page 96

1.6K 87 20
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com


loadιng...........✍🏻


🌐 *ZÃN RAYU DA KAI*

Story_*oum zahra*
*Written$edit__pheeymarrh*
*MRS NOOUR*
Pheeymarrh@gmail.com
Wattpad me *@pheeymarrh*

بسم الله الرحمن الرحيم

9⃣6⃣

Gaba ɗayansu suka fashe da kuka da ƙarfi Afnan ba kiran sunanta tana riƙe da hannunta ,Ammyn kuwa sallati kawai takeyi irama cikin kukan yayinda Amjad duk ya gigice yana riƙe da ita yana girgizata saiya kalleta ya rungumeta a girjin shi yana kiran sunanta da ƙarfi yana sambatu iri iri,
Shi kanshi daddyn daya shigo yaga parlon duk a hargitse ga jini duk jikinta hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba ƙarasawa yayi yana faɗin "maza muje asibiti before its too late"
"daddyn bata numfashi fa ya kashe ta wallahi ta mutu Zah..."
Wani irin mugun naushi ya kaiwa bakin Afnan daya sanyata ƙasa cigaba da maganar ta,

Kallon ta yakeyi cikin fita hayyaci yana sauke numfashi da ƙarfi wanda dukkanin su suna ita jiyowa idanun sgi sun ƙaɗa sunyi jajur yake faɗin" dont ƙarki sake faɗin haka i will kill you first zahra bazata taba mutuwa ba,bazata mutuba i knew that nasan bazata taɓa varin amjad ɗinta cikin gagarin rayu..."

"Son!!!daddyn ya daka mashi tsawa yana matsowa kusa dashi,control your self mana lets hurry mukai ta asibiti" ya faɗa yana riƙo Afnan tsaye wacce ke dafe da hancinta dake zubar jini tana kuka matsananci

a zabure ya miƙe da ita ya fice da gudu suna biye dashi sum cikin gudun suka shiga motar wanda ɗanbayero tuni yayo revearse ɗinta baya amjad ya kwantar da ita Ammyn tayi saurin faɗawa motar tum kafin ya rufe ƙofar,tana shiga ya datso ƙofar da ƙarfi ba tare da ya lura da ammyn ba zagayawa yayi ya biɗe mazaunin driver yana kokarin fuzgo ɗan bayero waje da sauri ya fito jikin shi na rawa don ya tsorota da yanayin amjad ɗin dayake shirin yin driving wanda kallo ɗaya zakayi mashi ka tabbatar da bashi cikin hayyacin shi,

ganin haka ya sanya daddyn zagayawa ya buɗe gefen driver ya zauna,Afnan ma tasamu ta buɗe baya gefe ta shige tun kafin ta rufe murfin motar ya fige ta da itakacin ƙarfin sa Allah ya sanya maigadi ya buɗe gate da tabbas saiyayi ciki da gate ɗin ya rushe katangar,
gudu yakeyi cikin ƙarshe speed tamkar motar zata tashi sama amma duk da haka gani yakeyi baya gudu,su kansu su ammyn gani sukeyi baya gudun duk hankalinsu tashe yake daddyn ne kawai yaketa adduar saukar su lafiya ba tare da ya iya yiwa Amjad ɗin magana ba don yasan bazai saurare shiba,

Ihuu Afnan ta sanya cikin ɗaga muryar daya sanya shi take burki a firgice ba tareda ya duba a tsakiyar titi yake ba,Allah yasa babu wata mota dake kusa dasu,
"Jini! jini !! jini !!! Ammy"Afnan take faɗi tana nunawa Ammyn yadda jini ya gangaro har zuwa jikin Afnan ɗin wacce ke zaune kusa da ƙafafun Zahra,
a gigice ya fito domin vaƙaramin tsorata yayi da jinin ba balle murfin motar yayi yayo watsi da Afnan waje ya kinkimo zahra yana kuka sosai dube dube ya soma nan take idanun shi suka sauka kan wani ƙaramin maternity clinic ba tareda ya tsaya ƙarantawa ba ya nufi ƙofar asibitin da ita cikin gudu yan kiran sunanta da faɗin"please karki mutu ki barni Zahra ,bazan iya rayuwa babu keba,maiyasa kikayi min irin wannan sadaukarwa bayan ban chanchanci hakan daga gareki ba don Allah karki fanshi ranki a kaina ban chanchanta,van chanchanta ba"har nirse suka fito da gadon marasa lafiya aka ɗorata bai daina sambatun ba yana riƙe da hannun har zuwa emergency,da sauri nurses suka riƙeshi aka turo ƙofar aka rufe,zubewa yayi wurin yana kuka sosai tamkar ƙaramin yaro saida daddyn ya ƙaraso ya kamashi ya miƙe tsayi ya rungume shi jikin shi yana bubbuga bayanshi cikin lallashi har ya daina kukan ya fara sauke ajiyar zuciya,zaunar dashi yayi kan kujera yana lallashin shi tareda ƙarfafashi akan zata tashi addua itace ya kamata yanayi ba kuka ba,

ZAN RAYU DA KAIWhere stories live. Discover now