin na Nasreen amma batajin zuciyar ta zata daure barin shi shiƙadai yana buƙatar taimako da kwanciyar hankali tareda adduoe wanda tasan bazai taɓa samun hakan daga Nasreen ba wanna hakkin tane wannan aikin tane ya zamar mata dole tayi fito na fito ko kwana ne ya raba masu,zata jure duk wani irin wulaƙanci daga Amjad ɗin da Nasreen har ya gane manufarta akan haka,,
Tana gama ɗora abincin ta fita waje chan wurin masu aikin da sauri ɗan bayaro ya taso gareta yana duƙawa cikin girmamawa ya gaida ta,amsa wa tayi sannan tace "don Allah number su ammyn zaka sake gwada min ko zata shiga har yanzu bai samu ya siya wata wayar ba tun faruwar abunnan"
da sauri ya ciro wayar yana faɗin gashi hajiya konemesu ai dama komai sai a hankali,ya juya ya koma channinda suke zaune,jiyawa tayi ta koma chan baƙin ƙofar parlon tana adduar Allah ya sanya a same su,kira kusan sau goma tana gwadawa amma yaƙi shiga sam doke ta maida mashi duk ranta babu ɗaɗi sai yanzu takejin haushin manta number su a gida,komawa kitchen tayi tana saƙa dole zata san yadda zatayi ta nemesu,
YOU ARE READING
ZAN RAYU DA KAI
RomanceLabari akan tsantsar soyayya ga Wanda baisan tanayi ba saima niyyar mummuna daya kudira akan ta ,amma hakuri da ladabi hade da karfin soyayya datake masa tun tana karama ya juyar da akalar kudiransa mummuna zuwa ga na alkhairi